An haifi Adekunle Gold da cutar Sikila. Hoto: Adekunle Gold  

Daga Charles Mgbolu

Tauraron mawaƙin Nijeriya Adekunle Gold ya tsaya a gaban dubban masoyansa a wani babban dakin taro da ke birnin Birmingham na kasar Birtaniya, inda ya dakatar da makaɗa da masu masa amshi don bayyana wani saƙo mai matuƙar ƙrfafa gwiwa.

Mawakin mai shekaru 37 da ya rera wakar ''Party no dey stop'' crooner, wanda a halin yanzu yake rangadi a Turai yana tallata kundin waƙoƙinsa, ya ce yana son ya zama wata fitila mai haske don karfafawa masu fama da cutar sikila.

''Ga wadanda suka tsira daga cutar sikila, sun zama mayaka a halin da suka tsinci kansu ciki. Ina so na karfafa muku gwiwa kan cewa za ku iya. Idan har zan iya to kuma za ku iya, '' a cewarsa yayin da masu sauraronsa sun ka yi ta masa shewa a ranar 24 ga watan Febrairun nan.

A watan Yulin 2022 ne Adekunle ya fara bayyana gwagwarmayar sa kasancewarsa wanda ke dauke da cutar sikila.

Ana gadon cutar ce ta hanyar jini sakamakon karancin iskar Oxygen da toshewar hanyoyin jini, wanda hakan kan haifar da matsanancin ciwon jiki da kuma wasu cututtuka masu tsanani a cewar WHO.

A shekarar 2022 Adekunle Gold ya sanar da masoyansa labarin cutar da yake dauke da ita.

Kimanin yara 1,000 ne ake haifa masu dauke da cutar a kowace rana a Afirka, lamarin da ya sa cutar ta fi ƙamari a yankin.

Fiye da rabin yara masu fama da cutar na mutuwa kafin su kai shekaru biyar, in ji WHO.

A wani wasikar sako da aka rabawa masoyansa a watan Yuli 2022, Adekunle ya bayyana karara irin tsananin azabar cikin dare da kuma yadda a wasu lokutan yake yi wa kansa mutuwa.

"Daya daga cikin mafi munin azabar da na fuskanta sakamakon cutar shi ne a lokacin da nake shekara 20. Na tuna ina kwance da tsaka dare, ina neman a kawo min karshen lamarin. Na roki Allah ya karbi raina," in ji shi.

“Abin farin ciki ne a ƙarshe da na samu damar bayyana wannan ɓangare na rayuwata tare da ku, daga ƙarshe na samu damar faɗan gaskiyata a lokacin da nake bayyana yadda na yi gwagwarmaya don kaiwa ga inda nake a yau, ina bukatar ku sani cewa gwagwarmayata ta kasance da gaske."

Waƙar ƙarfafa gwiwa

Rayuwa da cutar sikila shi ne jigon da karfafawa fitaccen mawakin gwiwa wajen rera wakokin albam dinsa mai suna 'Five star' wanda a ciki ya ƙarfafa masoyansa gwiwa kan su ci gaba da ƙoƙari kuma kada su ba da dama yanayi ya tantance musu abin da ya kamata su za zama a ƙarshe.

Adekunle Gold, wanda ya lashe lambar yabo a matsayin wanda ya yi fice a kyautar Nishadi ta Nijeriya a shekarar 2015, ba shi kadai ba ne yake bayyana sakonni masu karfafa gwiwa kamar wadannan ba, wasu masu nishadantarwa ma sun soma fito wa fili wajen bude wa duniya irin kalubalen rayuwa da suka yi fama da shi a rayuwa da kuma hanyar da suka bi wajen shawo kansu wadanda masoya ke yabawa a matsayin karfafawa.

Wasu mawakan Nijeriya biyu, Augustine Miles Kelechi (Tekno), Olamide Adedeji, da tauraron mawakan Tanzaniya, Diamond Platnumz, duk misalai ne; inda suka fito fili suka bayyana wa duniya kalubalen da suka yi fuskanta a lokacin da suka yi fama da matsalar da ta shafi lafiyar kwakwalwarsu.

A shafukan sada zumunta, masoya sun yaba wa Adekunle bisa ga jarumtakarsa wajen bude wa duniya halin da ya fada ciki da kuma yadda ya ci gaba da kasancewa mai karfin gwiwa.

‘’Allah ya saka da alheri, Adekunle Gold. Mu yi amfani da damar da muka tsinci kanmu a ciki. Idan kuna tunanin abin da rayuwa ta jefa ciki shine karshe ko mafi muni, toh tabba kuna kuskuren tunani. Kowa ya zo duniyar nan da kaya,'' in ji @retireesnigeria a shafin YouTube.

Wani masoyi mai suna @omololaesho1210 shi ma ya rubuta a kafar Youtube cewa: ''Labari mai matukar sosa rai.... Ina ma ɗana zai gana da Adekunle ya karfafa masa gwiwa .... ƙauna mai yawa''

Darasi ga mutane da dama

Wasu magoya bayan sun bukaci sauran fitattatun mutane su kara himma wajen taimaka wa masoyansu su san cewa akwai sauran rayuwa a bayan duk wani kyale-kyale da kawa kuma su yarda da cewa ba abun gyama ba ne mutun ya kasance cikin yanayi rauni.

Adekunle Gold ya bayyana cewa yana son ya zama fitilar da ke haskaka hanya. Hoto: Adekunle Gold

''Muna samun karfin gwiwa daga ire-iren waɗannan sakon, suna taimaka mana wajen sanin cewa ba mu kadai ba ne muke fuskantar kalubalen rayuwa, wannan shine abin da ya kamata fitattatun mutane da suka shahara suna yi… su zama jakadun bege '' a cewar sakon da @realakan ya rubuta a shafin Youtube.

Adekunle ya ce zai ci gaba da taimaka wa mutane musamman masu fama da cutar sikila, domin samun karfin gwiwa daga labarinsa, kada su karaya.

''Don haka wannan sako na zuwa ne ga duk wanda ke fama da radadi ko azabar cutar sikila ta [sickle cell]. za ka iya. Bai kamata ya hana ka ba. Kalle ni; Ni fitaccen tauraro ne a yanzu,'' in ji shi a wurin taron shagalinsa na London.

Adekunle Gold zai ci gaba da rangadinsa a Birtaniya inda wuri na gaba da zai ziyarta shi ne Wembley a ranar 3 ga Maris yayin da mawakin Afrobeats din ke ci gaba da nishadantarwa tare da karfafa mutane da dama gwiwa.

TRT Afrika