A 2020 kadai, sama da mutum miliyan 19 aka gano sun kamu da nau’o’in cutar daji daban-daban a duniya / Photo: Getty Images

Wani rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa ana hasashen yawan masu cutar daji a duniya ya karu da kashi 55, ya zuwa shekarar 2040, idan an kwatanta da 2020.

A shekarar 2020 kadai, sama da mutum miliyan 19 aka gano sun kamu da nau’o’in cutar daji daban-daban a fadin duniya.

Hasashen na Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa matukar yawan masu kamuwa da cutar ya ci gaba da zama yadda yake, yayin da yawan karuwar jama’a da kuma tsufa suka ci gaba bi-da-bi, an yi kiyasin za a samu sabbin masu kamuwa da cutar miliyan 28 a duniya, nan da 2040.

Hakanan, ana sa ran samun karin kashi 54.9 cikin 100 na yawan masu cutar idan an kwatanta da shekarar 2020. Sai dai kuma, ana hasashen karin ya kasance kashi 60.6 cikin 100 a maza, sama da mata.

Cutar daji ita ce abu na biyu da ya fi kisa a duniya. Duk shekara, ana gano mutum 734,000 masu cutar. Sannan mutum daya cikin mutum shida da suke mutuwa a duniya a shekarar 2020, cutar daji ce sababi.

A shekarar ta 2020, mutane sama da miliyan 19.2 aka gano sun kamu da cutar a fadin duniya, yayin da sama da miliyan 9.9 suka mutu da dalilin cutar.

Cutar daji a maza da mata da yara

Nau’o’in cutar daji da suka fi addabar maza su ne kansar huhu da kansar mafitsara da kansar dubura da kansar tumbi da kansar hanta.

Su kuwa mata an fi samun su da kansar mama da kansar dubura da kyansar huhu da kansar bakin mahaifa da kyansar makoko.

A duk shekara, kididdiga ta nuna kananan yara 400,000 ne ake ganowa sun kamu da cutar kyansar a fadin duniya.

Dabarun magani

Cutar daji cuta ce mai bukatar dawainiya ta fuskoki daban-daban, kamar kashe kudi wajen yin magani, da kuma kumaji da damuwa wajen kulawa da mara lafiya.

Hakan ya sanya cutar mai matukar wahalarwa, musamman ga mutane da ke rayuwa a kasashe masu matsakaici ko karancin samun kudi.

Dabarun magance cutar kyansa da suka fi shahara su ne:

Tiyata

Gashin inji

Hasken radiation

Juyen bargo

Alkaluma sun nuna cewa gano cutar da kuma daukar mataki kanta a kan kari, zai iya rage mutuwa sakamakon dalilai da suka shafi kansa, da kashi 30 zuwa 50 cikin dari.

Sai dai kash, da yawan adadin masu fama da kansa ba su da damar samun ingantattun hanyoyin gano cutar da kuma magungunanta a kan lokaci.

Yawan masu cutar kansa a Afirka yana ta’azzara saboda sauyi a salon rayuwa da halayyar mutane, da yawan tsofaffi, da zubin kwayoyin halitta, da sauran cututtuka, da kuma yanayin muhalli.

Yayin da aka kiyasta adadin masu cutar ya ninka a yankin Afirka da ke kudu da Sahara cikin shekaru 30 da suka gabata.

Wani kiyasin ya nuna duk shekara mutane miliyan 1.1 a Afirka, za su rasa rayukansu sakamakon cutukan kansa ya zuwa shekara 2030.

TRT Afrika da abokan hulda