Daga Abdulwasiu Hassan
Fada wa mutum "Ko kun san" ba tare da niyyar bata mas arai ba, na iya zama mafarar tafiyar neman ilimin da zai kawar da tsohuwar fahimtar da aka dade a kai.
Kamar sanin cewa jakar hannun ku mai tsada kirar Italiya na da jinin Nijeriya sama da na Italiya a cikin ta.
Ko kuma, a fada maka cewa manyan kamfanonin fata na Italiya da Spaniya na sayen wani bangare na fatun da suke sarrafa wa daga arewacin Nijeriya.
Fatun Nijeriya, musamman fatar jar akuyar Sokoto, ta yi shuhura a duniya saboda tsabagen ingancin ta.
Samar da ayyuka, kudaden kasashen waje
Duk da cewa Nijeriya ba ta da kamfanonin jimar fata da yawa kamar a shekarun baya, fata na ci gaba da zama daya daga hajojin da ke samar da ayyukan yi da kudaden kasashen waje a kasar mafi yawan jama'a a Afirka.
Hukumar Kididdiga ta bayyana cewa kusan gidaje miliyan 16.6 na kiwata awaki da tumaki miliyan 124 a kowacce shekara, wanda hakan ke nufin samun fatu da kiraga ga masana'atun sarfafa fata.
Kamfanonin jeme fata a arewacin Nijeriya, musamman ma birnin Kano na kasuwanci, sun dogara kan makiyaya kanana da ke kawo musu fatun da suke sarrafa wa domin fita da su kasashen waje da amfanin cikin gida.
"Masana'antar sarrafa fata na bayar da gudunmowa sosai ga habakar tattalin arziki da fadada hanyoyin samun kudade," in ji Dr Jerry Tagang, malami a Cibiyar Nazarin Kimiyya da Fasahar Sarrafa Fata ta Nijeriya da ke Zaria, yayin da yake tattauna wa da TRT Afrika.
Ana fitar da kaso 90 na fatun Nijeriya zuwa kasashen ketare
"Kayan amfanin da ake da su a kasar, kwararrun masu aiki, da gwamnati mai bayar da tallafi (irin Manufar Fatar Kasa da Kayan Fatu) na samar da yanayi mai kyau wajen habakar wannan fanni."
A yayin da alkaluma daga Hukumar Habaka Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya ke bayyana cewa kashi 90 n akayan fatu da ake samarwa a Nijeriya na tafiya kasashen waje, Dr Tagang ya ce bukatar cikin gida kawai za ta iya kula da rayuwar dununnan 'yan Nijeriya.
"Fatun Nijeriya da masana'antun sarrafa su a Nijeriya a yau na samar da ayyukan yi ga mutane 750,000, inda kimanin 500,000 daga cikin su na mu'amala da fatun da aka gama jeme su," in ji Dr Tagang.
"Masana'antar za ta iya samar da karin ayyuka ga 'yan Nijeriya matasa da mata, matukar dai an yi aiki yadda ya kamata a fannin samarwa da sarrafa fatun.
Gogayya a kasuwannin duniya
Da yawa daga wadannan kamfanoni na cikin gida na yi wa Winston Leather aiki ne, wand aya fadada yawan kayan fata da yake samarwa daga wada yake fita da su,
A wani bidiyo da aka yada a shafin Tiktok din kamfanin, shugaban kamfanin Winston Udeagha ya ce kayansu iri daya ne da na manyan kasashen Turai, kuma nasu sun fi arha da sauki.
"Mu ma wani bangare ne na 'kayan da aka samar a Afrika' wanda suke iya gogayya da sauran kasashen duniya," ya fada wa TRT Afrika.
"To idan ka ga jakar da aka samar a Nijeriya a yanzu sannan ka ga wata da kake son saya daga kasar waje inda ka je yin sayayya, to ka sani suna gogayya wajen inganci."
Kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa waje
Shafin yanar gizo na Hukumar Habaka Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya ya bayyana cewa kashi 71 na fatun da ake fitarwa ana kai su Italiya da Spaniya.
Fatar awaki na tafiya Italiya, wana su ne kashi 68 na wannan kasuwanci. Spaniya na shigar da kashi 21 na fatun awaki Nijeriya inda China ke sayen kamar kashi 4.
India ce ta fi sayen fatar tinkiya daga Nijeriya da kashi 36, sai China da kashi 22.
Ali Muhammad Tilashi ya dauki kusan shekaru goma a wannan kasuwanci, yana aika kwantenoni cike da fata zuwa Italiya, Spaniya, China da India. "Duk abinda ka samar mai inganci, za su saya," Tilashi ya fada wa TRT Afrika.
Inganta Haja
Ko a lokacin da ba a samar da kaya d ayawa, fatun da Ali ke fitarwa a lokaci guda na kaiwa kwantena goma mafi karanci.
"An yi kiyashin cewa a shekarar da ta gabata an fitar da fatar kananan dabbobi daga Nijeriya zuwa kasashen waje na dala miliyan 272," Dr Tagang ya shaida wa TRT Afrika.
Har ma tare da hajoji kamar jemammiyar fata, kasa na iya asarar kudaden shiga saboda kasashen da ke sayen su su karasa amfani da su ne ke sharbar romonsu.
Hakan ne ya sanya dole gwamnatocin Afrika su mayar da hankali wajen kara inganci ga hajojinsu kafin fitar da su kasashen waje.
'Da sauran aiki sosai'
A Njeriya, alkaluman fitar da kayayyaki na nuna cewa masu samar da kayayyaki na cikin gida irin su Winston Leather na da sauran tafiya sosai kafin su iya yin mamaya a kasuwanni kamar yadda kamfanonin kasashen waje da suke shigar da fatu ke yi.
Wadanda NILEST ke baiwa horo na iya yada wa da tallata kayayyakinsu ta yadda su ma za su dinga smaun kudade sosai a kasuwar fatu da kiraga ta duniya.
NILEST na taimaka wa wajen ilmantarwa da horar da mutane kan yadda za a samar da kayayyaki daga fata. Cibiyar na kuma kan gaba wajen gudanar da binciken inganta yadda ake sarrafa fatu a kasar.
"NILEST na gudanar da shirin horaswa na bai daya kan fasahar sarrafa fatu da kiraga, samar da takalma da sauran fannoni masi alaka, domin biyan bukatar da ke karuwa ga wadanda suka cancanci samun horon a masana'antar." Dr Tagang ya fada wa TRT Afrika.