Daga Mazhun Idris
A ‘yan kwanakin nan, an yi ta tafka muhawara a zaurukan sada zumunta a Arewacin Nijeriya, bayan kalaman wata jaruma a masana’antar Kannywood game da matsanancin kuncin da ta shiga sakamakon jarababbiyar soyayyar da take yi wa wani jarumi.
Rakiya Mousa ta yi kalaman ne a hirar da fitacciyar tauraruwar nan ta Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi da ita a shirin da take gabatarwa a YouTube.
Ba ta fito kai-tsaye ba ta bayyana sunan masoyin da take magana a kansa, amma tuni jita-jita ta watsu cewa fitaccen mawakin nan ne Hamisu Breaker. Ko da yake ya wallafa sako a shafukansa na soshiyal midiya yana nesanta kansa da wannan batu.
A iya cewa jarabar so na Rakiya Mousa ne ya fito fili, amma a hakikanin gaskiya akwai dumbin mutane da a baya da kuma yanzu suka sha samun kansu cikin taskun soyayya, ba ma a Nijeriya ko Afrika ba, har a fadin duniya baki daya.
Ko a labarai irin na kunne ya girmi kaka an san yadda labaran soyayyar Laila da Majnun da kuma Romeo da Juliet suka yi tashe, wadanda dukkan su masu nasaba ne da matsananciyar soyayya.
Matsananciyar soyayya ta sha saka mutane cikin tasku iri-iri, a wasu lokutan ma har a kai ga haduwa da ciwon zuciya ko na hawan jini, ko a rasa rai baki daya.
To ko me ya kamata a yi don magance afkawa cikin hadari saboda irin wannan “wahaltacciyar soyayyar”?
TRT Afrika ta tuntubi masana dabi’a da tunanin dan Adam kan hanyoyin da mutum kan iya bi don shawo kan matsananciyar soyayya, da kuma samun waraka daga dafin soyayya ko damuwa sakamakon rashin nasara a soyayya.
Shin akwai cutar so?
TRT Afrika ta tambayi wata kwararriya kan zamantakewa da matsalolin aure a Nijeriya, Malama Hannatu Bilyaminu ko akwai cutar so?
“Tabbas akwai cutar so, sannan akwai ma cutar da fi ta so, wato ta naci, wadda ta fita daga zangon soyayya, ta koma kamar jarraba.”
Bayanin Malama Hannatu, wadda ke bai wa mutane horo kan kyautata halayya da zaman iyali, ya nuna cewa naci da jarabar soyayya kan bi matakai ne kafin ta kai koluluwa.
“Da farko yawanci mutum yakan ji cewar akwai yiwuwar soyayyar ta samu. Saboda haka sai ya fara shirye-shiryen yadda zai shawo kan wanda yake so, wataƙila ta hanyar kyautata masa, ko kyautata wa makusantansa kamar iyaye ko yayye ko kanne ko abokai.
“Yayin da aka samu akasin rashin cimma burin ramakon soyayya har yunƙurin ƙulla soyayyar ya ci karo da tarnaki kuwa, mutum kan shiga yanayi na fushi da damuwa da taraddadi, ko ma kawai ya ji ba ya son kowa, ba ya son komai,” in ji ta.
Ta ci gaba da cewa “Daga nan kuma sai mutum ya samu rauni a fagen daraja kai, ya kuma fara yanke mu'amala da mutane”.
“Akwai binciken da ya nuna zafin da mutum kan ji idan an yi watsi da shi, ko an ƙi karɓar soyyarsa, yakan shafi ɓangaren ƙwaƙwalwa da ke taɓuwa yayin da dan adam ya ji ciwo na zahiri,” a ta bakin Malama Hannatu.
Shi kuwa Farfesa Maikano Madaki na Sashen Ilimin Halayyar Dan Adam a Jami’ar Bayero Kano, ya yi gargadi mai karfi ga mutane cewa dole su guji azabtar da zuciyoyinsu wajen “azababbiyar soyayya”.
“Irin wannan gigitacciyar soyayyar kan jawo matsananciyar damuwa har ma da taba lafiyar hankalin mutum.
“Ya kamata mutum ya gode wa ni’imar rayuwa da ta lafiya da mutuntaka da yake da ita, ya guji saka kansa a uku,” Farfesa Maikano ya jaddada.
Son mara son ka, ko son wanda ya daina sonka?
Wasu dai na zargin cewa Rakiya ce take tsananin son tauraron amma shi dama bai taba nuna son ta ba, kamar yadda shi da kansa ya bayyana. A takaice dai kamar “son maso wani” ake lakawa matashiyar, wacce har wata waka sun taba yi ita da Breaker.
TRT Afrika ta nemi Malama Hannatu, wacce har takan shirya zaman sulhu na ido-da-ido, ko tattaunawa ta intanet tsakanin masoya da ma’aurata, da ta bambance tsakanin nau’o’in rashin nasara a soyayya tsakanin mata da maza.
Ta ce, “Masana ilimin halayyar ɗan Adam na ganin son wanda ya ƙi sonka ya fi wahala, kan son wanda ya ƙi ka daga baya.
“Dalilin kuwa shi ne, shi wanda bai so ka ba, rashin mu'amalar soyayyar kan sa ya zauna a matsayin wanda kake gani a masoyin da ya fi kowa dacewa”.
A muhawarar matasa da ta gudana a shafukan sadarwa kamar su Facebook, akwai wadanda suka bayyana matsananciyar soyaya da cewa ta dogara ne kan “mafarki mara tabbas”.
Bisa wannan fahimta, soyayyar wanda ba a samu amincewarsa ba, takan wanzu ne a wani yanayi na tunanin wanda kake so din, ba shi da wani aibu ko makusa.
Shi kuwa wanda ya daina muradinka bayan kun fara son juna, akwai yiwuwar a zamantakewar an taɓa samun saɓani har wani aibu ya bayyana.
Maganin radadin rabuwa
A cewar masaniyar zamantakewar, mataki na farko na kaucewa matsananciyar soyayya shi ne sassauta zurfin soyayya da sanya mata linzami.
Ta ce, “Ga Musulmai, wannan na nufin yin soyayya cike da imani da ƙaddara mai dadi da mara dadi. Wannan shi zai kai mutum zuwa ga hakuri da abin da ya afku”.
“Matukar mutum ya auna kokarin da ya gabatar, kuma ya yi amanna cewa ya yi iya yinsa don ceto alaƙar amma abu ya ci tura, to alamu ne na bukatuwar saduda ko dangana, don kaucewa fusata da damuwa”.
Mataki na biyu shi ne, “A yanayi na karayar zuciya na ciwon rabuwa da masoyi, zazzafar rabuwa ko son maso wani, akwai bukatar mutum ya samu wani amininsa ya faɗa masa damuwarsa.
Ana sa ran samun kalamai da dabarun tausasawa da taya alhini.
Mataki na uku shi ne kokarin barin tunanin mutumin da yake so, ya kuma zabi cigaba da rayuwarsa.
A nan ana shawartar masu fama da damuwar rashin samun abin kaunarsu da su takaita mu'amala da su, da kuma kauracewa aikata abubuwan da za su tuna da su, kamar kallon hutunansu ko sauraron sautinsu.
Shiga cikin wasu lamuran rayuwa na daban, kamar hira da iyalai ko abokai, ko kawaye da fita shan iska, ko wasannin motsa jiki, duk suna iya taimakawa.
Mataki na hudu shi ne daukar darasin rayuwa daga abin da ya afku, ta hanyar juya akalar juyayinsu ya koma sabon ilimi.
“Yana da kyau mutum ya ɗauki darasin zamantakewa, ya fahimci abin da ya sa ya faɗa soyayyar, da dalilan da ya janyo rashin nasararsa, don gano inda yake buƙatar gyarawa a mu'amalarsa da wani masoyin nan gaba”.
“Yana da kyau ya jaddada wa kansa cewa rashin samun soyayyar wani ba ya nufin shi bai cancanci a so shi ba, soyayya na cikin ni'imomin rayuwar dan adam”.
Mataki na biyar shi ne maye gurbin wanda kake so a baya, da waninsa, yayin da kake warkewa daga cutar so.
“Wannan na taimaka wa wajen kauce wa sake zurmawa wancan ramin. Misali, maimakon bibiyar tsohuwar zuma, za ka iya fara ziyartar sabuwar zuma, don begen salon sakarta.
“Hakan zai iya hadawa da toshe tsohon kamu ko goge su daga jerin abokai a shafukan sada zumunta, idan ganin su yana tunzura ka,” in ji Farfesa Maikano
Domin samun nutsuwa, a duk yayin da ka ji kamar kana son magana da su, to ka yi ƙoƙarin kiran wani a madadinsu.
A karshe, fahimtar darajar kai da sanin cewa ka cancanci so na haƙiƙa, ba ta ala tilas ba, yana taimakawa.
Sai kuma babban abu da ke rage radadin soyayya ko na rabuwa, wanda shi ne tafiyar lokaci wanda ke zagwanyar da tunanin ko yakinin yiyuwar komawa kogin soyayyar tsohon masoyi.