Yawancin Bakin hauren su kan yi amfani da dabarun dafa abinci da suka koya a ƙasashen waje don kafa kasuwanci a ƙasarsu ta asali. Hoto: Naima Said Salah  

Daga Naima Said Salah

Yayin da labarin kwararar baƙin-haure da ke bi ta ruwan teku zuwa Amurka da Turai ya karade ko ina, amma akwai wani bangaren na labarin da a cika taɓowa ba.

Yawancin bakin-haure da suka gaza isa wuraren da suka yi burin zuwa ko kuma aka komar da su da zarar sun isa yayin da wasu kuma kan zaɓi su koma kasashensu na asali ta ƙashin kansu.

Tun bayan barkewar yakin basasa a Somaliya a karshen shekarun 1980, kimanin mutum miliyan biyu, kusan kashi 10 cikin 100 na al'ummar kasar ne suka tsere daga kasar.

Somaliya na daga cikin kasashen da al'ummarsu ta bazu a duniya. Yawancinsu sun yi ƙaura ne zuwa ƙasashen Larabawa na yankin Gulf.

A mafi yawan lokuta a kan ajiye su a cibiyoyin kora kafin a mayar da su kasashensu na asali, mafi akasari su kan yi korafin rashin samun kulawa.

An mayar da Abdikadar Abdirahman Hussein mahaifi ga 'yara hudu daga kasar Saudiyya a shekarar 2021 bayan ya shafe tsawon shekaru dama yana zama a can. Da ya dawo Mogadishu, ya yi gwagwarmaya sosai don sake gina rayuwarsa.

Abdikadar Abdirahman Hussein ya kan hada ire-iren abincin Saudiyya a Somaliya: Naima Said Salah

Daga nan ƙwaƙwalwarsa ta gabatar masa kasuwancin soma dafa irin abincin Saudiyya ga ƴan Somaliya.

Ƴan'uwansa sun ba shi gudunmawar dala 500 don ya fara kasuwancin gidan abinci mai suna Boufiyah Jeddah.

Yana amfani da dabarun dafa abinci da ya koya daga Saudiyya wajen dafa irin abincin Larabawa, da suka hada da shawarma da biredi na musamman mai suna khubus, da kuma nama da shinkafa a hankali da ake dafa su tare mai suna mandi.

Gidan abincin da ke kan titin gundumar Hawlwadag na Mogadishu, kan cika da mutane wadanda ke sha'awar ɗandana sabon nau'in abincin, kana ya shahara ga ƴan Somaliya da aka kora daga ƙasashen yankin Gulf waɗanda suka yi kewar irin abincin da suka saba ci a can.

Babban abin da aka fi so shi ne ruwan 'ya'yan itatuwa da kayan marmari hadin gida da hada wa madara da mangwaro da ayaba da kuma kankana da dai sauransu.

'' Na fara ne da sayar nau'in abinci masu sauki akan ƙasa da dala daya wato $0.50," a cewar Mista Hussein "Kasuwancina ya bunkasa cikin sauri kuma zuwa yanzu na dauki matasa shida aiki, wadanda duk aka kore su kamar ni," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

A sannu da hankali kasuwancin su na dada samun karbuwa. Hoto: Naima Said Salah

Ya ce yana samun riba tsakanin dala 20 zuwa dala 30 a rana wanda ya isa ya ciyar da iyalinsa.

Sannan yana biyan ma'aikatansa dala 10 a kowace rana, sannan yana sake mayar da duk wani kari da aka samu cikin kasuwancin.

Mutum na farko da Mista Hussein ya fara dauka aiki shine Adde Abdirashid Mohamed wanda ya bar kasar Somaliya zuwa Saudiyya a shekarar 2017 saboda tashe-tashen hankula da rashin tsaro da suka mamaye kasar.

An mayar da shi gida a shekarar 2022.

"Na kasance ina siyan abinci a gidan abincin ne saboda ina son irin abincin Saudiyya," in ji shi.

"Daga nan na samu dama na shaida wa Hussein cewa na iya girka irin abincin Larabawa. Ya dauke ni aiki kuma ina gode masa saboda rayuwata ta canza. Ina farin cikin zama gida yanzu da nake samun kudi."

Wani ma'aikaci mai Ahmed Aweys Mohamud, bai ji dadi ba bayan tilasta dawowarsa gida Somaliya sakamakon ƙaura da yi zuwa yakin Tekun Fasha tun yana ɗan ƙarami ya dawo kuma ba shi da masaniya sosai kan al'adun Somaliya.

"Mutane a Mogadishu sun kan yi min dariya saboda ban iya magana da harshen Somaliya sosai ba," in ji shi yayin da yake motsa hadaɗɗiyar abincin da daura kan wuta cikin wata katuwar tukunya.

“Kwatsam sai na samu aiki a Boufiyah Jeddah. Muna da fahimtar juna kuma sun zama tamkar ’yan’uwa a gare ni.”

Wani ɗan gudun hijirar da a yanzu ya ke samun ci gabaa gida Somaliya Omar Mohamed Osman.

An koro shi daga Amurka a shekarar 2021 bayan ya gudu daga Somaliya a 2012 saboda barazanar mayakan Al Shabaab.

Da farko ya soma zuwa Afirka ta Kudu ne daga nan ya tafi Amurka a 2017 inda bayan wasu shekaru a can aka ki amincewa da bukatarsa na neman mafaka.

Ya sha gwagwarmaya bayan ya dawo gida Somaliya amma daga bisani ya kafa wani karamin kantin sayar da kayayyaki a gundumar Waberi ta Mogadishu.

Mutanen da suka dawo sun ce, tasa keyarsu zuwa Somaliya ba abu ne mai sauki ba. Hoto: Naima Said Salah

Ya ce ya yi farin ciki da ya tsallake rijiya da baya a shekarar fako da ya yi bayan dawo da shi gida da aka yi.

A yanzu haka matashin mai shekaru 40 yana da ɗa kana yana samun abin da zai iya ciyar da iyalinsa.

Mista Osman ya ce daga cikin mutane 87 da aka kora tare da shi daga Amurka, wasu sun shiga aikin sojin Somaliya, kazalika ya ce da mutane da dama sun mutu bayan da suka kasa samu rayuwa mai kyau a gida yayin da wasu kuma suka sake barin Somaliya.

Wani matashi ɗan Somaliya, Mohammed (wanda ba asalin sunansa na gaskiya ba ne), an dawo da shi Mogadishu bayan kin amincewa da neman mafakarsa a Birtaniya, komai ya tsaya masa tcak a lokacin da ya koma kasarsa ta haihuwa.

Da farko dai ya kasa samun inda zai zauna ko isasshen abinci da zai ci. A hankali, ya fara sake gina rayuwarsa.

Ya fara ne a matsayin mai horar da ƴan ƙwallon ƙafa mai zaman kansa, a wasu lokutan ya kan samu dala daya a matsayin tukwici. Sai kuma ya samu aiki a matsayin Lebura da ke aikin na wasu sa'o'i a wuraren gine-gine, sana'ar da ya koyo daga Birtaniya.

Daga baya wani kamfanin gine-gine ya ba shi aiki na dindindin kuma a yanzu ya soma tara iyali.

Kazalika matan da aka koro su suma suna taimakawa wajen ci gaban al’ummarsu.

Wasu sun sauya masana'antar kyau da kwaliyya ta Somaliya ta hanyar bullo da sabbin dabaru, kamar salon gyara gashi iri daban-daban da kuma kwalliya irin ta amare.

Da yake galibin gidajen kwalliya mata ne suke mallakarsu kuma ma'aikata mata ne kawai suke dauka aiki, waɗanda aka kora sukan ji daɗin aiki a irin waɗannan wuraren.

Sauran wadanda suka dawo kuma su kan rungumi sana'ar kawata wuraren biki a irin salon da suka gani kuma suka koya yayin da suke zaune a kasashen waje.

Ko shakka babu, yawancin waɗanda ake dawowa da su gida kan yi gwagwarmaya don tsira, musamman waɗanda ba su da dangi ko ƴan uwa a Somaliya da za su iya taimaka musu don su kafa kansu.

Wadanda aka tilasta dawowarsu musamman bisa ga aikata manyan laifuka suka shafi muggan kwayoyi, su kan fusknaci tsangwama daga al’ummarsu.

Ƴan ciranin da aka dawo da Somaliya sun bayyana rashin sauki da wahalhallun da ke tattare da rayuwa bayan isowarsu kasar.

Amma ga jajirtattu da kuma ƴan kasuwan cikinsu su kan dawo da sabbin dabaru ƙasarsu inda suke koyar da wasu tare da samar ayyukan yi.

TRT Afrika