Mabiya ɗarikar Orthodox na ƙasar Habasha a ranar Laraba sun gudanar da bikin Meskel, daya daga cikin bukukuwa mafiya tsarki a al'adun Kiristoci a wannan kasa.
Daga cikin mabiya darikar Orthodox a Habasha da makociyarta Eritiriya, sun gudanar da bikin Meskel na tuna wa da ranar da Waliyya Helena ta gano asalin kuros din da aka gicciye Annabi Isa da shi.
A almarar da ake bayar da labarinta, Helena, mahaifiyar Sarkin Rum Constantine na I, ta je wajen da kuros din, abun da aka yi imanin an dawo da shi Habasha - a cikin hayaƙi bayan wani wasan wuta da aka yi.
A jajiberen Meskel, masu ibada na gina manyan tuddan wuta a kan tituna da kewayen majami'u don bikin da ake kira "demera" wanda ke bayar da sakon fara bikin.
Idan rana za ta fadi, bayan awanni da aka dauka ana rawa da waka, sai a ƙona wadannan tuddai da aka cika kansu da fure da kuros. Ana yin haka a dukkan fadin kasar.
Tudun wuta mafi tsayi na nan a Dandalin Meskel, wani babban waje ne da ke tsakiyar birnin Addis Ababa. Dubban mahalarta da suka hada da shugabannin coci da mabiyan darikar Orthodox ne ke halartar wajen sanye da tufafi mai kayatarwa.
"Karfin Kiristanci na dawo da asalin hadin kan da muke da shi. Yana taimaka mana mu manta da bambance-bambancen da suka yi ta tagayyara mu tsawon shekaru, inda suke saka mu yaƙar juna da rikici da tsana da ... bala'o'i," in ji wani malamin ɗarikar Ortodox da bai bayyana sunansa ba yayin da ya halarci bikin.
Habasha da ke da ƙabilu daban-daban kusan 80, na daya daga cikin kasashen Kiristanci mafiya dadewa a duniya.
Daular Aksumite, kakannin jama'ar Habasha na yau, sun mayar da Kiristanci addinin kasar daga karni na 4, lokaci guda da Daular Rumawa.
Ana hasashen kaso biyu cikin uku na jama'ar Habasha miliyan 120 Kirisitoci ne inda sauran kuma suka kasance Musulmai da maguzawa.
Mafi yawan Kiristocin mabiya darikar Orthodox ne, duk da cewa a baya-bayan nan akwai mabiya ɗariƙr Protestant.
A yankin Tigray, mahaifar masarautar Axumi, an fara bikin Meskel a cikin kwanciyar hankali tun 2020 a yayin da gwamnatin tarayya ta fara yaki da shugabannin 'yan tawaye a arewacin yankin.
A watan Nuwamban bara aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya bayan rikicin shekaru biyu.
"Ina yin bikin Meskel ta hanya mafi inganci fiye da shekarun baya. A kalla a yanzu ba ma jin ƙarar harbin bindiga, muna yin biki a cikin nutsuwa," in ji Kalayu Kiros daga Meleke, babban birnin Tigray.
Amma ya ce "akwai makircin afkuwar yaki da suke sanyawa ba zan iya wannan biki ba."
Meaza Teklemariam, shi ma daga Mekele ya ce bikin Meskel "bai zama kamar wanda ake yi kafin yaki ba" kuma tsadar rayuwa ya sanya da wahala a iya bikin.
Duk da kawo karshen yakin Tigray, rikici ya barke a wani yanki na Afirka da ke da jama'a da yawa, inda aka kacalcala jama'ar yankunan.
A Amhara, inda 'yan bindiga suka dinga arangama da sojojin Habasha tun watan Afrilu, an saka dokar ta baci a yankin inda aka yi zargin kashe mutane da kama su.
"Ta yaya za mu yi bikin Meskel yayin da dokar hana fita da tsoro sun sanya ka kana cikin gida? in ji wani mazaunin garin mai suna Debre Markos da ya nemi a boye sunansa.