Koffi Olomide ya hada aƙalla kundin wakoki 28 a aikinsa wake-wake da ƙide-ƙide. Hoto: Koffi Olomide  

Duk da cewa shekarunsa sun kai 67 a duniya, har yanzu Koffi Olomide yana da sauran kuzarinsa domin kuwa zai sa matasa maza gudu wajen neman kudi a filin rawa.

Mawakin ɗan asalin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ne wanda ya shahara da irin tufafin da yake sanyawa masu Kala da daukar ido wanda galibi ya an hada shigar matsassun riguna da manyan wanduna.

Wasu daga cikin sunayen da aka fi sanin Koffi da su sun hada da Le Grand Mopao - ma'ana babban shugaba, a zahiri sunan Koffi- wanda ya ke rera waka a harshen Lingala- ya jagoranci salon nau'in wakar Soukous a sama da shekaru 40.

A lokacin da wasu ke tunanin zai daina waka a cikin ƴan shekaru kaɗan, ya ci gaba inganta kansa wajen ƙirƙira wasu wakokin don samun karbuwa daga al'ummomi daban-daban masu sauraronsa.

Koffi ya soma harkar waka ne da ƙungiyar Papa Wemba. Hoto: Wasu

Mai shekara 60 yana sauraron Koffi, haka kuma dan shekara 20 na sauraron Koffi… Wannan shine labarin Le Grand Mopao.

An haife shi ne a ranar 13 ga watan Agusta, 1956 a garin Kisangani da ke arewa maso gabashin jamhuriyar dimokradiyyar Kongo, ainihin sunan Koffi, Antoine Christophe Agbepa Mumba.

Sunansa na farko Antoine, sannan sunan da aka sanshi na wakensa shi ne Olomide, akwai labarin da ya biyo bayan sunan. Lokacin da aka haifi Koffi, mahaifinsa ba ya nan.

Abubuwa da dama sun dagula lamura a lokacin, domin mahaifiyarsa ta kasa samun madarar nono. Wata maƙwabciyarta ce ta shayar da Koffi, don ya nuna godiyarta, mahaifiyar Koffi ta sa masa sunan mijin maƙwabciyarta, Antoine.

Sunan Olomide ya samo asali ne daga harshen Yarbanci - Olumide - ma'ana "Allahna ya zo." Mahaifiyar Koffi ta hada ruwa biyu wato rabin ta 'yar Nijeriya ne da Saliyo.

Koffi Olomide sananne ne a irin salon waƙensa na musamman. Hoto: Koffi Olomide

Tun yana ƙarami Koffi ya soma sha'awar kada garaya, ba tare da sanin cewa gayarar ce za ta kasance ɗaya daga cikin kayan kiɗan da za ta ɗaukaka shi zuwa ga shahara a duniya ba.

Salon wakokin Soukous da Rhumba da kuma Makossa suna daga cikin kundin da Koffi ya fi kyauna. Duk da ya nuna sha'awarsa ta kiɗa, Koffi ya kasance ɗalibi mai mayar da hankali a makaranta, inda yake kan gaba a darussan kimiyya.

Iyayensa sun kai shi birnin Paris na kasar Faransa inda ya karanci digirinsa na farko a fannin kasuwanci sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin lissafi.

Bayan ya koma DRC a shekarun 1970, Koffi ya daura kan burinsa na yin waƙa da fasaha a matsayin sana'a.

Ya shiga ƙungiyar Papa Wemba Viva La Musica a ƙarshen shekarun 1970.

Ya kasance jigo a kungiyar har zuwa shekarar 1986, lokacin da ya tafi ya kafa tsa kungiyar mai suna Quartier Latin International.

Kungiyar ce ta taimaka masa wajen tsara ayyukan wakensa na Fally Ipupa da Ferre Gola da Cindy Le Coeur da dai sauransu.

Koffi ya fitar da kundin wakokinsa na farko a shekarar 1989, tun daga lokacin tauraronsa ya ke ta haskawa.

Ya hada aƙalla kundi wakoki 28, inda ya samu lambobin yabo da dama a wannan tafiya.

Koffi da abokiyar aikinsa, Aliane, wacce ya aura a 1993, suna da yara da yawa tare.

A kokarin kutsawa cikin kasuwannin Afirka baki daya, Koffi ya hada kai da mawakan matasa da dama wadanda suka hada da Davido na Nijeriya da Diamond Platnumz na Tanzaniya da dai sauransu.

A yanzu – duk da cewa ya kusan kaiwa shekara 70 – wani sashe na masoya wakokinsa sun amince da cewa suna duniyar Koffi ce, kuma a cikinta kawai suke rayuwa.

TRT Afrika