Manchester City ta shirya tsaf don lashe Kofin Zakarun Turai na bana, sakamakon irin nasarar da kulob din ya samu a gasar zuwa yanzu da yake matakin kusa da na karshe.
A zangon fako na wasansu na karshe da Bayern, sun zura musu kwallaye har uku, dadilin da ya sa ake ganin wasan yau ba zai kai City dare ba, duk da dai a gidan Bayern za a buga, wato a Allianz Arena.
Ga wasu dalilan da bisa dukkan alamu za su taimaka wa City su cimma burin cin kofin da ba su taba dagawa ba a tarihinsu.
Aljanin dan wasa Haaland
Hazikin dan wasan Manchester City Erling Haaland yana da nasibi a duka gasannin da yaka bugawa kulob dinsa. Kowane kulob da zai tunkari City yana shakkar Haaland.
A wassanni biyu na karshe da ya buga a Gasar Zakarun Turai, dan wasan wanda dan asalin kasar Norway ne, ya ci kwallaye har guda shida shi kadai.
A wasansu da RB Leipzig, saura kiris ya ci kwallaye shida ko bakwai ba don Guardiola ya cire shi ana minti 30 kafin gama wasan.
Sannan ya yi kokari a wasansu da Bayern, duk da dai kwallo daya kacal, ya ci sai kuma tallafin da ya bayar ga Bernardo Silva wajen cin kwallo ta biyu a minti na 70.
Burin Guardiola na karshe
Baya ga yawan wasannin da kofunan da koc Pep Gurdiola ya ci a Manchester City, ya yi wani abu da ya bai wa masana kwallon kafa al’ajabi.
Baya ga yawan wasannin da kofunan da koci Pep Gurdiola ya ci a rayuwarsa ta horar da kungiyoyin kwallo, ya yi wani abu da ya bai wa masana kwallon kafa al’ajabi.
A lokaci guda Guardiola ya yi watsi da ‘yan wasansa na baya guda biyu, ana tsaka da kakar wasa. A hakan kuma ya yi rainon wasu ‘yan wasan kuma ba tare da matsala ba suka maye gurbin na da.
‘Yan wasan su ne Joao Cancelo da Kyle Walker. A cikin kakar wasa biyu na baya sun ya kasance daya daga cikin ‘yan wasa mafi tasiri a tsarin salon wasa na Guardiola.
Amma kwatsam sai kocin ya zabi ya sauya Cancelo ya duko dan tsakiyar baya, Nathan Ake, saboda kokarinsa na tsaron gida.
Yayin da Cancelo ya nuna rashin jin dadin barinsa, sai Guardiola ya tura shi aro zuwa Bayern Munich.
Haka shi ma Walker, Guardiola ya cire shi daga jerin ‘yan wasan baya a sabon salon tsara ‘yan wasansa, wanda ya kunshi mutum uku a baya, sai biyu masu tsaro daga tsakiya.
De Bruyne ya dawo fom
Dan wasa dan asalin Belgium, Kevin de Bruyne shi ne hazikin dan wasa tun zuwan Guardiola Manchester City. Haka kuma shi ne dan wasa mafi hazikanci ta kocin ya koyar tun bayan Lionel Messi.
A farkon watan nan, De Bruyne ya zamo dan wasan da ya fi kowa saurin taimaka a cin kwallaye 100, a tarihin gasar firimiya.
Sai dai hakan bai hana Guardiola sukar kokarinsa ba a wasu lokutan.
Sai dai kuma, masana kwallo suna gani wannan takun saka tsakanin koci da De Bruyne shi yake kara wa dan wasan kaimi, wajen himmatuwa don buga wasa mai kyau. A yanzu dai, dan wasan ya ci kwallaye 9, ya taimaka a cin guda 22.
Ala ayyi halin, masu sharhi suna ganin City dai za ta wuce zuwa zagaye na gaba, na dab da karshe a gasar ta Zakarun Turai, inda Real Madrid take jiransu a gwabza irin tataburzar da suka yi a kakar bara.