Daga Mazhun Idris
A tsakar ranar Asabar, Salmanu Sani Salihu dan shekara 14, yana zaune kan kafafuwansa a cikin shago, inda yake koyon sana'a. Cikin tsanaki, yana rike da zare kalar ruwan kasa, da 'yar allura, yana dinka zaren kan wani kyalle ruwan fauda.
Salmanu yana dinka kakkauran zaren kan shatifi zane da fensiri, a wuyan rigar da ba a kammala hade ta ba. Yana fitar da aikin riga mai kawanya da yawa, inda yake dora zaren yana harhadewa da juna.
A zaune daura da shi akwai yayansa, kuma mai koyar da shi dinkin hannu, masanin dinki Nuhu Sani Salihu, dan shekara 35. Nuhu shi ya mallaki shagon dinkin da ke tsakiyar sananninyar Kasuwar Zaria, da ke jihar Kadunan Nijeriya. Suna dinka tufafin Hausawa na gargajiya daban-daban.
“Saboda karshen mako ne, mun zo aiki tun da hantsi, kuma za mu tashi da karfi hudu na yamma,” in ji Salmanu, da yake hira da TRT Afrika, yayin da shi da sauran yara masu koyon aiki suka mayar da hankali kan zare da allurar da suke aiki da ita.
Hada koyon sana'a da makaranta
Salmanu ya fara koyon dinkin hannu tun shekara hudu da suka wuce. A yau, yana aiki ne tare da 'yan-uwansa biyu, Abdulkadir da Jabir, da kuma wasu yaran su biyu masu koyon dinki, Abdullahi da Abdulkarim.
Bayan daukar shekaru suna koyon dinkin hannu, yara suna girma su zama kwararru masu dinkin tufafi.
Kamar sauran yara a arewacin Nijeriya, Salmanu yana hada koyon sana'a da zuwa makarantar boko, wata dabi'a da take rage hadarin rashin samun aikin-yi bayan kammala karatu.
Salmanu yana karatu a makarantar Barewa College, sananniyar makarantar sakandare da aka kafa a 1921, wadda daga nan ne Firaiministan Nijeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, da wasu shugabannin Nijeriya na baya suka yi karatu.
Salmanu ya fara kwarewa a koyon dinkin hannu - inda yakan iya aiki shi kadai, wanda ke ba shi damar samun kudi. Sauran abokansa masu koyon aiki su ma sukan samu kudi idan sun yi aiki.
“Ina jin dadin koyon aiki nan, kuma da kudin da nake samu kullum idan an tashi aiki, ina biyan wani bangare na kudin makaranta, har nakan taimaka wa gidanmu,” in ji Abdullahi Isyaku, wani mai koyon dinkin hannu da ya zanta da TRT Afrika.
Abdullahi ya nuna kayan da yake sanye da su, sannan ya kara da cewa, “Ni na sayi kayan nan na jikina, kuma ni na dinka aikin rigar da kaina.”
A ranakun makaranta, lokacin da aka tashi daga makaranta wajen karfe 1 na rana, yaran sukan nufi gida su ci abincin rana, sannan su taho shagon koyon dinki, inda za su yi aiki har zuwa karfe 4 na yamma, lokacin da za su tafi makarantar Islamiyyar yamma.
“Babana ne ya kawo ni nan na koyi aikin dinkin hannu, maimakon gararamba a gari,” a cewar Abdullahi.
Al'ummar Hausa sun gaji wannan sana'ar tsawon shekaru dubu. Mafi fice a kaftani dinkin hannu ita ce babbar-riga, wadda ta ke da farin jini a Yammaci da Tsakiyar Afirka.
A al'adar Hausa, an fi ganin tufafi masu dinkin hannu a jikin maza, duk da akwai wasu nau'in tufafin mata da ke wa dinkin hannu. Kamar sauran sana'ar dinki, an yi gadon sana'ar ne tun kaka da kakanni.
A 'yan shekarun nan, dinkin surfani da ake yi da inji ya shigo, kuma ya karbe wani bangaren kasuwar dinkin hannu. Wasu madinka suna amfani da injin, mai kwamfuta da ke zayyana zane salo-salo. Amma duk da haka, tufafi masu dinkin hannu suna da farin jini gun mutane a al'umma, har da masu sarauta da 'yan siyasa.
Ana sayar da tufafi masu dinkin hannu da dinkin surfani na inji a kasuwannin cikin gida, kuma ana fita da su kasashen waje, yawanci ga 'yan Afirka mazauna Turai da Asiya.
Kamar sauran harkokin kawa, masu dinkin hannu sukan samu ciniki sosai a lokutan bukukuwa masu maimaituwa, kamar bikin Sallar Idi na Musulmai, yayin da bukatar sanya sabbin tufafi ke karuwa.
Yara kamar Salmanu da Abdullahi, suna kallon koyon sana'ar da suke yi a zaman wata dabara da za ta taimaka musu nan-gaba, baya ga karatun boko da na addini.