Lupita Nyong’o ta shirya kuma ta ba da umarni fina-finai. / Hoto: Reuters

Lupita Nyong’o, sananniyar tauraruwar fim da ta taba cin kyautar Oscar za ta shugabanci tawagar alkalai ta kasa da kasa, a bikin nuna fina-finai na Berlin International Film Festival.

Za a yi bikin ne a watan Fabrairu, in ji wata sanarwa da ta fito ranar Litinin, daga masu shirya bikin.

Bikin na “Berlinale 2024” wanda shi ne sahun farko a bukukuwan nuna fina-finai a nahiyar Turai a shekara, zai gudana daga 15-25 na Fabrairu.

Zai kasance na karshe karkashin shugabancin babbar darakta Mariette Rissenbeek, da daraktan fasaha Carlo Chatrian.

Sanarwar daraktocin bikin ta ce, Nyong'o “ta cika abubuwan da muke sha'awa a harkar fina-finai: wato iya taka kowace rawa a duk wani shirin fim, da iya magana da masu kallo mabambanta, da gwanintar salo da aka san ta da shi”.

Nyong'o ta ce ta yi "matukar alfahari” cewa za ta shugabanci tawagar alkalan ta kasa da kasa, kuma tana fatan “gudanar da bikin da zai kalli muhimman ayyukan masu shirya fina-finai daga fadin duniya.”

Masu ba da umarni da shiryawa

Tauraruwar wadda aka haifa a Mexico, wadda iyayenta 'yan Kenya ne, ta shirya kuma ta ba da umarnin fim, sannan ta fito a fina-finai. Haka nan ta rubuta littafin labarai na yara, mai suna, “Sulwe.”

Lupita ta ci kyautar Oscar a matakin babbar mai taimakawa jarumi, a shekarar 2014, saboda rawar da ta taka a fim din “12 Years A Slave.”

Masu shirya bikin sun saba ambata sauran 'yan tawagar alkalan dab da fara bikin. A badi dai, tawagar ta samu mambobi bakwai karkashin tauraruwa Kristen Stewart, inda suka zabi wadanda suka ci gasar, kuma suka ba da babbar kyautar Golden Bear ga darakta Nicolas Philibert dan Faransa, kan dokumentari mai suna “On the Adamant.”

Labarin nada Lupita Nyong'o a matsayin shugabar alkalan ya zo ne kwana daya kafin ministan al'adu na Jamus, Claudia Roth, ya shirya sanar da wanda zai karbi ragamar bikin daga Rissenbeek da Chatrian.

Roth ta ce daga yanzu, bikin zai gudana ne karkashin jagorancin mutum guda .

TRT Afrika