Daga Abdulwasiu Hassan
Fargabar abin da ka iya faruwa na iya zama mai ƙarfi kamar fuskantar wannan lamari mai sanya tsoro da firgici.
Zahara Dattani, 'yar kasar Tanzaniya da take da wani gidan kula da tsofaffi a Birtaniya, tana cikin irin wannan mummunar fargabar a duk lokacin da ta ji labarin cewa an kai wa wani baƙon haure hari a tarzomar da ke faruwa a kasar.
Ba tsoron lafiyarta kawai take yi ba har ma da na yawancin ma'aikatan kiwon lafiya 'yan cirani da suke aiki a ƙarƙashinta.
"Ina ganin tarin tasirin da muke ji shi ne na tsoron duk wani abu marar kyau da ka iya faruwa," Dattani ta shaida wa TRT Afrika.
"Ko da yake ni da ma'aikatana ba mu gamu da masu tayar da tarzomar ba, ganin abin da ke faruwa a fadin kasar nan tamkar jiran faruwar wani abu mara kyau ne."
Rikicin da aka shirya ɗin ya faro ne tun mako guda da ya gabata, bayan da ga dukkan alamu kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke fafutukar ƙyamar baki suka fara shi sakamakon wani labari da aka samu game da ainihin wanda ya kashe wasu 'yan mata uku har lahira a yankin Southport da ke arewacin Ingila a ranar 29 ga watan Yuli.
Tuni dai aka ci gaba da tashe-tashen hankula a biranen kasar ta Ingila, inda ake ci gaba da kai hare-hare kan baƙin haure 'yan Afirka da Asiya duk kuwa da cewa hukumomin kasar sun yi gargadin cewa za a hukunta wadanda suka aikata ta'addancin wariyar launin fata.
A wasu wurare kamar Belfast a Arewacin Ireland, masu tarzoma da ke da tsattsauran ra'ayi suna rera taken ƙyamar addinin Musulunci, sannan kuma an kai hari kan kasuwannin yankin.
Ƙasar da ƴan Afirka da yawa ke ƙaura zuwa can a yanzu kwatsam zama a cikinta ya zama haɗari a gare su. Dama can ba wai komai yana tafiya daidai ba ne, sai dai wannan rikicin ya nuna matsalar da ake ciki.
'Yan Afirka da 'yan Asiya sun sha fama da zarge-zarge daga masu ƙin jinin baƙin-haure a Birtaniya na cewa sun ƙace ayyukan 'yan ƙasar.
Matakan kariya
Ganin zahirin halin da ake ciki, gwamnatin ta yi alkawarin ƙarfafa tsaro don gamsar da mafi yawan 'yan Afirka da ke zaune suna aiki a Birtaniya cewa ba da daɗewa ba komai zai wuce.
Tun ranar 5 ga watan Agusta, masu biren suka yi fito-na-fito da 'yan sanda a lokuta da dama a Belfast da Darlington da kuma Plymouth.
"A haka za a ga kamar akwai tsaro a Birtaniya saboda kasancewar 'yan sanda a kowane lungu da saƙo, amma fa abubuwa sun damalmale a yanzu haka," in ji Dattani.
Ta sanya ma'aikatanta sun bi wasu matakan kariya, inda ta fahimtar da su cewa suna cikin haɗari, da kuma yadda za su magance abin da ke faruwa a kewayensu.
"Mun kimsa musu cewa kar su fita su kaɗai da daddare, musamman bayan tashi daga aiki, kuma a ko yaushe su kasance ɗauke da katunan shaidarsu. Wasu daga cikin ma'aikatanmu aikin dare suke yi, kuma dole su kula da tsaron kansu," Dattani ta ce.
Wani ɗan Nijeriya da ke koyarwa a jami'a a Birtaniya, Dr Ishaka Shittu Almustapha ya ce a yanzu zaɓi ɗaya ya rage wa baƙin haure shi ne su bi a sannu su kuma jira hankula su kwanta.
"Muna duk abin da za mu iya don sanya mutane taƙaita zirga-zirgarsu. Limamai na ta aika saƙo — cewa mutane su yi taka tsantsan, su kuma guji zuwa masallaci da yara da mata a yanzu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Shi kuma wani ɗan Nijeriyar mazaunin London, Dr Shamsuddeen Hassan Muhammad ya ce a yanzu dai yana cikin tsaro a birnin mafi girma na Birtaniya, amma fa ba zai saki jiki ba.
"Yawanci muna cikin gida a rufe tun bayan fara boren, kuma da yake hutu ake yi yanzu yara ba sa zuwa makaranta. Mun taƙaita fita sai wadda ta zama dole, kamar zuwa sallah. Hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron iyalanmu a wannan yanayi na rashin tabbas," ya ce.
Gargaɗi ga masu tafiye-tafiye
Nijeriya, wadda tana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke da yawan 'yan cirani a Birtaniya, ta fitar da gargaɗi ga 'yan ƙasarta masu shirin zuwa can a yayin da rikicin yake sake bazuwa zuwa wasu sabbin yankunan, bayan boren farko da aka fara a arewacin Ingila.
Sanarwar da kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Eche Abu-Obu ya sanya wa hannu, ta ce "Tashin hankalin ya dauki salo mai hadari, kamar yadda rahotanni suka nuna kan harin da aka kai kan jami'an tsaro da lalata kayayyakin more rayuwa."
An shawarci ‘yan Nijeriya da su guji gudanar da jerin gwano na siyasa da zanga-zanga da gangami ko maci da kuma shiga wuraren da jama’a ke taruwa.
Tuni dai ofishin jakadancin Nijeriya a Birtaniya ta sake fitar da wata sanarwa, inda ta ba da tabbacin cewa za a sanar da su a hukumance abubuwan da ke faruwa.
Shi ma ofishin jakadancin Kenya, ya fitar da wata sanarwa inda ya bukaci daukacin al'ummar yankin gabashin Afirka da ke zaune a Birtaniya da Ireland ta Arewa da su yi taka tsantsan tare da yin rajistar kansu a shafukan ofisoshin diflomasiyya na ƙasashensu.
A yayin da tarzomar ta bazu a fadin Birtaniya, wasu mutane da ƙungiyoyi sun yi zanga-zangar ƙyamar masu tsattsauran ra'ayi inda suka sha alwashin tinkarar masu zanga-zangar 'yan ra'ayin mazan jiya.