Gari ne da ke samun karuwar jama’a da sauri-sauri, kuma yana habaka sosai.
A kowacce rana, daruruwan mutane na zuwa garin don neman nasara.
Birnin mai habaka, sai ya zama kamar wani mafarkin Afirka. Gari ne da ke da dukkan damarmaki.
Wakilin TRT na sashen Faransanci ya zazzaga Kamaru daga gabas zuwa yamma da kudu da arewa daga don samo muku bayanai kann wannan kasa.
Ziyarar tasa ta fara ne da babban birnin Kamaru Yaounde don yin nazari kan abubuwan da ya shahara da su.
Duk maziyarcin da ya je Yaounde a karon farko, zai fara tunanin ya shiga wata duniyar kwarran bishiyoyi ne.
Tun daga unguwannin talakawa zuwa na masu kudin gaske da ke nuna wadata, akwai tsananin cunkoson ababen hawa da cuncurundon mutane.
Yaounde na yi wa sababbin zuwa garin maraba da manyan karafansa da babbar majami’arsa da manyan unguwanninsa da korayen ganyayyaki da tsirrai masu aikewa da sakon jin dadi na musamman.
Garin yana yankin tsakiyar Kamaru ne kuma yana marabtar maziyartansa da yanayin bazara irin na Indiya, inda yanayi yake yin lif-lif bayan an sha fama da zafi.
Mamaki na farko shi ne na launi. A Yaounde launin shudi na da haske kamar ruwan makuba, irin launin shudin da ya sha bamban da korayen ganyayyakin bishiyar ayaba da na rogo.
Launin shudin sararin samaniya ya mamaye launin ja da ke kan tuddan garin.
Ba ka saba da rikici da rigingimun yankin ba, amma a karshe za ka karbe su har ma ka saba da su.
Sannan ba za mu iya yin biris da barazana mai nisa ta masarautar baunaye ba, dajin da a baya ya zagaye cibiyar taro, a yanzu ya zama babban abun alfahari ga dukkan ‘yan kasar Kamaru.
Gari ne da yake dauke da daya daga cikin sanduna bakwai. Gari ne da ke da tsaunuka bakwai, kabilu bakwai, mata kyawawa guda bakwai, manyan dakunan taro bakwai da yaruka bakwai.
A don haka za a iya ce masa garin bakwai-bakwai.
Kyawun yanayi
A gefen hanya mai layuka hudu da aka kammala da ke da ban sha’awa, akwai bishiyoyi da aka yi ado da su kamar wasu janar-janar na soja. Akwai hotunan ‘yan takara na siyasa a kakkafe.
Ba zata, kana fitowa daga wata kwana, sai kawai ka ga wadi a gabanka kuma babu komai, babu alamun sakafa, kawai dai za ka yi ta ganin bakin kwaltar ne a malale.
Labari
A ranar 30 ga Nuwamban shekarar 1889 ne wani masani kan tsirrai dan kasar Jamus Georg August Zenker, ya gano inda garin yake.
Sai ya saka masa suna Yaounde, sunan da aka samo daga masu barar gyadar yankin.
Babu wani abun a zo a gani a wannan gari saboda a baya-bayan nan ne aka gina babban kantin saye da sayarwa na farko a birnin.
Akwai filin wasanni na Olembe, wanda ya kasance babban dandalin wasanni ne.
Ita kuma Unguwar Nkoldongo, unguwa ce da aka gina da tsarin Amurka wadda wani bangare ce na tarihin birnin.
Yaounde na nan a kan wani tsohon dutse da dukkan mazaunansa sun san shi saboda ingancin da tabon da ake samowa daga cikinsa yake da shi.
Akwai baki daga kasashe makota da ke zaune a Yaounde irin su Ekutoriyal Gini da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Gabon.
Wadanda suka san garin a zamanin baya na iya tunawa da ginin da jami’an gwamnati suka zauna.
Wakilin TRT ya samu ganin gida na farko da aka gina a Yaounde. An yi rufin gidan da tubalai da aka samar da tabo, a gidajen sarrafa duwatsu na Yaounde.
Ya kuma ga gidan gwamna Bajamushe Hans Dominik wanda jama’ar wajen suke kira Dominiki.
Tarihi ya bayyana yadda yake amfani da munanan hanyoyi wajen hukunta ‘yan tawaye da masu adawa. Don haka akwai gidan gyaran hali da kotunan ladaftarwa da tanada.
A kowacce rana wadannan tubalai masu tarihi na ci gaba da bayar da labarin birnin ga masu wucewa da masu yawon bude ido.