Amsoshin da Frank Lampard ya bayar kan komawa horar da  Chelsea

Amsoshin da Frank Lampard ya bayar kan komawa horar da  Chelsea

Lampard zai rike ragamar kungiyar ne a matsayin riko, har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Frank Lampard ya ce  Chelsea tana da dadadden tarihin cin nasara / Hoto Getty

Tsohon dan wasa kuma tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, wato Frank Lampard ya sake karbar ragamar horar da kungiyar da ke birnin Landan.

Dawowarsa zuwa Chelsea ta biyo bayan sallamar tsohon manajanta Graham Potter ranar Lahadi da ta gabata, bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Aston Villa ranar Asabar.

Yayin gabatar da shi a matsayin sabon manaja a ranar Alhamis, Frank Lampard ya yi wata tattaunawa da manema labarai, wadda aka wallafa kai-tsaye a shafin Twitter na kungiyar @ChelseaFC.

An tambayi Lampard, “Ko ka taba tunanin da ma za ka dawo bakin aiki a matsayin manajan Chelsea?”

Lampard ya amsa da cewa, “Ni mutum ne mai cike da kwarin gwiwa. Kuma Chelsea kungiya ce da muke da wata alaka ta musamman.”

A karo na farko na zamansa manaja a Chelsea, Lampard ya kwashe tsawon shekaru biyu, daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Lampard dai wani tsohon gwarzon dan wasan Chelsea ne, wanda ya taka wa kungiyar leda tsawon shekaru 13.

Ko da aka tambayi Lampard ko ya yi saurin amsa tayin dawowa Chelsea ne don ya “karasa ladansa”, sai kocin mai shekar 44 a duniya ya ce, “A yanzu muna wani sabon babi ne. Idan ka ce na zo “karasa ladana”, tamkar kana so na yi kurari ne irin na ‘jaruman fim din Hollywood”.

Chelsea dai ta yi ta sha sauya manajoji a ‘yan shekarun nan. Shi ma tsohon manajan kungiyar da ya sauka a makon daya wuce, Graham Potter, watanni bakwai kacal ya rike ragamar kungiyar, wadda a yanzu take mataki na 11 a teburin Firimiya.

Kocin da ya rike kungiyar bayan tafiyar Lampard a 2021 shi ne Thomas Tuchel, wanda ya ciyo wa kungiyar kofin Zakarun Turai a shekarar ta 2021.

Duk da nasarar da Tuchel ya kawo wa Chelsea, zamansa bai yi karko ba, inda aka sallame shi a watan Satumban 2022, bayan rike ragamar kulob din daga Janairun 2021.

Lampard ya rufe tattaunawarsa da ‘yan jarida da cewa “Gaskiyar lamari shi ne muna bukatar mu ci wasanninmu kafin mu samu damarmaki. Amma sanin kowa ne Chelsea tana da dadadden tarihin cin nasara.”

Yanzu dai aiki ya rage wa mai shiga rijiya, saboda za a tsumayi ganin wane sauyi Frank Lampard zai kawo wa kungiyar Chelsea don ganin ko zai kawo wa kungiyar tagomashin da za ta iya buga wasan Zakarun Turai a kakar wasa ta gaba.

TRT Afrika