Daga Halima Umar Saleh
A shekarun baya-bayan nan, ga alama farin jinin fina-finai masu dogon zango na kasashen waje na karuwa a Nijeriya.
Ko da yake fina-finan Indiya da na Mexico da na Koriya ta Kudu na da farin jini a tsakanin 'yan Nijeriya, fina-finan Turkiyya sun kutso kasuwar tare da sace zukatan masu kallo.
Masu sharhi na ganin yanzu babu na biyun fina-finan Turkiyya wajen karbuwa musamman a arewacin Nijeriya.
Ta kai ga fina-finan na Turkiyya na gogayya matuka da fina-finan Kannywood da wasu fina-finan masu dogon zango wadanda ake yi a arewacin Nijeriya da harshen Hausa – kamar ’Kwana Casa’in’ da ’Dadin Kowa.’
Bayan bacewar kaset na bidiyo da kuma raguwar tagomashin faifan CD da DVD, sai fina-finai masu dogon zango suka farfado a nahiyar Afirka, musamman ma da taimakon gidajen talabijin na tauraron dan adam masu gabatar da shirye-shiryen nishadantarwa da kuma manhajojin kallo na intanet kamar Netflix da Youtube.
A tashoshin talabijin na tauraron dan adam a Nijeriya dai an fi nuna fina-finan Turkiyya irin su 'Adını Sen Koy' wanda aka ba shi suna 'Tarkon Kauna' da Hausa, da 'Elimi Bırakma' da ake kira 'Rayuwata' da kuma ‘Kyautata Rayuwa’ wato ‘Böyle Bitmesin.’
Yayin da a Youtube da Netflix kuma aka fi kallon irin su Dirilis Etrugul da The Magnificent Century.
Kusan duk gidan da ka shiga musamman a jihohin arewacin kasar kamar Kano da Bauchi da Katsina da Kaduna da Jigawa da sauransu, za ka tarar da masu son kallon wadannan fina-finai na Tukiyya - babba da yaro, mata da maza.
Mene ne ya sa fina-finan Tukiyya ke da farin jini wajen 'yan Nijeriya?
Wata rana da yammacin Asabar na kai ziyara wani gida a birnin Kano, inda na tarar da ilahirin iyalin gidan sun taru a babban falo sun yi wa talabijin kuru suna kallon fim din Etrugul cikin harshen Turkiyya.
Wani jigo a cikin iyalin da ake kira Baba Abdullahi ne mai fassara wa sauran abin da ake fada a cikin fim din, kasancewar yau da gobe ya fahimci harshen Turkiyya.
Ga alama dai hankalinsu duk ya karkata a kan fim din, wanda suka sauke shi takanas daga Youtube.
A zaman 'yan mintinan da na yi, sai da Baba Abdullahi ya yi min takaitaccen bayani a kan fim din da suke kallo da yadda suke jin dadinsa sosai.
Ya ce mani "ki yi hakuri baiwar Allah, kin same mu duk hankalinmu a kan fim din nan. Yana da kyau da ma'ana ne.’’
Ya kara da cewa "Fim din na Turkawa ne sannan yana magana ne a kan tarihin Daular Usmaniyya ta Musulunci a kasar, da irin karfin da ta yi a duniya.’’
Ya ma ba ni shawarar na nemi fim din na kalla, domin ta haka zan fi gane abin da ya ke nufi.
Na sha zuwa gidaje a garuruwa daban-daban a Nijeriya inda na ganewa idanuna yadda iyalai ke zakuwa wajen kallon fina-finan Tukiyya.
Da yawa sun bayyana mini cewa dabarar da gidajen talabijin ke yi ta fassara wadannan fina-finai zuwa harshen Hausa na daga cikin dalilan da suka sa mutane suke rububinsu.
Fatima, mai shekara 30, uwa ce mai 'ya'ya uku a birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.
Ta shaida mini cewa salon ‘yan Tukiyya na tsara fina-finan da tsaftace su ya sa ba ta jin nauyin kallo tare da 'ya'yanta.
"Kin ga dai muna ganin kyawawan al'adun Turkawa da yanayin zamantakewarsu da tarihinsu, wanda ke cike da ilimintarwa.
"Ba za ki ga wani abin assha da zai sa ka kasa kallo tare da yara ba," a cewarta.
Taurarin fina-finan Turkiyya masu farin jini wajen Hausawa
Wasu da suka samu labarin cewa zan tafi Turkiyya sun rika yi mani bayani na nuna kauna ga taurarin inda wasu suka ce “don Allah ki gaishe min da Malama Nisa idan kin isa Turkiyya.
“Ki yi hoto da ita ki turo mana,’’ wata ta ce mani, “ni kuma Zehra da Omer za ki gai da min,” in ji wani daban.
“Ina fatan wata rana na je Turkiyya don ganin su,” abin da yawancin mutane ke gaya min kenan.
Ba komai hakan ke nunawa ba illa tsananin soyayyar da suke yi wa fina Turkiyya.
Sunayen mutanen da ake ambata din ‘yan fim din Turkiyya ne da ke tashe, kuma masu farin jini.
Malama Nisa wato Nergis Öztürk ta fito ne a fim din Böyle Bitmesin da aka fassara zuwa Kyautata Rayuwa.
An nadi shirin ne a shekarar 2012 zuwa 2015.
Fim din yana nuni ne kan kyautata mu’amala ta zama da mutane inda Nisa ke yawan sasanta duk wata baraka da ta kunno kai tsakanin mutane musamman a zamantakewar aure ko aiki.
Wannan ya sa take da farin jini a wajen masu kallo da dama, saboda yadda matsalolin ma’aurata na daga cikin wadanda ke damun mutane a Nijeriya.
Kazalika idan ana maganar taurarin fina-finan Turkiyya masu farin jini a wajen ƴan Nijeriya dole a ambaci Zeyra da Umeyr da suke taka rawa a fim din da aka fassara zuwa “Tarkon Kauna”.
A ciki dai Umeyr wato Erkan Meriç, ya fito ne a dan kasuwa mai matukar arziki da ya yi auren kwangila na wata shida da wata karamar ma’aikaciya Zehra wato Hazal Subaşı, don ya faranta ran kanwarsa mai fama da wata rashin lafiya.
Sai dai auren kwangilar ya rikide zuwa soyayya ta ainihi da ke zuwa da matsaloli sosai.
An nadi shirin ne a shekarar 2016 har zuwa 2018.
Tasirin fina-finan Turkiyya a Nijeriya
Duk da dai babu wani adadi a kididdige da ke nuna yawan Turkawan da ke zaune a Nijeriya, amma a bayyane yake cewa akwai su da yawa wadanda ko dai harkokin kasuwanci ne ya kai su, ko kuma huldar diflomasiyya.
Sai dai yawan nasu bai yi tasirin da zai sa 'yan Nijeriya, wadanda yawan su ya kai mutum miliyan 200, su koyi wani abu na al'adu ko zamantakewa ko harshensu ba.
Amma sai ga shi lokaci guda ta hanyar fina-finai, 'yan Nijeriya da dama sun fara koyon Turkanci suna zaune cikin gidajensu.
Lokacin da na hadu da Muhammad, magidanci mai shekara 32, wanda ke mayatar kallon fim din The Magnificent Century da ake yi da harshen Turkiyya, na yi mamaki da na ji har yana iya hada ‘yan jimloli da Turkanci.
“Ni da farko na fara kallon fina-finan da ake nuna wa a talabijin ɗin ne masu fassarar Hausa.
Amma daga baya sai na gano akwai wasu masu daɗin sosai da ake samu a Netflix ko Youtube’’ in ji Muhammad.
Ya kara da cewa “kawai sai na bazama can. A yanzu haka ina fahimtar me ake faɗa da Turkanci kuma na kan ɗan iya haɗa jimloli ƙanana.’’
Muhammad ya ce bai taba karanta tarihin Daular Usmaniyya ta Turkiyya wadda ta kasaita a duniya tsakanin karni na 14 da karni na 20 ba.
To amma a dalilin fina-finan, ya fahimci tarihin ya kuma zauna a kansa daram. Burinsa na gaba kamar yadda ya ce, shi ne ya samu zuwa Turkiyya don ganin yadda ƙasar take da kuma ganin tarurarin fina-finan.
Kafin yaduwar fina-finan Turkiyyaa baya-bayan nan, da yawa cikin al’ummar Hausawa na wannan zamanin a Nijeriya ba su san abubuwa sosai ba kan Turkiyya idan ka ɗauke wata fitacciyar magana da ake yi don siffanta mace mai son mulki da isa.
Wato a duk lokacin da wata ta yi wani abu na nuna isa sai manya su ce “sannu ‘yar Sarkin Santanbul.”
Amma a yanzu mutane irin su Hafsah Ringim, wata mai matukar kallon fina-finan Turkiyya a Kano, ta ce a dalilin kallon ta san wasu abubuwa na tarihin ƙasar sannan ta lura da yadda suke da salon mu’amala mai kyau.
Hafsah ta ce ta koyi dabi’ar yin sulhu a wajen Malama Nisa ta fim din ‘’Kyautata Rayuwa’’ domin ‘’gaskiya na kara gane sulhu alheri ne daga irin salonta.”
Ba mu’amala kawai fina-finan Turkiyya suka koya wa Yaya Hafsah ba, domin a cewarta “na lura da yadda suke girmama shan shayi ko gahawa a cikin yini zur, musamman idan suna cikin damuwa ko wani lamari ya sha musu kai.
“Sai na lura idan suka sha gahawa kamar hankalinsu na kwanciya, su samu natsuwa da kuzari.’’
Hafsah ta kara da cewa sanadiyar haka ita ma ta fara wannan dabi’a ta shan gahawa domin samun natsuwa kuma cikin ikon Allah sai na fara ‘’jin irin yanayin natsuwar da nake gani suna samu.’’
Malama Hafsa ta ce tana fatan wata rana ta ziyarci kasar Turkiyya domin gani da idonta.
Fina-finan Tukiyya sun kere na Indiya
Maimuna S Beli, marubuciyar litattafan Hausa ce, mai sharhi ce kuma marubuciyar fina-finai masu dogon zango na Hausa da ake yi a Nijeriya.
Tana cikin marubutan fitattun fina-finai masu dogon zango na Hausa wato Kwana Casa’in da kuma Dadin Kowa.
Ta ce duk irin tsananin son da Hausawa ke yi wa fina-finan Indiya, a yanzu kam wannan yayin ya wuce don kuwa hankula duk sun karkata kan na Tukiyya.
Ta ce: “Fina-finan Turkiyya dai kan fi mayar da hankali ga batutuwan soyayya irin wacce Bahaushe ke son samu.
“Kazalika suna nuni kan zamantakewar iyali da batun addini da na tarihi. Irin wadannan batutuwa kuma na da matukar karbuwa a wajen Hausawa masu kallon fina-finai.
“Sannan suna koya wa mutum juriya da jajircewa da hakuri da yakana, wadanda duk halaye ne masu kyau wadanda ni kaina na koyi abubuwa masu yawa,” in ji ta.
A hasashen Maimuna a matsayinta na mai sharhi, ta ce “a yanzu ba da fina-finan Indiya suke gogayya ba, da namu na gida masu dogon zango da ake yi fina-finan Turkiyya ke gogayya.”
Kamar Hafsah, yanzu ‘yan Nijeriya da dama na yawan neman bayanai a kan Turkiyya, galibi kuma saboda tasirin da wadannan fina-finai suke yi a zukatansu.
Wannan kuma na taimaka wa wajen bunkasa harkokin kasuwanci da neman ilimi tsakanin kasashen biyu, musamman ‘yadda ‘yan Nijeriya ke zuwa kasar ta Turkiyya.