Rawar da ‘yan Afirka da ke ƙetare ke takawa a cigaban tattalin arzikin nahiyar na kara kasancewa muhimmi yayin da yawan kudaden da suke turawa gida ke ƙara yawa lamarin da ke ƙara yawan kuɗaɗe ga ayyukan da za su yi tasiri kan rayuwar mutane.
"’Yan Afirka da ke ketare sun zama wadanda suka fi bai wa nahiyar kudi. Wannan ba bashi ba ne. Muna magana ne kan kyaututtuka ko kuma tallafi 100 bisa 100, wani sabon nau’in kudi mai sauki wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da hanyoyin samun kudin shiga ga miliyoyin ‘yan Afirka," in ji Akinwumi Adesina, Shugaban Bankin Cigaban Afirka (AfDB),a wani taron da aka yi a babban birnin kasuwancin Côte d’Ivoire, Abidjan a cikin watan Disamban bara.
Bankin na cigaban Afirka (AfDB) tare da Hukumar Kula da masu Kaura ta Duniya (IOM) sun kaddamar da wani shiri na dala miliyan 3.9 don haɓaka hannayen jarin ‘yan Afirka da ke ketare a kasashen nahiyar takwas.
Shirin, wanda hukumar kaura ta duniya (IOM) za ta jagoranta, na son karfafa yaki da hijira ba bisa ka’ida ba.
A shekarar 2022, ‘yan Afirka da ke rayuwa a ƙetare, waɗanda aka yi kiyasin cewa sun kai miliyan 160, sun tura dala biliyan 95.6 zuwa Afirka.
Kasar Masar daya ce daga cikin kasashen da suka ci moriyar wannan kudi da ake turawa yayin da ta samu kimanin dala biliyan 28 daga ‘ya’yanta da ke ketare.
Nijeriya ce take kan gaba a kasashen Afirka na Kudu da Sahara yayin da ta samu akalla dala biliyan 20 daga ‘ya’yanta dake ketare.
Wadannan kudaden da ake turawa wadanda gwamnatoci da kungiyoyi masu zama da kansu suka tabbatar suna ba da muhimmiyar gudunmawa wajen rage kwararar dubban ‘yan Afirka zuwa kasashen ketare cikin gagarumin hatsari ba tare da tabbacin samun ingantacciyar rayuwa ba a can.
Shiri na farko
Shirin da Bankin Cigaban Afirka (AfDB) ya kaddamar ranar 3 ga watan Disamba, tare da Kungiyar Tarayyar Afirka da Hukumar Kaura ta Duniya, ya dogara ne kan bai wa ‘yan nahiyar da ke ketare karin dama wajen inganta cigaba a gida domin dakile kwararar bakin haure daga Afirka.
Hukumar Kaura ta Duniya (IOM) ta yi amannar cewa wannan shirin zai iya samar da ayyukan yi da kuma arziki a nahiyar, lamarin da zai bai wa masu neman dama a ketare wani zabin da ya fi afkawa cikin ruwa a wani kwale-kwale mara kyau a wani yanayi mai cike da hatsari da rashin tabbas.
Tattaunawa da ‘yan ketare daya ne daga cikin muhimman ayyukan hukumar IOM a Afirka, inda take shirye-shirye a kasashe da dama tun shekarar 1980.
"Ta hanyar ƙwarewarta, hukumar IOM tana son ta daidaita zuba hannayen jarin mazauna ketare da habaka hannayen jarin ‘yan kasuwa da kuma rage rauni ta hanyar fadada kasuwanci tare da cinikayya a kasashen Afirka takwas," in ji Eric Mazango, mai magana da yawun bakin kungiyar a ofishinta na Addis Ababa, Ethiopia, a hirarsa da TRT Afrika.
Wadanda za su fara cin moriyar shirin, wanda ke samun tallafin hukumar Tarayyar Afirka, su ne ‘ya’yan kasashen Gambia da Liberia da Madagascar da Mali da Somalia da Sudan ta Kudu da Zimbabwe da kuma Togo.
A kasar Togo, asalin masani a kan harkar warware rikici Kag Sanoussi, kudin da ADB da kuma IOM suka ware ya kai kusan kudin Cfa biliyan biyu.
"Yadda ‘ya’yan nahiyar da ke ƙetare ke tasiri kan Afirka maudu’i ne da na sani sosai. Ni ma ina tura kudi gida lokaci-lokaci," in ji shi.
"Kalubale na yanzu shi ne tabbatar da cewa kudaden da aka tura sun ba da gudunmawa wajen cigaba. Kamar da yawa, shiri ne mai kyau da ya kamata a bi shirin da zuciya daya.
"Ya kama mu tallafa wa masu ruwa da tsaki cikin wannan shirin da kuma shirye-shiryensu domin su iya samar da cigaba a aikace domin tabbatar da mutane cikin hali na dama."
Tabbatar da kiyayewa
An yi la’akari da fargabar da Sanoussi ya ambato. Hukumar Kaura ta (IOM) wadda za ta kaddamar da shirin, tana son ta yi amfani da ababen da ta gani a baya wurin tabbatar da cewa shirin ya ci gaba yadda ya kamata.
"The eight targeted beneficiary countries will build on previous and ongoing initiatives, besides the lessons learned in their respective regions. The examples include the IOM-UNDP Development Fund project that began in 2008 with over 700 Somali diaspora experts deployed in their home countries," explains Mazango.
"Kasashen takwas din za su ci moriyar shirin za su yi gini ne kan shirye-shiryen da da wadanda suke tafe baya ga darrusan da aka koya a yankunansu.
"Irin wadannan sun hada da asusun cigaba na Hukumar Ƙaura ta MDD da Hukumar Cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM-UNDP) da aka fara a shekarar 200 inda sama da ‘yan Somaliya na ketare da aka tura kasarsu," kamar yadda Mazango ya bayyana.
Wani binciken da hukumar IOM ta dauki nauyinsa mai taken "tura kudi da kuma tattaunawa da mutanen ketare a Sudan ta Kudu " da kuma hadin gwiwar kungiyar da bankin cigaban Afirka (AfDB) wajen wani shiri a Burundi don rage rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar hada kan ‘yan kasar dake ketare.
Mazango ya kuma ambato tallafin hukumar IOM ga Togo wajen samar da dandalin ‘yan ketare domin tattaunawa, hadin gwiwa da horarwa da kuma harkokin da suka gwamnati da ‘yan ketare domin jin dadin mutanen kasar
Masu cin moriyar
Hukumar IOM tana son ta yi amfani da dala miliyan 3.9 wajen taimaka wa al’ummomin da rikici da sauyin yanayi da sauran bala’o’i suka addaba.
"Waya na da mutum biyar zuwa goma nnan zai taimaka wa akalla mutum 50,000 a kasashen da ake hako, ciki har da mutanen da za su ci moriyar shirin kai tsaye (kashi 50 cikin 100 mata da kuma kasha 40 cikin 100 matasa) da kuma wadanda ba za su ci moriyar shirin kai tsaye ba (domin iyali na da mutum biyar zuwa goma)," kamar yadda Mazango ya bayyana .
Ta hanyar tura kudi kai tsaye ko kuma akashin hakan, wadannan kudaden za su biya kudin dawowar ‘yan ketare zuwa nahiyar don ba da horo a fannoni irin su noma da kiwon kifi da kuma kiwon dabbobi kafin a taimaka wajen komarsu nahiyar.
Sanoussi ya yi ammanar cewa ya kamata a mayar da hankali wajen saka kudi fadakarwa cikin mutanen, musamman matasa kan illar kwarar bakin haure.
"A gare ni, akwai muhimman ababen biyu dake tallafa wa juna. Daya shi ne a sanar da matasa hatsarin da ke cikin kwarar bakin haure.
"Fadakarwa game da hatsarin da yake da shi, yawan mace-macen da yake janyowa, da kuma rashin gaskiyar labarin cewa kasar waje ba ta da matsala. Ya kamata a kara wannan," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ya kuma ba da shawarar saka kudi kan harkoki masu “dorewa” na samar da kudaden shiga.
"Idan muka kayyade matakanmu kan fadakarwa kawai, mutane za su cigaba da afkawa cikin kasadar.
"A wannan shirin da ma shirye-shirye na gaba, dole wadannan su zama amsu dorwa kuma su kara daraja mai yawa domin kada su kauce bayan ‘yan watanni," in ji Sanoussi.
Wadanda za su ci gajiyar shirin daga baya, wanda za a yi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2026, su ne ‘yan kasuwa a kasashen (kamfanoni da kuma hukumoni a kamfanoni masu tallafa wa kanan masan’antu) da bankuna da kungiyoyi masu zaman kansu a kasashe daban-daban na cikin wadanda ake kasashen za su amfana.
Bayan shirin ya isa kasashe takwas na farko, akwia yiwuwar fadada shirin zuwa sauran kasashen Tarayyar Afirka.