Bukin AMAA na 2023 ya samu jar darduma inda sanannun masu shirya fim suka ji dadin bukin. Hoto: Wasu

Daga Charles Mgbolu

Jarumai da masu shirya fina-finai daga bangarori daban-daban na nahiyar Afirka sun taru a kan jar darduma a wajen bukin bayar da kyaututtuka na Africa Movie Academy Awards (AMAA) karo na 19 da aka gudanar a ranar Lahadi, 29 ga Oktoba don murnar nasarorin da aka samu a fannin a 2023.

Wadanda suka samu kyaututtukan sun fito daga nahiyar Afirka, inda mai shirya fina-finan Senegal Moussa Sene Absa ya gabatar da shirin Xale da ya samu Fim Mafi Kyau, yayin da mai shirya fim ta kasar Burkina Faso Apolline Traore ta samu kambin darakta da ya fi kowanne.

Fim din Mami Wata na mai shirya fina-finai na Nijeriya C.J 'Fiery' Obasi ya samu kyaututtuka mafiya yawa. Hoto: Obasi Instagram

Fim din Mami Wata na mai shirya fina-finai na Nijeriya C.J 'Fiery' Obasi ya samu kyaututtuka mafiya yawa - Shirin Dacewa da Sinima Mafi Kyau da kuma Shirin da Ya Fi Kowanne Kwalliya.

Sauran fina-finan da suka lashe kambi sun hada da shirin Anikulapo na Kunle Afolanya wand aya lashe Kambin Ousmane Sembene na Shirin Fim Mafi Kyau da Aka Shirya da Yaren Afirka, inda Jude Idana, darakatan shirin Kofa ya lashe Kambin Michael Anyiam Osigwe na Fim MAfi Kyau da Daraktan Afirka ya bayar da umarni a yayin da yake rayuwa a kasar waje.

Shirin Anikulapo na Kunle Afolanya wanda ya lashe Kambin Ousmane Sembene na Shirin Fim Mafi Kyau da Aka Shirya da Yaren Afirka,

Kambin Jarumi Mafi Nagarta ya tafi hannun jarumin Nijeriya Tobi Bakre, inda Kambin Jaruma mafi kwarewa kuma ya tafi ga jarumar Nijeriya Nse Ikpe-Etim.

A bangaren tasauwuri kuma, "Jabari" da kamfanin Animax FYB na kasar Ghana ya samar ya samu Kambin Jubril Malaifia na Tasawwuri mafi kyau.

Yana tsaye da jaririyar da aka haifa masa, tare da kambin da ya lashe, Tobi Bakre ya yabi malamansa da suka raine shi a sana'ar.

Ya ce "Ina mika godiya ta musamman ga kowa d aya kasnace wani bangare na wannan tafiya tawa tin daga fari. Duk wanda Allah Ya sa ya zama wani bangare namu. Ina addu'a Allah Ya yi albarka.

"Ina addu'a duk abun da kuka taba ya koma zinariya!!! Mun lashe mun lashe!!! Afirka muna nan" in ji shi a wani sako ta shafin Instagram.

C.J 'Fiery' Obasi' ma ya yabi wannan kambi ta shafinsa na Instagram ind aya kira shi karramawa.

Ya rubuta "Na ji karramawa da MAMI WATA da ya wakilci Nijeriya fasgen Kasa da Kasa. Ina godiya ga 'yan tawagata, dukkan masu daukar fina-finai na, da suka kasance da mu wajen wannan gwagwarmaya, Ina son ku!"

A kowacce shekara ake gabatar da Bukin Bayar da Kyaututtukan Fina-Finai na 'Africa Movie Academy Awards' inda kwararru daga Afirka da wajen nahiyar suke samun kambi a bangarori daban-daban. Bukin na da manufar karrama kwarewa a wannan al'ada.

Shahararriyar mai shirya fina-finai ta Nijeriya marigayiya Peace Anyiam-Osigwe wadda ta rasu a watan Janairun bana ce ta ƙirƙiri bikin ba da kyaututtukan.

TRT Afrika