Daga Pauline Odhiambo
Kullum cikin tufafi masu kyau da suke dauke da kwalliya masu yawa a jiki yake. Wannan ne tsarin fitaccen telan nan mai suna Allen 'The Dapper' Igatanyi.
Kayayyakin ado da yake hadawa ne suka daga darajarsa a Kenya, inda fitattun mawakan kasar irin su Mejja fa Otti Brown da da mawakan gengetone suke amfani da kayayyakin kamfaninsa mai suna FALA Wear.
Amma mutane da dama ba su san cewa kamfanin nasa - wanda Fashionable African Latest Attire aka takaita zuwa FALA- ya samo asali ne daga gyara rigar mahaifiyarsa ba, inda ya mayar da rigar ta zama wata abar sha'awa.
"Wani shudin bujen dogon wando ne, sai na yanke ya koma gajere," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika, sannan ya kara da cewa, "Sai kuma na yanke hannun kwat din, sannan na kara kalolin Afrika a jiki ta bayan rigar."
'Wawan' Dan gayen
Wannan tufafin marigayiyar mahaifiyarsa din da ya gyara ce ta bude masa kofa har ya kai ga assasa kamfaninsa, duk da farko dariya ake masa, ana masa kallon wawa.
Sai suke kiransa da Fala, wanda a Ingilishi yake nufin 'fool' wato wawa.
"Ina yawan sanya kayayyakin da suke nuna ni dan Afirka ne saboda yanayin kalolin da suke jiki. Idan mutane suka ganni, sai su rika cewa cheki yule fala wato kalla wancan wawan," inji Allen mai shekara 29 cikin murmushi.
"Hakan ya sa na fara tunanin yaya zan mayar da sunan da suke kirana ya zama amfani ta hanyar sanya wa kamfanina sunan? Hakan ya sa na assasa kamfanin Fala Wear a shekarar 2015."
Sunan The dapper ma da ake kiransa na da asalin mai kyau
"Wannan sunan daga fastonmu ya samo asali. Idan yana wa'azi, sai ya nuna ni ya ce, 'Allah Yana son mutane masu tsabta (dapper) kamar wannan yaron.' Sai na yi tunanin Allen 'the dapper' zai yi dadin fada, sai na fara kiran kaina da sunan, har ya samu karbuwa a wajen mutane."
Ya taba shiga makarantar koyon dinkin nan fitacciya ta Buruburu Institute of Fine Arts (BIFA) da ke Nairobi, amma ya fita domin ya samu mayar da hankalinsa waken aikinsa.
"Na karu da makarantar BIFA, amma ko mako daya ban yi ba saboda ban ga amfanin zama a aji ina sauraron karatu a kan yadda zan yi dinki ba, alhali zan fi kwarewa ne idan ina yi a aikace."
Kullum cikin shiri
Farkon taron kwalliyar da ya halarta ya kasance na daukar bidiyo ne, wanda a cewar Allen ya kara daga masa daraja sama da kudin da ya samu.
"A wajen daukar wannan bidiyon, ni ne ya yi wa dukkan wadanda suke wajen kwalliya. Na sha wahala saboda ni kadai ne mai kwalliya a wajen, duk da cewa akwai takaici a ce ka yi wa dukkan wadanda suke wajen kwalliya ba tare an biya ko kwabo ba."
Sai dai wannan damar ce ta sa aka fara gayyatarsa tarukan manya, wanda hakan ya taimaka masa wajen daga martabar kamfaninsa.
Babbar damarsa ta zo ne a lokacin da ya yi wa Jimmy Gait, wanda fitaccen mawakin yabon Kirista ne kwalliya domin daukar bidiyonsa.
"Sai bidiyon wakar ya samu karbuwa, inda cikin kankanin lokaci ya shahara, wanda wannan ne ya daukaka ni saboda na kasance cikin wadanda suka yi aikin wakar, wadda da ta karade gari," in ji Allen.
"Daga wannan lokacin ne sai wasu fitattun taurarin suka fara bukatar aikina. Har mutanen gari ma sai suka fara nemana suna so su yi aiki da ni, ko su saya kayana. Wannan ne mafarin daukakar da na samu har ta kai muna hadaka da wasu kamfanoni kayayyakin adon."
Zama fitacce
Yi wa fitattun taurarin kwalliyar da za a iya kafa musu kyamara a kowane lokaci, da kuma yin aikin wasu finafinai ne suka sa Allen ya gano wata baiwarsu, wato ta fim.
Zama jarumi ya zo masa da sauki saboda yanayinsa mai son kwalliya da kuma kasancewarsa fitacce, wanda hakan ya sa ya samu shiga cikin wani shiri mai dogon zango da ake haskawa a Afirka ta Kudu.
Kara samun karbuwar da yake yi ya sa dole ya kara inganta ayyukansa da kara fadada basirarsa saboda aikin da yake yi wa mutane da yawa.
"Yana da kyau mutum ya rika tunani sosai, sannan kuma ya rika rufe ido wajen gwada sababbin abubuwa," in ji shi.
"Aikin kwalliya ya bude min damarmaki da dama. Na fahimci cewa duk da cewa kwastoma kamar sarki yake, amma yana da kyau ya kasance ka yarda da kanka da kuma aikinka, domin kada ka ba da kanka da yawa."
Allen ya kara da cewa yanayin rayuwarsa ya taimaka masa wajen fadada basirarsa.
"Burina shi ne na samar da kayan da za su rika sanya farin ciki a zukatan mutanen da suke cikin bakin ciki: irin kwalliyar da mutum zai yi, ya rika jin kan shi," in ji shi.
"Sannan ina da burin ganin kowa ya mallaki kayayyakina. Wadannan abubuwan ne suke kara karfafa min gwiwa."