Kiyayyar Faransa na kara yaduwa a tsakanin mutanen Nijar da ma nahiyar baki daya. Hoto: Others    

Daga

Abdulwasiu Hassan

Shekara daya - ranar 26 ga Yulin 2023- ke nan da Jamhuriyar Nijar ta fuskanci juyin mulki, inda aka hambarar da Shugaban Kasa Mohamed Bazoum daga mulki.

Har yanzu abubuwa ba su daidaita ba a kasar da ke Afirka ta Yamma mai yawan mutane kimanin miliyan 25, wadanda yawanci suka fi magana da Hausa da harshen Farasanci.

Bayan juyin mulkin, sai kasar ta koma kamar yadda ta fuskanta a gomman shekarun baya. Wannan ne karo na biyar da sojoji suka yi juyin mulki a kasar tun ranar 3 ga Agustan 1960 da kasar ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka.

Inuwar mulkin mallakar Faransa

Jim kadan bayan sojoji sun kwace mulkin, sai kasashen Yamma irin su Faransa suka fara kokarin tursasa Janar Abdourahamane Tiani a kan ya janye daga hambarar da Bazoum daga mulki.

Haka suma kungiyoyin nahiyar, kamar Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Tarayyar Afirka suka fito fili suka yi Allah wadai da juyin mulkin, sannan suka yi kira da a dawo da mulkin dimokuradiyya.

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana juyin mulkin da haramtacciya, inda ya yi zargin cewa mulkin sojin zai jawo wahalar rayuwa a kasar da ma yankin baki daya.

Amma sai dai kamar yadda aka yi zato, gwamantin Janar Tiani ta yi watsi da barazanar Macron din, inda ta fito tana ta kalubalantar tsohuwar uwar gidanta din, Faransa.

Gwamnatin sojin ta bayyana rashin tsaro a matsayin daya daga cikin dalilan juyin mulkin. Hoto: Reuters

A lokacin ne kuma ECOWAS ta bukaci gwamantin sojin da ta saki Bazoum ta mayar da shi mulki ko kuma ta fuskanci takunkumin da za a kakaba mata, ciki har da yiwuwar amfani da karfin soji.

Dimbin magoya bayan mulkin sojin ne suka fito suka yi zanga-zanga a birnin Niamey na kasar, wanda hakan ya nuna cewa suna samun karbuwa. Wannan zanga-zangar ce ta nuna akasin abin da aka fara tunani bayan zanga-zangar bukatar a dawo da Bazoum mulkin.

Ra'ayoyi mabambanta

A wajen wasu daga cikin mutanen Nijar, shekara daya bayan juyin mulkin, yanzu ne suke ganin sun samu cikakken 'yanci.

Duk da cewa kasar ta samu 'yanci daga Faransa shekara 64 da suka gabata, 'yan Nijar kamar su mai rajin kare hakkin dan Adam daga Maradi, Abdou Dan Neito, sun yi amannar cewa yanzu ne kawai suka samu cikakken 'yanci daga Turawan mulkin mallaka.

Tahirou Guimba, dan siyasa daga Niamey shi ma ya bi bayan Abdou, inda ya ce, " Muna godiya ga Allah wanda Ya nuna mana karshen mulkin mallakar bayan fage da ake mana tsawon shekarun," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Dan kasuwa Laouali Houseini ya ce shi farin cikin shi da aka yi juyin mulkin ba tare da zubar da jini ba. " Ina tunanin an so a zubar da jini ne, Allah Ya kiyaye. Ko a haka mun fi wasu kasashen. Muna godiya ga Allah," in ji shi.

Yanzu da kasar ta shiga shekara ta biyu a karkashin mulkin soja, akwai ra'ayoyi mabambanta a kan abubuwan da Janar Tiani yake yi daidai da kuma hanyar da ya kamata ya dora kasar a kai domin ciyar da ita gaba.

"Abin da yake ban sha'awa shi ne yanke alakarmu da Faransa da Jamus da Amurka. Mun daina dogaro da sojojin kasashen wajen. Babban abin da mutanen kasar ba sa kauna shi ne komawa karkashin mulkin mallaka," in ji Tahirou.

Tun a 26 ga Yulin 2023 Janar Abdourahame Tiani yake mulki. Hoto. Others

Yanzu me yake so gwamnatin sojin kasar ta yi?

"Shawarata ga gwmanatin yanzu ita ce ta yi adalci sannan su cika alkawuran da suka dauka wa mutane," kamar yadda Tahirou ya bayyana wa TRT Afrika.

"Sannan su sayo kayan yaki na zamani. Za a iya samun irin wadannan kayayyakin yakin daga kasashe irin su Turkiye da China da Rasha."

Shi kuma Abdou cewa ya yi, tabbatar da wadatuwar abinci ga mutanen kasar ne ya fi muhimmanci ga gwamnatin sojin a yanzu.

Dawowa mulkin dimokuradiyya

A daidai lokacin da wasu 'yan Nijar suke kiran a dawo da Bazoum mulki, wasu kuma kuma suna fargabar abin da suka bayyana da "Dimokuradiyyar Turawan Yamma."

Tahirou yana cikin masu irin wannan tunanin, inda ya ce suna sha'awar dimokuradiyya da za ta dabbaka al'adun da muradun mutanen Nijar ne, maimakon aro musu dimokuradiyyar da take cike da cin hanci.

A daya bangaren kuma har yanzu Shugaban Kasa Mohamed Bazoum yana tsare a hannun sojojin da suka yi masa juyin mulki.

"Maganar yaushe za a dawo dimokuradiyya bai dame mu ba yanzu," inji Tahirou a tattaunawarsa da TRT Afrika.

"Abin da ke gabanmu yanzu shi ne yadda za a gyara kasar da yadda za a tsara mana dimokuradiyya da ta yi daidai da al'adunmu da rayuwarmu, ba abin da muka aro daga Turawa ba."

Abdou yana da ra'ayin bai kamata a yi gaggawar kawo batun zaben sabon Shugaban Kasa ba.

"Idan na samu damar ganawa da Janar Tiani, zan ba shi shawarar ya mayar da hankalinsa a kan sulhunta tsakanin al'umma. Muna so ne a zauna a tattauna tare domin samar da hanyar da za a gudu tare a tsira tare," in ji shi.

TRT Afrika