Kiristocin Afirka ta Kudu sun yi tururuwa zuwa Majami’ar Saint Francis Anglican da ke gundumar Soweto a garin Johannesburg, inda suka yi tarukan tunawa da ranar komawar Yesu Almasihu zuwa sama.
Bikin Easter na bana ya fado ne ranar 10 ga watan Afrilu.
A abin da ke zama alamar goyon bayan juna tsakanin Kiristoci da Musulmai a Senagal; Musulman Senagal da Kiristocin na haduwa waje guda tare da shan alawar Ngalakh wadda ke bayyana irin hadin kai da goyon bayan da ke tsakaninsu.
A Senagal da kusan kashi daya bisa hudu na al'ummar kiristoci ne, suna hada kai da Musulmai yayin gudanar da bikin Ista.
Salomom André Mehoua yayin da yake gabatar da ibada a cocin Cathedral of Our Lady of Perpetual Help da ke Niamey, babbar birnin Nijar.
Masu ibada a cocin Redeemed Christian Church of God, da ke Jihar Rivers, reshe na daya a birnin Fatakwal.
AA