Mashahuran Afirka da aka zaba don shiga Gasar Kambin Brits ta 2024

Mashahuran Afirka da aka zaba don shiga Gasar Kambin Brits ta 2024

A ranar Asabar, 2 ga Maris 2024 za a gudanar da bukin lashe Kambin Brits. a O2 Arena da ke Landan.
Shahararren mawakin Nijeriya Asake na daga wadanda aka zaba don shiga gasar Kambin Mawakin Kasa da Kasa. Hoto: Getty Images

A kowacce shekara shahararrun mawakan Afirka na samun wajen zama a fagen wake na duniya inda suke lashe kambin da ke jan hankalin duniya.

Bayan shiga gasar Grammy 2024 a bangarori daban-daban, shahararrun mawakan Afirka sun kuma samu gurabe a jerin wadanda za su shiga gasar '2024 Abrits Awards'

Burna Boy, Rema, Libianca, Asake, da Tyla na cikin wadanda aka zaba don shiga gasar ta '2024 Brits Awards', za su fafata a bangarori daban-daban.

Mawakan Nijeriya Burna Boy da Asake, na takarar samun Kambin Zakaran Kasa da Kasa tare da Gwarazan Amurka Taylor Swift, Miley Cyrus, Sza, Olivia Rodrigo, da Lana Del Rey.

Sauran bangarori

Rema ya shiga jerin wadanda ke neman Kambin Wakar da ta fi kowacce a duniya, saboda wakarsa ta 'Calm Down'.

Wakar Water da mawakin Afirka ta Kudu Tyla na neman lashe kambin Wakar Kasa da Kasa.. Hoto: Getty Images

Mawakiyar Kamaru kuma Ba'amurkiya Libianca da Tyla daga Afirka ta Kudu sun samu shiga takarar Wakar Kasa da Kasa Madi Kyau, saboda wakokinsu na 'People' da 'Water'.

Mawakin Pop Raye ne ya fi samun guraben takara da yawa, wand aya kafa tarihi a Gasar Brit ind aya zama mawaki na farko da ke takara a bangarori har guda bakwai.

A ranar Asabar, 2 ga Maris 2024 za a gudanar da bukin lashe Kambin Brits karo na 44, a O2 Arena da ke Landan.

TRT Afrika