Daga Charles Mgbolu
Yare shi ne jinin da al'umma ke rayuwa da shi, hanya ce da ake amfani d aita wajen isar da ilimi, fasaha da al'adu daga wata al'umma zuwa wata, ana tabbatar da cigaba da tsira.
Wani abu da ke tabbatar da wajabcin hakan shine bayanin da ke cikin fim din darakta dan kasar Canada Deniz Villeneueves da ya rubuta a 2016 mai suna 'Arrival', wata hikaya ce da ke bayyana yadda wanzuwar dan adam ta dogara kan fahimtar yaren halittu,
Masanin ilimin harshe Louise Banks na da ra'ayin cewa jarumar fim din na ta kokarin fahimtar abinda dodanni suke fada. a yayin da take zagaya wa a cikin sauti, da hawa da saukar sa da ke bayyana wannan yaren.
Fahimtar Louise na tabbatar da muhimmancin da ke akwai wajen magance babbar musiba a duniya. Amma wannan kagaggen labari ne.
A gaskiyance, dukkan al'ummu na bata ne a lokacin da yaren da suke magana da shi ya mutu. Geez, Gafat, Memes, Vazimba, Kw'adza, da Ngasa - duk daga Gabashin Afirka - a yanzu suna nan ne a wani dan yanki.
UNESCO ta ware wasu yaruka a matsayin wadanda "Ke fuskantar barazana", tana cewa wadannan za su iya mutuwa idan ba a kawo musu daukin gaggawa ba.
A 2006, UNESCO ta ayyana yaren Igbo wanda sama da mutane miliyan 20 ke magana da shi a gabashin Nijeriya, a matsayin 'mai fuskantar hatsari'.
Wannan yanayi ne ya sanya wasu daga cikin malaman yaren, kafafan yada labarai da masana hana hannu waje guda don kubutar da yaren daga mutuwa. kusan shekaru 18 baya, masu magana da yaren Igbo irin su Oluchi Akachukwu na da damuwar wannan barazana ba za ta kau ba.
Daidaituwar asalin mutane
Oluchi ta shaida wa TRT Afirka cewa "Ina jin akwai wasu a zamaninmu na yau na alakanta kansu da zamani suna manta wa da asalinsu, ciki har da hakura da yarensu."
Mai fasahar na ta yin kokarinta tsawon shekaru hudu, tana amfani da shafukan sada zumunta don koya wa yara harshen Igbo.
Ta fara aikin nata a 2020, bayan ta haifi danta na biyu. Yaronta na farko na magnaa da yaren Turancin Ingilishi kuma na iya kirge har zuwa 100 a yaren Faransanci.
"Ina tuna wa sanda na ke kallon sa yana kai komo a cikin wadannan yaruka, a koyaushe sai na tambayi kaina 'Yaya yarona ba zai iya magana da yarensa na asali ba?' hakan ya dame ni." in ji ta.
Sai kwarin gwiwa ya zo. "Na yanke shawarar koyar da yaren Igbo ba ga yarana kawai ba, har ma ga dukkan yarann Igbo ta kafar Youtube da suaran shafukan sada zumunta na yanar gizo," in ji Oluchi.
Gwagwarmayar mutum guda
Aiki ne gagarumi. Oluchi ta tattara dukkan kudadenta da ta juya wa, ta nufi wajen masu sanar zane mai motsi. "Babban hoto mai motsin da na yi shi ne na wakar Ingilishin makarantar rainon yara, 'Old McDonald had a farm', a cikin yaren Igbo. An sake ta a watan fabrairun 2021.
Oluchi ta dinga yin gwagwarmayar rike karsashinta a yayin da take zumudin kallon yaranta na kura ido kan hotuna masu motsi bayan an sake su. "Na yi matukar farin ciki. Na samar da wannan, abu ne na musamman gare ni yadda yarana suka ji dadin kallon bidiyon. Hakan ya ba ni karfin gwiwar yin wasu," in ji ta.
Aikin da Oluchi ke yi ya shiga batutuwan barazanar da yaruka da dama ke fuskanta a Afirka da ma wajen nahiyar.
Zaizaya a hankali
A kasa da shekaru 10 da suka wuce, yaruka 7,000 da ake magana da su a duniya sun mutu. Mafi yawancin su yaruka ne kanana da suka fuskanci barazanar mutuwa.
'Ethnologue', wani dab'i da ake yi duk shekara a tkarda da yanar gizo na samar da alkaluma da sauran bayanai kan yarukan duniya da ke raye, kuma ya bayyana ya zuwa 2001 akwa yaruka masu rai 7,358 a duniya.
Ya zuwa 20 ga watan Mayun 2015, an bayyana akwai yaruka masu rai 7,102 a duniya. A ranar 23 ga fabrairun 216, Ethnologue suka bayyana akwai yaruka 7,097 a ban kasa.
Masana harshe sun yi gargadi kan abinda suka kira 'mutuwar yare a sirrance' wadda ita ce hanya mafi shahara da yarukan ke mutuwa.
"Mutuwar yare a hankali na faru wa ne idan mutanen da ke magana da yaren suka yi mu'amala da jama'ar da ke magana da yaren da suke kallon ya fi nasu matsayi.
Da farko wadannan mutane na zama masu magana da yaruka biyu, sannan zamani na tafiya, suna rasa karfin magana da nasu yaren, kuma a karshe zai zama babu mai magana da yaren," in ji Dr Nabuife, mataimakin farfesa na yaren Igbo a Jami'ar Lagos.
Tasirin yin hijira
Domin ganin yadda abubuwan suka munana, 'yan shekarun da suka gabata sun ga yadda miliyoyin matasan Afirka ke kaura zuwa wajen nahiyar don neman arziki a kasashen waje.
Kungiyar Kula da Gudun Hijira ta bayyana cewa kusan 'yan gudun hijirar Afirka miliyan 40.6 ne suke zaune a Turai.
"Ina tsoron da yawa daga cikin su za su girma d iyalansu kuma yaransu a sa iya magana da yarensu na asali," in ji Oluchi cikin takaici.
Kokarin da take yi a kafafan sada zumunta kamar mai hawa sama ne ya taka leda, amma tana yin tasiri sosai.
Masu koyo ta shafinta na Youtube na ta karuwa sosai, a tasharta mai suna "Kpakpando" (Star) inda a yanzu take da mabiya sama da 5,000 d akuma kallo 900,000.
"Adadin na karuwa da gaske," in ji Oluchi. "Ina godiya matuka da yadda wannan e ba ni damar amfanaar da yaran da ne ke isa gare su."
"Tana da burin yin bidiyo a fasahar 3D, amma samun kudade ne kalubalenta. "kwanan nan aka kawo min bukatar na biya $1,500 (Naira miliyan 1.7) don shigar da hotunanta kan fasahar 3D.
Sai na tambayi kaina, "Ina zan samu wannan kudi? Gaskiya hakan ya yi tsada sosai ga abinda na ke son yi.
Amma Oluchi ba ta tsorata ba. Tana fatan cewa kowanne yaro da ya girma yana koyon yaren Igbo ta wanna kafa zai amfana da kokarin nata.