Daga Kudra Maliro
Mujallar Forbes ta ayyana Firaministar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, Judith Suminwa a matsayin macen da ta fi ƙarfi da tasiri a Afirka a shekarar 2024, a cikin jerin mata mafiya tasiri a duniya na shekara-shekara da take fitarwa.
Forbes ta ce an tantance jerin sunayen ne bisa la'akari da abubuwa hudu - da suka haɗa da kudi da kafofin watsa labarai da tasiri da kuma ƙarfin iko.
Suminwa, mai shekaru 57, Shugaba Felix Tshisekedi ne ya naɗa ta a watan Afrilun 2024 a matsayin mace ta farko da ta zama Firaminista a DRC bayan sake zabensa.
Ta kasance mace ta 77 a duniya a jerin da Mujallar Forbes ta fitar.
"Zama mace ta 77 mafi karfin iko a duniya ta Forbes ya fi gaban yarda da kai. Wannan alama ce ta kyakkyawan fata ga kowace yarinya da mace a DRC," in ji ta a wani saƙo da ta wallafa a dandalin X.
"Bari mu ci gaba da aiki don samun makoma inda kowace mace, a cikin DRC da kuma wajenta, za ta iya gane muhimmancinta da abin da za ta iya," in ji ta.
A baya Firaministan ta yi aiki da hukumar Majalisar Dinkin Duniya UNDP a matsayin mai kula da shirin zaman lafiya da ƙarfafa dimokruraɗiyya.
Ayyukanta sun maida hankali ne kan gabashin Kongo, yankin da ke fuskantar tashin hankali da rashin zaman lafiya.
Mpumi Madisa
'Yar kasuwa 'yar Afirka ta Kudu Mpumi Madisa, mai shekaru 45, ta kasance mace ta biyu mafi karfin iko a nahiyar kuma ta 87 a duniya.
Madisa ita ce ke jagorantar kamfanin Bidvest na Afirka ta Kudu wanda yake da ma'aikata kusan 130,000 da kuma kasuwar dalar Amurka biliyan 5.3.
Ana la'akari da ita a matsayin mai bin diddigi bayan ta zama mace Bakar fata tilo da ta zama shugabar babban kamfani 40 a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Johannesburg lokacin da aka nada ta a matsayin shugabar zartarwa ta Bidvest a shekarar 2020.
Tana kuma cikin shugabannin rassan kamfanin 16, in ji Forbes.
Ngozi Okonjo-Iweala
Masaniyar tattalin arziki 'yar Nijeriya Ngozi Okonjo-Iweala, mai shekaru 70, ta kasance mace ta uku a Afirka mafi karfin fada a ji a shekarar 2024.
A watan Nuwamba, aka sake nada ta a karo na biyu a matsayin Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya.
Ta zama mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da ta riƙe muƙamin a watan Maris ɗin 2021.
A baya, ta rike mukamin ministar kudin Nijeriya sau biyu, daga shekarar 2003-2006 da kuma daga 2011 zuwa 2015. Ta kuma rike mukamin ministar harkokin wajen kasar na gajeren lokaci a shekarar 2006.
Samia Suluhu Hassan
Mace ta farko a Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, mai shekaru 64, ta kasance mace ta hudu mafi karfin iko a Afrika, kuma ta 91 a duniya, a cewar Forbes.
Ta hau kujerar shugabar kasa daga matsayin mataimakiyar shugaban kasa a watan Maris din 2021 bayan mutuwar Shugaba John Magufuli.
A watan Satumban 2021, ta zama shugabar ƙasa mace ta biyar a Afirka da ta yi jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, in ji Forbes.
Shahararriyar 'yar jaridar Nijeriya Mo Abudu, mai shekaru 60, ta kasance mace ta biyar mafi karfin iko a nahiyar Afrika kuma ta 97 a duniya.
Forbes ta bayyana ta a matsayin daya daga cikin mata masu karfi a kafafen yada labarai na duniya.
A shekara ta 2006, Abudu ta kafa gidan talabijin na Ebonylife TV, wadda ke watsa shirye-shiryenta a kasashe sama da 49 a fadin Afirka, da kuma Burtaniya da ma yankin Caribbean.
Yarjejeniyar da kamfaninta ya yi da Netflix ta zama karo na farko da wani kamfanin watsa labarai na Afirka ya yi da katafaren kamfanin.