Kamfanin Shell ya kasance a Nijeriya tun kafin kasar ta samu 'yancin kai daga Biritaniya: Hoto/Reuters  

An iya cewa tarihin zamanin hako mai a Nijeriya ya zo karshe, bayan da kamfanin Shell mai hedkwata a birnin Landan ya yi shelar siyar da kaddarorinsa na gabar tekun yammacin Afirka bayan shafe shekaru 68 yana aiki a can.

Kamfanin na kasar Birtaniyan wanda ya fara fitar da man fetur daga yankin Niger Delta a lokacin da Nijeriya ke karkashin mulkin mallaka a shekarar 1956, ya fitar da sanarwar ne a ranar 16 ga watan Janairu kan cewa zai sayar da kadarorinsa a yankin kan dalar Amurka biliyan 1.3

Gamayyar kamfanonin Nijeriya da za su siya wadannan kadarorin na Shell za su biya karin dala biliyan 1.1 a kan kudaden da yake samu a baya da kuma sauran kudaden da suka shafi ayyukan babban kamfanin a Nijeriya.

Kaddarorin da cinikin ya shafa sun hada da yarjejeniyar hako mai guda 18, wadanda jumillar aijiyarsu ya kai ganga miliyan 458.

Idan aka ninka adadin ganga da farashin danyen mai a halin yanzu, ribar da za a samu zai fi farashin da Shell zai sayar da kadarorinsa.

Shari’o’i da dama

Ko me zai sa Shell ya siyar da wadannan kadarori masu daraja a farashin nan da ake gani?

Mambobin al'umma sun koka kan katafaren kamfanin man:  Hoto/Reuters

Katafaren kamfanin man na Birtaniya, wanda ke matsayin na biyu bayan kamfanin benemoth ExxonMobil na Amurka a masana'antar mai da iskar gasa a duniya, ya fuskanci tarin kararraki da shari'o'i a tsawon shekaru.

Yawancin wadannan shari’o’in sun hada da illar da ake zargin kamfanin Shell ke haifarwa a yankin Niger-Delta, wajen lalata rayuwar al’umma da kuma gurbatar da muhallin yankin.

Mambobin al’ummomin yankin mai arzikin hako man suna ganin ba su samun kaso mai tsoka na arzikin da Shell ke samu a kasarsu.

Wasu shari’o’in sun sa kamfanin ya biya al’ummar yankin Niger-Delta miliyoyin daloli a matsayin diyya.

A wani misali, an taba tilastawa kamfanin Shell Petroleum Development Company of Nigeria Ltd ya amince ya biya dala miliyan 15.9 ga al’ummomi da kuma mutanen yankin Niger-Delta bayan shafe tsawon lokaci da aka yi ana shari’a a shekarar 2008.

Kazalika wasu manoma hudu a Nijeriya sun taba maka Shell a kotu bisa zargin gurbata musu amfanin gonakinsu da ya samo asali daga bututun kamfanin tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007.

Kotun daukaka kara ta Hague ta yanke hukuncin a shekarar 2021, bayan da ta samu Shell da laifin gurbatar bututun mai guda hudu a yankin Niger Delta.

Daukar Nauyi a hukumance

Gwamnatin Nijeriya, wadda kamfanin Shell ke bukatar amincewarta don ayyukansa cikininsa su tafi daidai, ta yi watsi da yarjejeniyar cinikin, a cewar karamin ministan albarkatun man fetur na kasar, Heineken Lokpobiri.

Bayan da sanarwar ta fito fili, jama’a suka fara ce-ce-ku-ce kan me hakan ke nufi ga Nijeriya.

Wasu na ganin barin Shell Nijeriya, kamar yadda wasu manyan kamfanonin duniya suka bar kasar, zai iya janyo koma baya tare da bata sunan kasar.

Shune da kuma matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ka'ida ba suna  haifar da fashewar mai: Hoto/Reuters

Masana da masu ruwa da tsaki na ganin matakin da Shell ya dauka na siyar da kadarorinsa da ke gabar teku, nasara ce a gareshi da kuma sauran 'yan kasuwa a masana’antar mai da iskar gas a Nijeriya.

"Gaskiyar al'amarin ita ce, IOCs (kamfanonin mai na kasashen duniya) sun fi son hako mai ta teku (wanda ke cikin teku kusa da gabar teku) zuwa bakin teku saboda karancin kalubale," kamar yadda Muhammad Saleh Hassan, shugaban kamfanin Skymark Energy and Power Ltd, ya shaida wa TRT Afrika.

"Ayyuka kan kasa sun fi zama asara ga katafaren kamfanin man fiye da riba, amma har yanzu kamfanin yana aiki a Nijeriya, Kawai dai zai mayar da ayyukansa cikin teku ne, kamar yadda ya ambato a baya." in ji shi.

Ko da yake, Hassan ya ce ba shi kadai bane yake ganin matakin Shell a matsayin wata dama ba, a maimakon koma baya ga bangaren mai da iskar gas a kasar.

Kamfanin Shell zai sayar da hannnayen jarinsa na tekun ga kamfanonin  hada-hada a Nijeriya ;Hoto/ REUTERS

"Hakan zai bude kofa ga masu zuba jari da ke da burin saka kudadensu a kamfanonin masu tasowa na mai da iskar gas a Nijeriya, musamman kamfanoni irin su Eroton da Seplat da wasu 'yan kalilan da ke da mutanen da suka koyi sana'arsu a kamfanonin mai na kasashen duniya IOC da suke son maye gurbinsu."

Minista Lokpobiri ya goyi bayan wadannan kyakkyawan fata, yana mai cewa janyewar kamfanonin mai na kasashen duniya (IOCs) daga ayyukan da suke yi a kan teku zai kara samar da riba da kuma kara daidaita tattalin arziki.

TRT Afrika