Diamond Platnumz na Tanzaniya mawaƙi ne wanda ɗaukakarsa ta samo asali daga sha'awar son waƙa da jajircewa da basirarsa.
Diamond, wanda sunansa na asali Naseeb Abdul Juma, an haife shi ne a ranar 2 ga Oktoban 1989 a Tandale, wata unguwa a babban birnin kasuwancin Tanzaniya Dar es Salaam.
Ya fito daga zuri'a masu tawali'u, sai dai Diamond ya yi ƙuruciya mai cike da ƙalubale da yawa. A wani zamani ma sai da dole ne ya koma wajen kakarsa da zama.
Mawaƙin ya tashi ne a hannun mahaifiyarsa, Sanura Kassim, wacce ake kira da Sandra.
Diamond ya yi karatun firamare a Tanzaniya daga 1995 zuwa 2002, sannan ya shiga makarantar sakandare. Bayanai sun nuna cewa ya kammala karatun sakandare a shekarar 2006.
Bayan haka, ya gwada yin ayyuka da yawa, ciki har da sayar da gwanjo da aikin ba da mai a gidan mai da ɗaukar hoto.
Amma duk wannan lokacin, ya ci gaba da burin son zama mawaƙi. A baya ya bayyana cewa ya sayar da zoben mahaifiyarsa ne domin ya samu kudin bude sutudiyon waƙa.
"Toka Mwanzo", waƙar da aka saki a 2006, ita ce rikodin farko na Diamond, amma sai da ya jira har zuwa 2010 don samun nasararsa ta farko ta "Kamwambie", wadda ta mamaye Gabashin Afirka.
A cikin waƙar Swahili, mawaƙin ya nemi wani abokin abokinsa ya je ya gaya wa tsohuwar matarsa cewa har yanzu yana sonta, kuma kada masu kuɗi su sa ta raina shi.
Bayan wakar "Kamwambie", sai tauraruwar Diamond ta fara haskawa. Manyan wakoki irin su "Mbagala" da "Nitarejea" da "Mawazo" da "Kesho" da "Ukimuona", da dai sauransu sun biyo baya, wadanda suka tabbatar da matsayin mawakin a cikin zukatan dimbin masu jin harshen Swahili.
Bayan samun magoya baya a Gabashin Afirka, Diamond ya ga akwai bukatar ya samu ƙarin masoya a wasu wuraren, lamarin da ya sa ya hada kai da mawakan wasu sassan Afirka da nufin fadada tasirinsa.
Davido na Nijeriya ya taimaka wa Diamond shiga kasuwannin Afirka ta Yamma ta hanyar wakar "Number One Remix". Sauran mawakan Nijeriya da ya yi aiko da su sun hada da Flavour da Waje da Chike da Patoranking da dai sauransu.
A Afirka ta Kudu, Diamond ya fito a cikin wata waka tare da marigayi mawaki AKA a cikin wakar da ta yi fice mai suna "Make Me Sing", yayin da a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, ya sha yin waka tare da marigayi Papa Wemba, da kuma fitaccen dan wasa Koffi Olomide, ciki har da shahararriyar waka ta "Waah".
A wasu wuraren ana ganin dan Tanzaniyan a matsayin wanda ke iya taka kowace irin rawa, saboda yadda ya iya waƙa da rawa da yin wasa da kuma canza salonsa.
Yadda za a tabbatar da cewa ya iya taka kowace irin rawa, mawakin ya kuma zama ƙwararren ɗan kasuwa ne, tare da saka hannun jari a wurare da dama ciki har da kafofin watsa labarai.
Diamond Platnumz ya lashe aƙalla lambobin yabo 28, ciki har da na MTV Europe Music Awards da Channel O Music Video Awards.
An san matashin mai shekaru 34 da wasu sunayen laƙabi, kamar su Chibu Dangote, sunan da ya bai wa kansa wanda ke da alaƙa da hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote na Nijeriya.
Diamond na cajin tsakanin dalar Amurka 70,000 zuwa 100,000 a kowane wasa, a cewar kamfaninsa.
Mawaƙin, wanda ke da arzikin da ya kai darajar miliyoyin dalar Amurka, yana da 'ya'ya huɗu da mata daban-daban suka haifar masa a Uganda.