Yadda nasarar 'yan Nijeriya da ke kasashen waje ke taimaka wa kasar ta habaka

Yadda nasarar 'yan Nijeriya da ke kasashen waje ke taimaka wa kasar ta habaka

Gida nan wajen da zukatan 'yan Nijeriya suke a yayin da suke taka muhimmiyar rawa wajen habaka arzikin kasarsu.
A yanzu 'yan Nijeriya na rike da manyan mukamai a Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Kasuwanci ta Duniya da Bankin Cigaban Afirka.

Daga Abdulwasiu Hassan

Me Bukayo Saka ya yi a lokacin da ya ƙi wulakanta damar da ya samu a Emirate? Ya hada kai da kungiyoyin tallafi wajen daukar nauyin tiyata ga yara kanana a Nijeriya, kasar da daga nan ne iyayensa suka yi kaura zuwa Landan.

Ko ka dauki misalin Jay-Jay Okocha, shahararren dan wasan kwallon kafa na Nijeriya wanda ya sanya ƙwallo take saurarensa, a lokacin da abokin wasansa a PSG Ronaldinho yake kwafsawa.

A gida, Okocha ya yi amfani a matsayinsa na kwallo wajen wayar da kan jama'a kan muhimmancin ilimi.

Mutumin Legas Victor Osimhen, wanda a yanzu ya zama mafi shawarar dan wasan gaba na kungiyar Super Eagles da kuma Napoli, ya dauki mataki mai kyau: yana son taimakawa nakasassu a Afirka.

"Idan ba ka da kafa, za mu samar maka da wata. Idan kuma damtse ne ka rasa, shi ma za mu kera maka wani," in ji shi a wajen wani taro da aka gudanar a watan Maris a Nijeriya.

Ƙaruwar fita waje

A baya-bayan nan, Nijeriya na shaida yadda ake hijira daga kasar zuwa kasashen waje, kwararru da ke samun kudadensu daidia gwargwado a kasar ne ke kan gaba wajen guduwa "Japa", wanda ke nufin kaura zuwa wata kasa, abu ne da ya ta'azzara a shekarar da ta gabata.

Kwararru sun bayyana 'yan Nijeriya da ke kasashen waje na taka rawa sosai wajen cigaban kasar. Hoto/Getty Images

Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo, a yayin da yake bayar da Alkaluman Ilimi Mai Zurfi ya ce daliban Nijeriya 99,985 sun tafi zuwa Ingila a shekaru biyar da suka gabata.

Kasar da ta fi kowa yawan jama'a a Afirka na ci gaba da fuskantar kalubalen cigaba, 'yan kasar da ke da arziki a kasashen waje na iya ba ta taimakon da take so.

Yin tasiri

Daga Ngozi Okonjo-Iweala, darakta janar ta Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), zuwa Amina J. Mohammed, mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Sannan daga mataimakin ministan baitulmalin Amurka, Wally Adeyemo, zuwa shugaban Bankin Cigaban Afirka Akinwumi Adesina, 'yan Nijeriya da ke kasashen waje na yi tasiri a duniya.

Kuma nasararsu na tallafawa kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka.

Kudaden da 'yan Nijeriya da ke kasashen waje ke aikawa gida, shi ne mafi yawa a kasashen Afirka da ya kai ala biliyan 21.9 a 2022, kamar yadda Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.

Wannan babban adadi ne, duba da yadda ya kai rabin kasafin kudin na shekarar da ya kama dala biliyan 39.9.

Dadin zama a waje

Masu nazari na bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ke sanya 'yan Nijeriya samun nasara a kasashen waje shi ne suna daga cikin mafiya kaifin basira da kasar ke samarwa.

"Wadannan masu hijirar da ma can kwararru ne ko kuma suna da kaifin basira a kasashensu."

Kamal Tasi'u Abdullahi, dalibin digirgir a fannin tsimi a tanadi a Jami'ar Istanbul, na jin karsashi wajen yin aikinsa a kasar waje.

Masu nazari sun yi amanna kan cewa Nijeriya na bukatar kara zage damtse don jan hakalin 'yan kasar su dawo gida don cigaban kasar. Hoto/Getty Images

Ya ce "Kasancewa na girma a Nijeriya, da yawa daga cikin mu sun taba fuskantar wani kalubale da matsalolin kasarmu suka haifar sakamakon rashin kayan more rayuwa da kuma gaza samarwa da jama'a abun da suke so.

Wannan ne ya sanya mu samun kuzari da juriya. Hakan ya sanya babu wahala mu saba da duk yanayin da muka samu kawunanmu a ciki, kuma mu habaka tare da tunkarar duk wani kalubale."

'Yan matsalolin da ka iya taso wa

Wasu masu nazari na bayyana cewa har yanzu Nijeriya ba ta kammala amfana da albarkar 'yan kasar da ke kasashen waje ba, kuma ta dakatar da kwarar da suke yi wajen fice wa.

"Ina tunani gwamnati na kokari kan wannan batu. Kowacce kasa da ta san ciwon kan ta ta san cewa 'ya'yanta da ke kasashen waje kadara ce," in ji Dr. Wudil.

Ya kara da cewa Nijeriya za ta iya amfana da kwarewa da ilimin 'ya'yanta da ke kasashen waje, musamman a bangaren ilimi da masana'antu.

Dr. Ishaka Shitu Al-Mustapha, dan Nijeriya da ke Ingila ya shaida wa TRT Afirka cewa Nijeriya na bukatar ta kyautata tare da gyara hanyar aiko da kudade da 'yan kasar ke yi daga kasashen waje ta yadda hakan zai zaburar da su wajen aiko da kudaden zuwa gida.

Hakan yana habaka tattalin arzikinsu tare da samar da zuba jari daga bangarori daban-daban.

Abdullahi na jin cewa Legas na iya karfafawa masu dawo wa su kafa sana'o'i ta hanyar amfana da rangwamen haraji, kyautata hanyoyin samun kudade da rage wahalhalun da dokoki suke janyo wa.

Ya ce "Gwamnati za ta iya bayar da bashin 'yan kasar waje, wanda zai tabo kishin da kwararrun suke da shi, sannan ya taimaka musu wajen samun kudade don yin ayyukan cigaban kasa, da suka shafin hanyoyi, lantarki da yanar gizo."

Wannan zai kuma dawo da amincewar 'yan kasashen waje ga gwamnati tare da jan hankalin 'yan Nijeriya su dawo gida.

Kokarin kungiyoyi

'Yan Nijeriya da ke aiki a kasashen waje da daman su na bayar da gudunmowa sosai wajen taimaka wa 'yan kasar da ke gida, daya-daya ko a kungiyance.

Daya daga cikin wadannan kungiyoyi ita ce Arewa Youth Mentorship, wadda ke da manufar cike gibin samun bayanan irin dimbin damarmaki da ake da su a kasashen waje na ayyuka da guraben tallafin karatu, wuraren samun litattafai na yanar gizo da binciken ilimi.

Dadin dadawa, suna da kwazo sosai," in ji Dr Yakubu Musa Wudil yayin tattauna wa da TRT Afirka.

Ana sa ran nasarar 'yan Nijeriya z ata ninku da taimaka wa kasar. Hoto/Getty Images

Shirin na amfani da dandalin yanar gizo don sanar da dalibai da da wadanda suka kammala karatu irin damarmakin da ake da su a kasashen waje don su ma su amfana.

Dr. Wudil ya kara da cewa "A yanzu muna da sama da matasa 100 da suka samu tallafin karatu dari bisa dari ko kasa da haka a kasashe daban-daban da suka hada da Amurka, Saudiyya da China,"

A yayin da John Utaka, tsohon dan kwallon Super Eagle kuma mai horar da kungiyar Montpellier a yanzu haka, yake kaddamar da asusunsa da ke samar da tallafin karatu ga matasa kwararru a kwallon kafa.

Ya ce "Na yi amanna cewa saka wa kasarka ko jama'arka na da muhimmanci saboda ni ma a cikin tsarin na ke a baya."

TRT Afrika