Ƴan'uwa da abokan arziƙi suna makokin wacce ta taɓa lashe lambar yabo a wasannin olimfiks Rebecca Cheptegei, wacce ta mutu bayan tsohon saurayinta ya jiƙa ta da fetur sannan ya banka mata wuta / Photo: Reuters

By Emmanuel Onyango

A wajen wasu mata ƴan wasan guje guje da tsalle a Kenya, lashe gasa da samun kyaututtuka da kuma garaɓasar nuna ƙwazo a gasannin ƙasa da ƙasa su ne mafarin samun matsala daga makusantansu.

Gagaruman nasarori da aka nuna wa masu kallo a faɗin duniya ta talabijin, suna sakaye cin zarafi na jiki da na tunani, da ke jiran su a gida daga wajen makusantansu na ƙut da ƙut.

Wata daɗaɗɗiyar matsala ce a wasannin motsa jikin da take faruwa a ɓoye a ƙasar ta gabashin Afrika, amma ƙaruwar labaru - har da na mace mace - yanzu ya fito da komai a fili.

"Babban batu ne da ke buƙatar a magance shi a mataki na ƙasa. Yana da sarƙaƙiya matuƙa kuma yana da wahalar magancewa," Barnaba Korir, wanda shi ne mataimakin jagoran tawagar Kenya a wasannin olamfiks na birnin Faris ya sheda wa TRT Afrika.

Cin zarafi daga makusanta musamman ya zama ruwan dare a Kenya. Aƙalla kashi 30% na mata sun fuskanci cin zarafi na jiki ko na jima'i a ƙasar, inda ya fi faruwa da matan aure, a cewar wani bincike na ƙasa.

Wasu cin zarafin na ɗaukar salon sarrafa tunani da kuma saka wa mutum ya aikata abubuwan da bai yi niyyar aikatawa ba, ya ƙara.

"Ba abu mai sauƙi ba ne kamar yadda masu kallon (wasanni) ke kallon shi. Babbar matsalar ce a wasannin guje guje da tsalle tsallenmu, kuma ana buƙatar matakin gaggawa domin magance ta," mai koyar da wasannin guje guje da tsalle tsalle, Caroline Kwambai ta gaya wa TRT Afrika, tana bayar da misali da tsawo shekarun da ta ɗauka tana sheda yadda ake katse rayuwar wasannin matasan mata ƴan wasan guje guje da tsalle tsalle sakamakon cin zarafi da shisshigi daga abokan zamansu.

An yi Allah wadai da kisan Rebecca Cheptengei a faɗin duniya Photo / Reuters

Kisan gillar da aka yi wa Cheptegei

Kisan gillar da aka yi wa ƴar wasan guje guje da tsalle tsalle ta Uganda, mazauniyar Kenya, Rebecca Cheptegei shi ne lamari na baya bayan nan game da yadda abun da ya faru ba a harkar wasanni ba, ya yi sanadin rasa sana'ar wata ƴar wasan guje guje da tsalle tsalle.

Maƙwabta a gidanta da ke Trans Nzoia county sun bayyana yadda Cheptegei ƴar shekaru 33 da haihuwa ta fito a guje daga gidanta tana ci da wuta, bayan an jiƙa ta da fetur sannan aka banka mata wuta a gaban ƴaƴanta mata guda biyu, kamar yadda aka yi zargin tsohon abokin zamanta da aikatawa.

An yi zargin harin na da nasaba da wata taƙaddama kan wani fili. Ta mutu kwanaki kaɗan tsakani sakamakon raunin da ta samu.

Abokin zamanta, wanda aka zarga da banka mata wuta, shi ma ya mutu sakamakon raunin da ya ji lokacin da abin ya faru.

Ƴar gudu mai dogon zangon ta dawo atisaye a kudancin Kenya kenan, bayan ta halarci wasannin olimfiks na birnin Paris, inda ta gama a matsayi na 44 a tseren dogon zango na mata.

Ita ce ƴar wasa ta uku kenan da aka kashe a Kenya tun shekarar 2021 a lamurra da aka danganta cin zarafin jinsi.

Garin Iten cibiyar atisaye ce mai farin jini tsakanin kwararrun maguda da masu gudu don motsa jiki daga ko'ina a faɗin duniya saboda kyakkyawan yanayinsa. Photo / Reuters

"Ɓagaren wani salo ne. A matsayinmu na ƙasa mun mayar da cin zarafi daga makusanci ba wani abu ba kuma a al'adu da dama, an yi imani wata alama ce soyayya da za ka kyautata matarka," ƴar raji kare haƙƙin bil adama, Immaculate Shamala ta sheda wa TRT Afrika.

A watan Afrilu shekarar 2022, an tsinci gawar da ta fara ruɓewa ta ƴar wasan guje guje da tsalle tsalle ta Bahrain haifaffiyar Kenya, Damaris Mutua, a wani gidan haya a Iten - wani gari da ya shahara a matsayin cibiyar atisaye ta maguda dogon zango.

Wani binciken gawa domin sanin musabbabin mutuwarta ya gano cewa an maƙure ta ne har lahira.

Mahukunta sun bayyana saurayi ta ɗan Ethiopia a matsayin wanda ake zargi na farko. A bara, an kashe magujiya da ta saba kafa tarihi Agnes Tirop da wuƙa a gidanta. Mijinta na fuskantar tuhumar kisan kai, amma ya musa.

Agnes Tirop ta lashe tagwayen lambar tagulla a tseren mita 10,000 a gasar guje guje ta duniya sannan ta lashe gasar tsere ta duniya ta 2015.

Shahara a duniya da dukiya Nasara a fagen guje guje da tsalle tsalle na samar da ɗaukaka da dukiya, kuma ya sa maguda mata su yi watsi da rawar da ya kamata su taka bisa al'adar Kenya.

Amma kuma suna zama masu sauƙin matuƙa ga abokan zamansu su damfare su kuɗaɗe da kuma cin zarafinsu.

"Ga musabbabin nan. Idan tauraron ƴar wasa daga kauye ya haskaka, za ta haɗu da wani mutum da zai buƙaci ya taimaka mata a wajen atisaye ko inganta ƙwazo, daga nan kuma idan tafiya ta yi tafiya sai mutumin ya zama mijinta ko kociyanta," Kociyan ƴan wasan guje guje da tsalle tsalle Boniface Tiren ya sheda wa TRT Afrika.

“Daga nan sai ya fara killace ta daga ƴan'uwa da abokan arziƙinta kuma daga ƙarshe sai ƴar wasan ta dinga rayuwa ƙarƙashin tursasawa. Duk abin da ta mallaka sai ya dawo ƙarƙashin kulawar mijinta," ya ƙara faɗa. Idan ƴar wasa ta yi yunƙurin samun ikon sarrafa sana'arta da kuɗaɗenta, sai cin zarafi ya soma ko ya ƙaru, ya sake daɗawa.

Hukumar Kula Da Ƴan Wasan Guje Guje da Tsalle Tsalle Ta Kenya ta ce tana shiga shiga ƙauyuka da sansanonin atisaye ta ilmantar da ƴan mata game da cin zarafi daga makusanci da kuma ilimin sarrafa kuɗaɗe. An samu waɗanda suka yi nasara da dama, amma cin zarafi da ya zama abin damuwa, na ci gaba da faruwa.

"Abu ne mai matuƙar wahala a magance shi saboda yanayinsa kusancin waɗanda abin ya shafa. Za mu iya raba ma'auratan (zuwa gidajen da babu barazana) amma bayan haka sai su sasanta tsakaninsu kuma su ce ba sa son katsalandan a cikin lamarinsu," inji Korir, wanda shi ne jami'in tsare-tsare na Hukumar Bunƙasa Matasan Ƴan Wasan Guje Guje Da Tsalle Tsalle Ta Kenya.

Ƴan rajin kare haƙƙin bil adama a Nairobi babban birnin Kenya suna zanga-zangar nuna adawa da ƙaruwar kashe matasan mata ranar 27 ga watan Janairu shekarar 2024.

Matan da maza suka kashe A watan Janairu, masu zanga-zanga sun yi tattaki a cikin manyan garuruwa a faɗin ƙasar don nuna adawa da kashe mata, biyo bayan jerin munanan kisa da aka yi wa mata fiye da goma a cikin ƴan makwanni.

Masu zanga-zangar sun ce akwai lamurra irin wannan da dama da ba a faɗa saboda al'adar da ke karfafa cin zarafi daga makusanci.

Ana yawan zargin mahukunta da ƙin ɗaukar mataki da ya dace a kan rahoto da suka samu game da cin zarafi har sai an aikata aikakkiya. Abin da zai saka mutum ya nuna juriya idan aka ci zarafinsa ya ma fi yawa wurin mata waɗanda

TRT Afrika