Watakila lokaci ya yi da za a fara gyara da kwaskwarima ga dokar 2004 da ta haramta saka kowanne irin kaya a makarantu Hoto: Reuters

Ba wai gwamnatin Faransa kawai ba, har ma wani sashe na al'ummar Faransa, mafi yawa masu tsaurin ra'ayi, da ba sa son irin wannan tufafi da ke da "tsayi" ko "alamar Musulmi".

Lalacewar ta yi yawa. Wani mataimakin shugaban makaranta a Faransa ya taba fada wa taron malamai su 30 cewa "Zan fada muku wannan abaya ce ko riga ce doguwa kawai. Idan kuka ga mutum haka za ku gane Musulmi ne ko akasin haka."

An fi yin kalaman nuna kyama ga Musulunci ga dalibai bakaken-fata ko 'yan Arewacin Afirka da ake yi wa kallon Musulmai.

Su ne suke fuskantar wannan nuna wariya. Daliba farar-fata za ta iya saka doguwar riga ba tare da wata kyara ba, amma 'yar ajinsu baka ko wankan-tarwatsa za ta fuskanci suka idan ta yi hakan.

Gwamnatin Faransa tana daukar irin wadannan matakai ne saboda ta sani cewa tsangwamar Musulmai na tattare da riba a siyasance.

Shi ya sa a baya-bayan nan Ministan ilimi na Faransa Gabriel Attai ya sanar cewa za a haramta saka abaya a makarantun fadin kasar.

Duk wani tufafi da yake da kala kuma yake da tsayi ko yake wakiltar 'nuna kunya' to matsala ne a wajen gwamnatin Faransa, matukar dai matan da ake wa kallon Musulmai ne suka saka shi, ko da ba su saka hijabi ba.

A yayin da kungiyoyin Musulmai a Faransa ke ta nanata raba dogayen kaya ga Musulunci, suna bayyana cewa kayan sun fi kama da na al'ada maimakon addini, saboda sun samo asali ne daga Gabas ta Tsakiya.

Amma har yanzu ministan na amfani da kalmar abaya don halasta hanin da aka yi don cusguna wa Musulmai.

Wannan haramci zai bayar da dama a dinga takalar daliban da suka fito daga kasashen Larabawa, Turkiyya, Asiya da Afirka.

Duk wadannan matakai na raba kawuna na da madogarar shari'a.

A 2004, Faransa ta kirkiri dokar "Boye Addini da Bayyana Alamomin Addini a Makarantu", wadda ta haramta sanya kayan da ke wakiltar wani addini kamar su dan-kwali, hulunan Yahudawa da kuros na Kiristoci.

Gwamnatin Faransa ta bayyana hujjar daukar wannan mataki da cewa shi ne tushen dokokin rayuwa a Faransa na raba addini da kasa, habaka 'yancin tunani ga dukkan 'yan kasa, ba tare da la'akari da addininsu ba.

A yayin da Faransa ta dogara da 'yanci da daidaito don kare manufofinta, kasar ta juya tana kyamar marasa rinjaye da sunan aiki da wannan doka.

Hakan ya ci karo da dokokinta. Magana ce ta fassarar ma'ana: aikin kare wani kudiri ya rikide ya zama na zaluntar mutane, in ji wani ra'ayi.

Tushe daga tarihi

Kafa ra'ayin kyamar Musulmai a Faransa na koma wa ga zamanin mulkin-mallakar Turawan Faransa.

Misali, a 1935, a lokacin da runduna ta 5 ta Faransa ta kaddamar da yaki da jama'a a Aljeriya, wanda ya mayar da hankali kan matan Aljeriya, shirin wani bangare ne na dabara don mamaye jama'a tare da hana su bukatarsu ta samun 'yancin kai.

Gwamnatin mulkin mallaka ta Faransa ta kafa wata akida da ke nufar mata, wadda ta tanadi cewa "Idan muna son tunkarar al'ummar Aljeriya, yadda take da kokarin turjiya, to dole sai mun yaki matansu; dole mu je mu nemo su a inda suka buya a bayan mayafi, da gidajensu da mazajensu suka boye su."

Shekaru tamanin bayan haka, ana ci gaba da assasa wadannan akidu a kan Musulman Faransa a yau.

Kokarin gwamnatin Faransa na sanya dokoki kan tufafin addini, daga sanya hijabi a makarantu, nikabi da burkha, na nuni da tsantsar yunkurin sauya akidar Musulmai mata.

Duk da akwai yiwuwar samun karfafa gwiwa, hanyar da ake bi guda daya ce, ana kuma bayyana damuwa game da amfani da salon dabarun mamaya na zamanin mulkin-mallaka.

Masaniyar zamantakewar dan adam Hanane Karimi ta bayyana wannan matsala a littafinta mai taken 'Are Muslim Women not Women?' (Shin matan Musulmi ba Mata ba ne?), inda ta bayyana yadda gwamnatin Faransa ke kallon mata Musulmai a matsayin wadanda ba a bukatar su, kuma suke bukatar a dinga ladabtar da su ko sauya musu addini.

Karimi ta rubuta cewa "idan suka turje, sai su zama masu hatsari ana kyamar su: daga sannan sai a fara kiran su da Musulmai makiya."

"Manufar ita ce a hana su sukuni da girmamawar da al'umma ke yi musu ta hanyar samar musu 'wayewa'. A zukatan masu janye musu hankali, sai an samar da dokoki da ka'idoji, kalamai da za su mayar da su matan da aka fitar musu da mutuntaka da matuta."

Lamarin da ya bayyana barazanar shugaban makaranta da ya ware mata saboda tufafinsu, wanda ake wa kallon ya yi girma kuma ba ya bayyana wane ne su 'siffar jikinsu', misali daya ne kawai na irin wannan danniya da kokarin juya mata Musulmai da ake yi a Faransa.

Siyasa

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Gerard Darmanin na shirin tsaya wa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Haka kuma, Ministan Ilimi na Faransa Gabriel Attai ya bayyana shi ma zai shiga takarar shugaban kasar. Dukkan suna daukar matakan da za su ja hankalin masu jefa kuri'a na kowanne bangare.

A zaben shekarar da ta gabata, Shugaba Emmanuel Macron ya kayar da 'yar takarar masu tsaurin ra'ayi Marine Le Pen da bambancin kaso 5 na kuri'un da aka jefa - inda za a ga a 2017 ya kayar da Le Pen da wajen kashi 30. An yi kamfe da kalaman nuna kyama ga Musulmai.

A yayin da ake cikin haka, rashin samun nutsuwa ta fuskar tsaro da ma rashin tabbas na damun al'ummar Musulmai.

Matakai kamar su haramta wa daliban Faransa Musulmai mata sanya tufafin da ya dace da addininsu na da mummunan tasiri.

Hakan ya bayyana karara a yayin da shugaban makaranta yake rutsa dalibai mata a makaranta, malamansu na jiran su a kofofin shiga makarantu don duba irin kayan da suka sanya sannan su tattauna ko za a bar su su shiga azuzuwa, idan har sun rage tsayin riguna ko zannuwansu.

Kamar yadda yake tattare da bakin mulkin 'yan mulkin-mallaka na Faransa wajen murkushe mutane kan wadanda suke mulka, cikin hanzari makarantun Faransa na zama wuraren bin diddigin halayen mutane inda babban abun da aka fi mayar da hankali shi ne a takura wa Musulmai dalibai.

Watakila lokaci ya yi da za a fara gyara da kwaskwarima ga dokar 2004 da ta haramta saka kowanne irin kaya a makarantu, kayan da ke iya bayyana wanne addini mutum ke bi. Dokar ta fi takura wa dalibai Musulmai, musamman ma mata.

TRT World