Daga Charles Mgbolu
Makwanni uku kenan da shiga sabuwar shekara, amma tauraron mawakin dan Nijeriya Davido ya taka rawar gani, inda ya bude wannan shekara da wani babban taron waka a babban filin wasa na O2 Arena mai daukar mutum 20,000 da ke Landan, wanda masu shirya taron suka ce tuni an riga an gama sayar da tikitin shiga kallo.
Wannan shi ne karo na uku da dan wasan mai shekara 31 ke yin nasarar irin wannan gagarumin taro, inda a baya ya yi nasarar gudanar da manyan tarukan waka a shekarar 2019 da 2022.
O2 Arena yana cikin manyan wuraren gudanar da shirye-shiryen nishaɗi a duniya.
A da, mawaka masu fasaha na Yammacin Duniya ne kawai ke da babbar dama a duniya, irin su Beyonce da Taylor Swift da Ed Sheeran da Drake, da sauransu, na iya tara taron jama'a masu iya cika wurin cikin gida.
Amma masu fasahar Afrobeats kamar Davido, Wizkid, da Burna Boy a yanzu sun samu irin wannan tagomashin.
Wajen taro na O2 Arena yana da tsada sosai, inda mawaƙa suke biyan kuɗin da ya kai dala 600,000 don yin hayar wurin a rana guda kawai.
Za a yi taron ne mai taken ''’Timeless Tour'' a ranar 28 ga Janairun 2024.
An shirya gudanar da ziyarar zagayen a birane daban-daban na duniya, ciki har da Paris da Laval (Kanada) da New York da kuma Florida.
Bayan taronsa na O2 Arena, ana sa ran Davido zai dan dakata na dan lokaci, yayin da aka zabe shi a cikin kyaututtukan Grammy na 2024 da wakokinsa ''Unavailable'', da 'Feel', da kuma 'Timeless'.
An zabi shi ne tare da 'yan Nijeriya Burna Boy da Asake da Olamide, da Ayra Starr.