Azzaluman shugabanni a Afirka da sojojin haya na Yamma ko kuma kamfanoni masu zaman kansu na soji da tsaro (PMSCs) sun samo asali ne tun lokacin fataucin bayi da kuma kutse a zamanin mulkin mallaka.
A shekarar 2002, kwamitin harkokin waje na Majalisar Dokokin Birtaniya ya saki wata takarda me ɗauke da doka wadda za ta sa ido kan sojoji masu zaman kansu. Dokar ta nuna cewa sojojin haya na yammacin Afirka ba komai bane illa alheri ga nahiyar.
Da yake bayar da misali da gawurtattun sojojin haya irin su Irishman Mad Mike Hoare da Frenchman Bob Denard da Belgian Jean Schramme a Afirka a shekarun 1960 da 1970, dokar ta bayyana yunƙurin da ƙasashen yamma ke yi na "ci gaba da samun ƙarfin iko kan yankin mai albarkatu" da alaƙa "masu mulkin mallaka da ke son ci gaba da samun ƙarfin iko".
Masana'anta mai cike da ruɗani
A tsarin tsaro na zamani, kamfanin tsaro da sojojin haya suna da rajista a hukumance domin "samar da tsaro da shawarwari da kuma bayar da horon soja ga sojoji da 'yan sanda na gwamnatoci".
Galibi suna aiki ne a ƙarƙashin sa ido, a wasu lokuta ma’aikatansu ana kiransu sojan arziki ko sojojin haya, domin su kan tsallake iyaka don shiga fadan soji da ayyukan siyasa, ko na tattalin arziki, ko kuma aikata rashin gaskiya a ƙasar da aka tura su.
Shekarun 1960 da 1970 sun kasance wasu shekaru da aka yi amfani da sojojin haya a Afirka, wanda shaidar hakan na ƙunshe a cikin wasu bayanai shida game da sojojin haya da aka rubuta a wata saɗarar doka ta 47 da ta yi bayani kan Dokar Geneva a 1977.
A wata maƙala da aka wallafa a watan Yulin 2023 a The Standard — "Yadda Landan ta zama gida ga wasu daga cikin kamfanonin tsaro mafi gurma" kamar yadda Sophie Wilksinson ta ruwaito Aegis da G4S na Birtaniya na cewa waɗanda kamfanonin tsaro ne da ke cikin biyar mafi girma a duniya.
Haka kuma an bayyana Aegis a matsayin "kamfani na biyu mafi girma da ya fi ɗaukar ma'aikata a duniya bayan Walmart, inda yake da sassa a ƙasashe 125". A faɗin duniya, ana sa ran waɗannan kamfanonin za su samu kuɗn shiga kimanin fam biliyan 231 kimanin dala biliyan 297 a 2026.
Mattatara a Turai
Wasu daga cikin kamfanonin tsaro a Afirka sun haɗa da Aegis da G4S. A baya-bayan nan, kamfanin sojojin haya na Wagner da ke Rasha ana yawan ganinsa wurin rikice-rikice a Afirka.
Daga cikin manyan kamfanonin tsaro masu zaman kansu na Faransa, akwai Agemira wanda kamfani ne da ke aiki a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo da kuma kamfanin Corguard da ke aiki a Ivory Coast. Secopex na aiki a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Somaliya da Libiya, wanda a nan ne aka kashe wanda ya ƙiƙiro kamfanin Pierre Marziali a wani juyin juya hali a 2011.
Sakamakon kwantiragi ta kuɗi masu yawa da kamfanin ya samu a DRC, Agemira ya jawo wasu masu bayar da shawarwari na Romania da Serbia a kan teburi. "Kamfanin ya tsani a kira sa 'sojojin haya', inda yake jaddada cewa su masu horarwa ne," kamar yadda ɗan jaridar Kongo Jaffar Sabity ya shaida wa TRT Afrika.
Sabity na ganin cewa duka Kongo da Agemira na tsoron takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda aka sabunta a Fabrairun bana domin mayar da hankali a kan "shugabannin soji da na siyasa na kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo."
Haka kuma ya bayyana cewa akwai masu fashin baƙi da dama da suka amince da cewa Agemira na da hannu sosai wurin yaƙi da 'yan tawaye irin su M23 na Jamhuriyar Dimokuradiyya Kongo. "Ba mamaki shi ya sa suke saka uniform mai tutar DRC," kamar yadda ya bayyana.
Alamar tambaya game da tushe
Bayan yaƙin duniya na biyu a Afirka, sojoji masu zaman kansu da kamfanonin tsaro na soji sun soma kitsa jerin juyin mulki tare da daƙile masu fafutikar neman 'yanci tun daga Zambia zuwa Burkina Faso.
Yunƙurin da aka yi na juyin mulki a Equatorial Guinea a ƙarƙashin jagorancin sojojin haya waɗanda ɗan kasuwar nan Mark Thatcher ya rinƙa ɗaukar nauyinsu da kuɗi, hakan ya buɗe sabon shafi na kamfanonin tsaro na ƙasashen yamma a ƙasashen Afirka. Mark Thatcher ya kasance ɗa ga tsohon Firaiministan Birtaniya Margaret Thatcher.
A halin yanzu bayan zamanin mulkin mallaka, ana zargin kamfanonin tsaro masu zaman kansu na ƙasashen yammaci da haɗa baki da manyan kamfanoni da kuma wasu ƙasashe ta ƙarƙashin ƙasa domin sace albarkatun ƙasa na Afirka, da safarar makamai da horar da 'yan tawaye.
"Kamfanonin soja masu zaman kansu suna haifar da haɗari da yawa - mulkin mallaka ne ta wasu hanyoyi," kamar yadda Lauyan Najeriya Idris Bawa, wanda ke aiki a matsayin mai ba da shawara kan samar da zaman lafiya ya shaida wa TRT Afrika.
"Suna haifar da matsaloli a cikin sahunmu sannan su ba mu shawara da mu samu sojojin haya da za su taimaka wajen warware matsalar da suka haifar mana."
Ya kamata Bawa ya sani, kasancewar yana cikin shirin horaswa da kamfanin bada shawara na soji na Birtaniya BMATT ya tsara wa sojojin Najeriya.
"Bayan abin da yake a zahiri, akwai sauran abubuwan da ke kawo masu horar da sojoji na kasashen waje zuwa Afirka," in ji shi.
Tarihin da sojojin haya suka kafa
Kwanan nan, gwamnatocin Afirka masu rauni waɗanda aka saka wa takunkumin makamai da na kuɗi sun gayyaci sojojin haya daga manyan ƙasashen duniya irin su Rasha da China da Turkiyya domin taimaka musu magance musu matsaloli.
Duk wani tarihi na sojojinhaya a Nijeriya dole ne ya soma daga sojojin haya daga - Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal da sauransu.
Ta hanyar ci da yaƙi da kuma yarjejeniya da wasu manyan shugabannin al'umma na Afirka, sojojin haya na zamanin mulkin mallaka sun soma tatsa da mamaye wasu sassan ƙasashen Afirka da suna daƙile masu cinikin bayi, inda daga baya suka soma tatsar arziƙin Afirka da kuma ayyukan mishan.
Zimbabuwe da Zambiya misalai ne guda biyu na ƙasashen Afirka da suka farfaɗo daga duddugar tokar kamfanonin sojin haya na Birtaniya, waɗanda aka ba da izini su kwace, da gudanar da ƙasashen da ake yi wa mulkin mallaka a Afirka a madadin gidan sarautar Birtaniya.
Ƙasashen biyu da ke kudancin Afirka duka ana kiransu Rhodesias, aunan da ya ɗauki alamar Cecil Rhodes, sanannen sojan haya na mulkin mallaka na Birtaniya kuma ya ci kudancin Afirka da yaƙi.
Bayan cin Rhodes da yaƙi a 1899, sai ya samu amincewa na tatsar arziƙin albarkatun ƙasa na Zambesia, sai ya kafa kamfanin British South Africa Company, wanda ya aza tubalin gina wani lardi na masarauta wanda aka yi masa laƙabi da sunansa.
An rubuta wannan a cikin littafin Stephen Alexander Massie na The Imperialism of Cecil John Rhodes, wanda ya ba da tarihin sanya sunayen yankunan da ke kan kogin Zambezi a matsayin "Rhodesia ta Arewa" da "Rhodesia ta Kudu". A ƙarshe sun samu 'yanci - Zambia a 1964 da Zimbabwe a 1980.
A cikin littafinsa mai suna The Trial of Cecil John Rhodes, marubucin nan dan Najeriya Adekeye Adebajo ya rubuta cewa, “An sha fada a zamanin daular cewa fatauci ya bi tuta, a gaskiya Rhodes ya juyar da hakan, gwamnatin Birtaniya ta bi sahunsa da ba da lamuni. goyon bayan siyasa, tattalin arziki, da da kuma taimakon soja domin taimaka wa sojojin hayarsa.
A cikin 1898, gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya ta amince da mallaka da kuma sunan Rhodesia a hukumance, wanda mazaunan suka karbe ba bisa ka'ida ba tun 1890.
Dogari mai zalunci
Duk da ƙara masa girma zuwa babban dogari, sunan "sojojin haya" ba za a iya raba shi da Baron Frederick Lugard, ɗan mulkin mallaka na biyu na Birtaniya a Afirka. Tsohon sojan kuma ya yi aiki a matsayin mai gudanar da mulkin mallaka a yankuna daban-daban na gabashi da yammacin Afirka.
Bayan ya yi aiki a Indiya ta Birtaniya, Kyaftin Lugard ya jagoranci ayarin sojoji masu zaman kansu da 'yan kasuwa da aka aika zuwa Afirka. Daga karshe ya shiga cikin kasashe goma sha biyu, daga Sudan zuwa Nijeriya da Tanzaniya zuwa Malawi.
A cikin littafinsa da ya yi tsokaci game da sake duba halin kirki na manufofin mulkin mallaka na Birtaniya a gabashin Afirka, masanin tarihin kasar Norway Jonas Fossli Gjersø ya yi rubutu game da yadda Lugard ya taka rawar gani wajen yin amfani da sojojin haya wurin gudanar da mulkin mallaka.
Ɗaya daga cikin misalan hakan shi ne wata yarjejeniya da wani kamfanin Lugard ya saka wa hannu a Disambar 1890 da Sarki Mwanga II na Buganda, wanda ya saka garin a ƙarƙashin tsaron kamfaninsa.
Tun daga 1894, Lugard ya rinƙa hulɗa da wasu kamfanonin Birtaniya na mulkin mallaka waɗanda suka haɗa da Royal Niger Comany da British West Charterland Company da ke Botswana da African Lakes Corporation na Malawi da Mozambique.
Dawowa bayan Yaƙin Duniya II
Maƙalar Wilkinson ta yi bayanin yadda "wasu ƙananan kamfanonin sojojin haya na Birtaniya suka yi amfani da yaƙin da ake yi a kudancin duniya" a shekarun 1960 zuwa 1970.
Sojoji na hayar sojoji da masu bin inuwar inuwar turawan mulkin mallaka sun taka muhimmiyar rawa wajen "murkushe tawaye da tayar da tarzoma".
Sojojin haya da wasu da ke taya Turawan mulkin mallaka ayyukansu sun taka muhimmiyar rawa wurin "daƙile tarzoma da tashin hankali".
A cewar rahoton na ofishin harkokin wajen Birtaniya, karshen yakin cacar baka ya kawo tsofaffin sojoji waɗanda wasu kamfanoni irin su Sandline da Executive Outcomes suka ɗauka aiki, waɗanda suka kawo ƙarshen 'yan tawaye a Saliyo da Angola.
Kamar yadda Sabity ya ambata, sojojin kasashen waje sun dade suna tsoma baki cikin al'amuran kasashen Afirka ta tsakiya - a cikin al'amarin DRC, tun bayan zuwan sojojin haya na Schramme na Belgium a Mobutu Sese Seko wadda a baya take Zaire.
Dan jaridar ya kuma bayar da misali da zargin da ake yi wa wasu sojojin haya na Ingila da Australiya da kuma Isra'ila da ke aiki a yankin 'yan tawayen na M23.
A lokacin yaƙin basasa na Nijeriya a shekarun 1960, an zargi sojojin Faransa da na Isra'ila wurin tsawaita yaƙin wanda ya shafe watanni 30 ana yi.