Daga Firmain Eric Mbadinga
Shirin fim dangane da ibtila'i na kokarin bayyana tsoron da ake da shi kan mummunar makomar da da a yanzu ba ma za a iya fahinmtar ta ba saboda tsabagen muni.
A yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi, wannan n abu mai sanya damuwa da tunanin dan adam ba ya bukatar bata lokaci wajen hakaito lallai akwai iti;a'in da ka iya zuwa. Har ma ta zo, kuma yanzu ne.
Shekarar 2023, mafi dumama a tarihi, ta zo da sakamako da dama na gobarar daji da fari a fadin duniya.
A jihar California ta Amurka, na'urar auna zafi ta nuna ya kai 54 a ma'aunin salshiyas a shekarar da ta wuce. A Maroko da ke Arewacin Afirka kuma ya kai daraja 50.
Kambamboli Tankoano, wani dan asalin Burkina Faso, na noma waken suya da kiwon dabbobi sama da shekara 15 a kauyen Ountandeni, wani bangare na jama'ar Diapangou da ke gabashin kasar.
Ga wannan mutum mai tsananin son kasa, yana tsoron illar da suuyin yanayi mara kyau zai iya janyowa.
A matsayin daraktan kungiyar makiyaya da manoma, yana kokarin sanin bayanan kimiyya game da tsananin zafin da el Nino ke janyowa da illar ta ga ayyukan noma da kiwo.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Muna iya gani da jin karantar da ake samu a yanayi, tilastuwa wajen shuka da girbe amfanin gonakinmu, daduwar cututtukan da ke damun dabbobi da tsirrai da kuma tsananin zafi da karancin ruwa."
Tankoano ya yi nuni da ana samun karancin yawan amfanin gona daga watan Yulin 2023 zuwa yau, wanda a bayanan Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya, hakan ya yi daidai da tasirin El Nino da ake samu.
Ya ce "Mun gano yadda ake ta samun fari, wanda ke janyo bushewar mabubbugar ruwan d aake baiwa gonaki da dabbobi.
"Sannan akwai karewar yanayi da wuri wanda ke janyo karancin amfanin da ake samu. Kiwon dabbobi ma ya shiga mummunan yanayi saboda karancin birtali.
Illoli daban-daban
Ndague Diogoul, mai bincike a Cibiyar Bincike Kan Teku da ke Dakar, Sanagal ta ce, tasirin El Nino ya bambanta duba ga yanki zuwa yanki.
A yankin Sahel na Afirka, misali, sauyin da ake samu na zuwa da yanayi gajere. Salon yanayin da ke sauyawa na iya kara tsawon lokacin fari, illata samun ruwan amfanin noman rani da bukatar jama'a.
Diogoul ta kuma ce karancin albarkatun ruwa a yankin Sahel, wanda Burkina Faso wani bangare ce na yankin, na zuwa da illoli da dama da matsin lamba ga manoma da makiyaya.
Ta fada wa TRT Afirka cewa "Yanayin bushewar gari na iya sauya ingancin amfanin gona, yana kawo kalubale ga al'ummun da suka dogara kan kiwon dabbobi. Dadin dadawa, daduwar sauyin da ake samu wajen girbin amfanin gona na iya janyo karancin abincin. Ana iya samun barkewar ambaliya a wasu yankunan."
Karancin ruwa
Shafin kula da muhalli na Planete Mer ya ce "daya daga cikin alamomin farko na sauyin yanayi a teku su ne karuwar zafin ruwan."
"Dadi kan wannan kuma shi ne kaddamar da wasu nau'ikan halitta da za su yi gogayya da wadanda ake da su," inda Diogoul da ke aiki kan illolin El Nino ga teku.
"Binciken baya-bayan nan ya bayyana cewa kifin karfasa na guduwa zuwa arewacin duniya saboda dumi da ruwa ke yi, wanda haan ke sauya wajen zama da yanayin rayuwar kifaye."
Kamar yadda binciken kimiyya da dama ya bayyana, karuwar zafi a 2023 ya shafi dukkan duniya.
Tsakiyar Afirka ma ba su tsira ba. Boris Efoua Aba'a, makiyayin shanu a Libreville, Gabon na fuskantar matsaloli da yawa a gonarsa saboda yanayin da ba a saba gani ba.
"Mun gano cewa zafi ya karu a lokacin rani. wanda yake kai wa har watanni uku na karshe daga Yuni zuwa Agusta, a yanzu yana kai wa har watanni hudu."
Har yanzu karancin ruwa na janyo matsaloli a karkara, "Rijiyoyin da muke da su suna ta bushewa, hakan ke sanya da wahala dabbobi su rayu. A kiwon dabbobi, ruwa na da matukar muhimmanci," in ji Boris.
Yawa da ingancin naman da wadannan gonaki ke samarwa na raguwa sosai, na yin tasiri kai tsaye ga kudaden da ake samu.
Yiwuwar samun waraka
Kasashe irin su Gabon wani bangare ne ayyukan binciken da aka yi kan tasirin EL Nino. Wadannan ayyukan bincike sun yi hasashen za a shiga yanayi mai wahala wajen samun sauyin zubar ruwan sama.
Diogoul ta kuma ce "Mummunan yanyi na kuma kara hatsrin samun gobarar daji, wanda ke tasiri kan zamantakewar halittu."
Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FOA) ta tsara wani daftari don rage illar EL Nino kan manoma da samar da abinci a kasashen da suka fi illatuwa a duniya.
Dala miliyan 160 da Amurka ta ware don gyara koguna da nufin magance ambaliyar ruwa, taimakawa masunta su kare jiragen ruwansu kafin guguwa ta taso, raba irin da yake bijirewa fari, da kuma ajje magungunan dabbobi. Ana bukatar wata dala miliyan 125 don daukar nauyin shirin.
FAO ta bayar da fifikon ayyukanta a kasashe 34 a Afirka, Asiya, Paciic, Latin Amurka da Caribbean, da manufar amfanar da mutane miliyan 4.8 nan da watan Maris din 2024.