A ranar Laraba ne aka caka wa Mounir Nasraoui wuƙa, wanda shi ne mahaifin matashin ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal.
Lamarin ya faru ne a wani filin fakin da ke unguwar Rocafonda ta arewacin birnin Barcelona na ƙasar Sifaniya, inda aka caka masa wuƙa a ƙirjinsa. A unguwar ta Rocafonda Lamine Yamal ya girma.
A yammacin Laraban ne aka garzaya da mahaifin ɗan wasan asibiti. Nasraoui yana da shekaru 32 a duniya, kuma yana sanye da rigar da ke ɗauke da sunan ɗan nasa, a lokacin da lamarin ya faru.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9.10 na dare a wani filin fakin, sannan 'yan sanda sun sanar da kama mutum uku 'yan awanni bayan nan, da ƙarfe 11 na dare, kuma suna ci gaba da bincike kan harin.
Rahotanni sun ce shugaban Barcelona, Joan Laporta yana cikin waɗanda suka je duba mahaifin na Yamal a asibiti.