Tsawon karni da dama ana yin tattoo a duniya. Hoto: Rueters

Daga Charles Mgbolu

Yin tattoo na daukar ‘yan awanni in da ake amfani da allura mai dan zafi da take dusasa fata a yayin da ake zana abun da ake so.

Ana wannan ta’ada tsawon karni da dama, inda ake bayar da labarai ko zana wasu abubuwa da adon tattoo da ake yi wa mutane.

“Ya zama babban abu ga matasa wajen bayyana ra’ayinsu,” in ji John Nwosu, mai shirya fina-finai kuma mai yin adon tattoo a Lagos, Nijeriya.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa “Matasan Afirka na son zama na daban. A ganina, ina yin tattoo ne don kar na zama wani gama-gari. Ina son zaman a daban.”

Wasu masu yin tattoo sun bayyana nadamarsu bayan an zana musu. Hoto: Rueters

An yi wa John tattoo a bayansa da kuma kafadarsa ta dama, abu ne da yake na musamman kuma mai ban ta’ajibi.

Ya ce ”Tattoo dina babban zanen zuciya ne da yake tsakiyar gobarar daji. Yana nufin wutar Ubangiji a jikina, kuma yana da kusanci da ni sosai. Shi ya sa na yi a inda ni kadai zan ga adon.”

Labarai na musamman

A wajen Marcos Levy, mawaki kuma marubucin waka daga tsibirin Praia na Cabo Verde, tattoo na isar da bayanai ga dan adam sama da magana da baki.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa “tattoo ado ne da ake iya yi a jiki inda muke bayyana kawunanmu tare da sanar da labaranmu na musamman.

"Tunatarwa ce da ba a mantawa da ita kan abubuwan da muke so."

Wasu na yi wa tattoo kallon zanen jiki na musamman. Hoto: Marcus Levy

Masu yin adon tattoo na gwagwarmayar a amince da su a wasu al’ummun.

“A shekarun 1990 da 2000, da wahala a ce a ga wani ma’aikacin ofis ko wata ma’aikata dauke da tattoo a jikinsa, amma yanzu komai ya sauya,” in ji Ashley Philips dag Afirka ta kudu, wadda take aiki a wani banki.

Nadamar yin tattoo

“Ina da tattoo da ya yi kama da sarkar wuya da ke wuyan hannuna. A lokacin da nake yi wa mutane intabiyun aiki, sai dai kawai a kalle shi.

"A wajena, abu ne da nake amfani da shi wajen fada wa kowa cewa ni mai kyau ce,” in ji Ashley a tattaunarta TRT Afirka.

Amma tattoo na iya fuskantar tasgaro inda mai dauke da shi zai zo yana nadama.

“Na kasa nutsuwa har sai bayan da na yi tattoo a kirjina. Ya zama kamar babu wani abu da ya taba faruwa,” in ji Azeez, wani dan Nijeriya mai gyaran gashi.

Ya ci gaba da cewa “Bayan na yi tattoo din, sai kuma na dawo ina nadamar yin sa. Sai na kalli tattoo din na kuma tambayi kaina mene ne wannan?”

Matasan Afirka na kara yin tattoo sosai. Hoto: Rueters

John Nwosu ya fahimci wannan abu: ya fada wa TRT Afirka cewa “Abu ne da ba za ka iya hasashe ba game da matasa”.

“Mutane da dama na yin tattoo saboda sun ga abokansu sun yi, ko suna ganin ana yayin sa, ko suna son su burge wasu. Amma idan ba ka zama mai alaka sosai da sakon da tattoo din ka ke dauke da shi ba, za ka kare a matsayin mai nadamar yin sa.”

Onoyungbo Taiwo, mai horar da masu motsa jiki ne kuma yake da tattoo da yawa. Ya bayyana cewa dole ne tattoo ya zama yana da ma’ana.

Ya fada wa TRT Afirka cewa “Ina son zane-zane, kuma dukkan tattoo din da ke jikina sun shafi rayuwar ‘yata.”

Duk da irin abun da ke biyo bayan yin tattoo, wasu matasa na ganin ya dace su yi.

“Dauki tawadar, fatarmu ta zama abun da muke raji," in ji mawaki Marcus na kasar Cabo Verde.

TRT Afrika