Aid by Turkish NGOs to restore ties with Nigeria / Photo: AA

Akwai mutane sama da biliyan biyu da ke fama da rashin ruwan sha mai tsafta, musamman a Afirka sakamakon dalilai na muhalli, da rashin kayayyakin aiki, da fari da sauran kalubalen zamantakewa da siyasa.

Wannan kokari na Turkiyya da ‘yan Turkiyya ya samar da jiriyoyin ruwan sha, da madatsan ruwa a fadin nahiyar.

Ga jerin ayyukan samar da ruwa wadanda kungiyoyin da gidauniyoyin ba da tallafi suka aiwatar a Afirka.

Cibiyar Hadin Gwiwa da Daidaton Cigaba ta Turkiyya, wato Turkish Cooperation and Coordination Agency (TIKA), sun aiwatar da tarin ayyukan gina rijoyoyin da tsaftace ruwa a matakin yaki da na kasa.

Cibiyar ta tona rijiyoyi 303 a yankuna daban-daban, da suka hada da yankuna 80 a Nijeriya, 27 a Habasha, 41 a Sudan, 78 a Burkina Faso, 30 a Mali, da 17 a Somalia. Duka wauraren nan suna da tsananin bukatar tsaftataccen ruwan sha.

a Somalia, cibyar TIKA ta gina rijiyoyin ne karkashin wani shiri na samra da ruwan sh mai tsafta, wato Somalia Clean Water Access Project. An samar da rijiyoyi 19 da tankunan ruwa da bututun daukar ruwa da kuma famfuna domin tallafawa dubban mutane a yankin.

A kasar Habasha kuwa, an gina ma’adanar ruwa a Lardin Shinille domin magance matsalar ga al’ummar yankin.

Haka ma a Sudan, TIKA ta samar da ruwa ga al’ummomi matalauta da ke jihar kudu maso gabashin kasar, wato Jihar Sennar. An gina musu bututn ruwa mai tsayin kilomita 3, da tankin ruwa mai daukar tan 40, da dakunan wanki, da injin jan ruwa na lantarki.

Har ila yau, a Djibouti, kamfanin State Hydraulic Works na Türkiyya, shi ya gina madatasar ruwa ta Ambouli Friendship Dam, a wajen da ake fama da ambaliyar ruwa, inda kuma kashi 75 cikin dari na al’ummar kasar ka zama.

Aikin madatsar ruwa za ta kawar da matsalar ambaliya, da kuma samar da ruwan noma, sannan da ruwan sha ga mutanen yankin.

Gidauniyar Türkiye Diyanet Foundation (TDV), wata cibiya ce karkashin Hukumar Harkokin Addini, wadda ta samar ruwan sha mai tsafta ga miliyoyin mutane.

A karkashin shirinta na Digon Rayuwa, wato “a Drop of Life", gidauniyar ta gina sabbin rijiyoyin samar da ruwa guda 890 da famfuna, a kasashen Afirka kamar Burkina Faso, da Nijar, da Togo.

Akwai kuma kungiyar tallafi ta Turkish Red Crescent (TRC), wadda kwanan nan ta da ba da gudomowar rijiyoyi masu aiki da hasken rana wajen samar da ruwan sha. An kaddamar da ayyukan ne ga al’ummomin lardin Kayunga a tsakiyar kasar Uganda, da nufin tallafawa gidaje 100 da ke fama da karancin ruwa, da matsalar taftar ruwan sha.

Selçuk Öztürk, shi ne shugaban ayyukan kasa da kasa a kungiyar ta TRC. Ya ce sun bude rijiyoyi 20 a shekarar 2021, tare da hadin gwiwar kungiyar Uganda Red Cross Society.

Ya kara da cewa kowace rijiya tana da tankin ajiye ruwa mai daukar kubik mita 10, da famfuna 15 masu iya samar da ruwa kullum

Kungiyar na da kudurin saukakawa al’ummomi ajen samun ruwa, a kasashe shida, Chad, Niger, Senegal, Somalia, Uganda da Sudan.

Shirin da gwamnatin Turkiyya ta kaddamar a Afirka don magance matsalolin samun tsaftataccen ruwan sh, da tsaftar muhalli, yana gudana a yankuna da dama a fadin Afirka.

TRT Afrika