Ahmed Musa na daga cikin 'yan wasan Afirka da suke taka leda a Turkiye yanzu/AA

Salon murnar cin kwallo da aka san dan wasan Uganda Majid Musisi da shi na "tafiyar kada", ba nishadi kawai ya sanya a fagen wasa na Turkiyya ba, sai da ya bai wa 'yan wasan Afirka damar zuwa taka leda kasar.

Baya ga Musisi, ‘yan Nijeriya irin su Daniel Amokachi (a Bésiktas) da Jay Jay Okocha da Uche Okechukwu da dan Masar Ahmed Hassan (a Besiktas) da Stephen Appiah na Ghana (a Fenerbahçe) duk sun murza leda a Turkiyya.

Sai kuma dan Afirka ta Kudu John Leshiba Moshoeu (a Fenerbahçe) su ne a sahun farko cikin ‘yan Afirka da suka cigaba da yi wa gasar Super Lig ta Turkiyya ado.

A kakar kwallon kafa ta bana, kimanin ‘yan Afirka 60 ne ke taka tamaula a kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya.

Sun fito daga Senegal da Kamaru da Nijeriya da Ghana da Kongo da Ivory Coast da Mali da Guinea da Angola da kuma Aljeriya.

A kowace shekara, adadinsu na karuwa saboda karfin Gasar Super Lig, da albashi mai tsoka da kayyadadden haraji da ingantattun ababen more rayuwa da kuma magoya baya masu shaukin wasa.

Kwararowa daga nahiya

Idan sha’awar da masoya kwallon kafa ke nunawa ta yi tasiri kan irin tsananin shauki da ake ciki, to yadda ake tafiyar da kungiyoyin da inganci, zai ci gaba da karfafa gwiwar ‘yan wasa ‘yan Afirka cewa suna da kyakkyawar makoma a fagen kwallon kafar Turkiyya.

Jay Jay Okocha ya yi farin jini sosai lokacin da yake taka leda a Turkiyya/AA

Zafin soyayya da magoya baya ke nunawa a cikin filayen wasa da ke cike makil tamkar wata muhimmiyar kadara ce.

Tsohon dan wasa Senegal Ricardo Faty, ya san gasar kwallon kafa ta Turkiyya sarai kuma ya yi imanin cewar mutanen kasar suna tsantsar son kwallon kafa.

“A nan idan mutane suka je filin kwallon kafa, ba zuwa kallo kawai suke ba. Su ma suna zuwa ne tamkar suna taya ka wasan," in ji shi cikin hirarsa da TRT Afrika.

Dan uwan Ricardo, Jacques, wanda ya yi wasa a kungiyar kwallon kafa ta Lazio Roma, kuma ya shafe shekaru da dama a Turkiyya, ya yi amannar cewar masoya kwallon kafa ‘’na cikin’’ wasan kwallon kafa kamar 'yan wasan da suke goya wa baya.

"Sun san za su iya tasiri kan alkalin wasa da tayar da hankalin abokan gaba - hakika, sun zo taya ka wasa ne," in ji shi.

"Gasar Süpa Lig na da ban sha’awa. Ba ta da wahala mai yawa a fagen dabara, baya ga haka gasa ce mai dadin kallo inda ‘yan wasa da yawa suka fito daga kungiyoyi masu dabarar kwallo da karsashin wasa.

Turkiyya kasa ce da kusan ko wane gida ke da kungiyar da yake goyon baya, kuma ma wadanda ba su damu da kwallon kafa ba suna da kungiyar da suke goyon baya. Na yi matukar ji dadin wasa a kasar."

Amokachi ya yi suna sosai lokacin da ya taka leda a Besiktas a Turkiyya/AA

Ga da yawa cikin ‘yan wasan Afirka da ke son su fara taka leda cikin manyan kungiyoyin kwallo na duniya, Turkiyya ka iya zama wata matakala.

Da yawa na da fatan su yi suna a wurin kuma su ja hankalin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai a Ingila da Italiya da Sifaniya da kuma Faransa.

'Yan Afirka sun kawo sauyi

Idan aka koma shekara goman karshe cikin karni na 20, Musisi na cikin ‘yan wasan farko da suka sauya kungiyar kwallon kafar, inda ya koma Bursaspor a kakar 1994 zuwa 1995 daga kungiyar kwallon kafa ta Faransa, Stade Rennais.

Ya kafa tarihi mai kyau ta yadda wasu taurari daga Afirka suka samu suka taka leda da manyan ‘yan wasan Turkiyya.

An samu wata guguwar a shekarun 2000.

Galatasaray ta karbi bakuncin yawancin ‘yan wasa daga nahiyar, irin su Didier Drogba (daga Ivory Coast) da Rigobert Song (daga Kamaru), Shabani Nonda (daga Kongo) da Abdul Kader Keita (daga Ivory Coast) da kuma Younès Belhanda ( daga Moroko).

Drogba na daga cikin 'yan wasan Afirkan da suka taka leda a Turkiyya/AA

Daga cikin wadanda suka taka leda a lokacin, an samu dan wasan kasar Togo Emmanuel Adebayor, wanda ya buga wa Istanbul Basaksehir, tare da Aurélien Chedjou dan Kamaru.

Tsohon dan wasan FC Barcelona da Inter Milan Samuel Eto'o, wanda ake gani a masayin gagara badau a Kamaru da Afirkar gaba daya, shi ma ya taka rawar gani a gasar kwallon kafa ta Turkiye a kungiyoyin Antalyaspor da Konyaspor.

Asamoah Gyan, wanda ya fi zura kwallo a raga a tarihin kwallon kafa a Ghana, ya buga wa Kayserispor.

Saukin aiki

Cigaba da taka leda a kungiyoyin kwallon kafan Turkiyya da ‘yan Afirka ke yi ba ya rasa nasaba da sassauta iyakar adadin ‘yan kasar waje da za su iya taka leda cikin gasar kwallon kafar kasar wanda aka yi tun shekarar 2015 (dokar ta ba da damar sayan ‘yan wasa 14 ga wace kungiya.

Sannan da yiwuwar saka 11 cikin filin wasa a lokaci daya, da kuma gagarumin karin darajar hakkin mallaka na saka wasa a talabijin.

Darajar ta haura daga kudi Yuro miliyan 362 aa kakar 2012-2017 zuwa Yuro miliyan 555 a kakar 2017-2022.

A kasuwar cinikin ‘yan wasa, kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya ba sa almubazzaranci. Suna taka tsantsan da yawan kudin sayen dan wasa, inda suke fifita nuna irin albashin da za su biya ‘yan wasan.

Wannan na samun goyon bayan tsarin haraji mai taimakawa. Harajin da ‘yan wasa suke biya bai kai na Faransa ba (15% a kan 47%).

Bugu da kari, sabanin yadda yake a Faransa, kungiyoyin kwallon kafar ne ke biyan harajin ‘yan wasan.

“Abin da muke samu a Faransa kudi ne da za a biya haraji a kai, a nan ba a biyan haraji a kai.

Baya ga haka akwai kudaden kyauta da muke jin dadinsu," in ji dan wasan Kamaru Dany Nounkeu.

Samuel Eto'o ma ya taka rawar gani a kungiyoyi biyu na Turkiyya Hoto AA

Ta fagen tsaro, Turkiyya ta taka rawar gani. Ta kaddamar da wani tsari mai tsauri don dakile fada a filayen wasa.

Don cimma wannan, an samar da wani tsari na adana bayanai, ciki har da katunan laturoni mai tattare da bayanai na magoya baya.

"Tsaro a ciki da wajen filayen wasa yana da karfi a kowane lokaci," in ji dan wasan kamaru na da Aurélien Chedjou.

Tururuwar ‘yan Senegal

Moussa Sow da Demba Bâ da Papiss Cissé — jerin sunayen ‘yan Senegal da suka kware a zura kwallo a raga kuma suka taka leda a Türkiye yana da tsawo.

A shekarar 2002 ne suka fara tururuwa, a lokacin da kasar ta yammacin Afirka ta ja hankalin kowa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Japan da Koriya ta Kudu.

Tururuwar ‘yan wasa Senegal zuwa Turkiyya bai tsaya ba tun lokacin.

An fara ne da ‘yan sharar fage irin su Tony Silva ( da ya je Trabzonspor, 2008-2010) da Diomansy Kamara (da ya koma Eskişehirspor, 2011 da 2014) da Mamadou Niang (da ya take leda a Fenerbahçe SK da 2010 da 2011 da kuma Besiktas 2013), suka bi gaban irin su Moussa da Demba da kuma Papiss.

Daya daga cikin uku na karshen ya koma Fenerbahçe SK a shekarar 2012. Ya yi wasa a kungiyar har zuwa shekarar 2015, inda ya zura kwallaye 66 a raga a cikin wasanni 154.

Ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahli (UAE), daga baya ya koma buga wasan aro a Fenerbahçe SK a kakar 2016-2017.

Dan wasan gaban Senegal ya koma buga wasa a Bursaspor (a shekarar 2018) da Gazişehir Gaziantep FK (a shekarar 2019) da kuma Ümraniyespor (a kakar 2020-2021).

Yayin zamansa a Turkiye, Demba ya samu damar zura kwallo 27 a raga cikin wasanni 44/Photo AA

Demba ya isa Besiktas a shekarar 2014 kuma ya buga wasan aro na kaka daya a kungiyar kwallon kafar ta Turkiye, amma ya samu damar zura kwallaye 27 a raga cikin wasanni 44.

Daga baya ya rattaba hannu a kontiragi da Göztepe SK na kaka daya (2018), sannan ya koma İstanbul Başakşehir a shekarar 2019, inda ya zura kwallaye 26 a raga cikin wasanni 83.

Papiss ya samu damar fara taka leda a Türkiye da kungiyar Alanyaspor (2018-2020). Ya buga wasanni 65 kuma ya zura kwallaye 42 a raga.

Sannan ya koma Fenerbahçe SK ( a kakar 2020-2021) kafin ya rattaba hannu a kwantiragi wa Çaykur Rizespor a kakar 2021-2022.

Kafin wadannan manyan ‘yan wasan gaban Senegal din, Issiar Dia ya kasance wani tauraro da ya taka leda a Turkiye.

Ya fara wasan kwallon kafa ne a Nancy (dake Faransa), sannan ya koma Fenerbahçe SK a kakar2010-2011 kuma ya zura kwallo17 a raga cikin wasanni 48.

Jumullar nasarorin wadannan ‘yan wasan ya sa gomman ‘yan wasa suka zabi Turkiye a matsayin inda suka fi son taka leda.

A kakar bana akwai akalla ‘yan wasan gaba 10 daga Senegal da suke taka leda a babbar gasar kwalon kafa ta Türkiye.

Abin jin dadi ne ga magoya bayan kwallon kafa a Turkiye cewar kasarsu ta kasance dandalin wasan gogaggu daga Afirka.

TRT Afrika