Daga Pauline Odhiambo
A tarihi ko a harkar ƙagaggun labarai, batun mata mayaƙa masu rashin tsoro da ƙarfin hali wani batu ne daɗaɗɗe.
A fina-finan kamfanin Marvel inda ake nuna duniyar tatsuniya ta Wakanda, rundunar jarumai ta Midnight Angels suna tsoratarwa, kuma suna sanye da sulkensu na yaƙi mai fukafukai inda suke gadin ƙasarsu da a'ummarsu.
Ita ma Afrika, tana da nata mayaƙa mata. Cikin aƙalla shekaru 300 daga ƙarni na 17, rundunar soji ta mata zalla mai suna Agojie ta yi yaƙin kare daular Dahomey, wadda a zamanin yanzu ta zama ƙasar Benin.
Tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, lokacin ganiyarsa, yana da rundunar Amazonian Guard, waɗanda suka ƙunshi dakarun tsaro mata masu kare shi har zuwa lokacin da aka hamɓarar da shi aka kuma kashe shi a 2011.
Duk da tarihin da ake da shi na mata mayaƙa, a harkoki da masana'antar ba a girmamam mata, kuma suna fuskantar ƙalubale da dama wajen haɓaka sana'arsu.
Wannan shi ne ainahin abin da ya ba wa Sienna Dutkowski ƙwarin gwiwa wajen kafa kamfanin Lady Askari, wanda ke harkokin tsaro da jigo kan mata, wanda aka kafa a Kenya da Habasha don ɗaukaka matsayin mata a fannin tsaro.
Sienna ta faɗa wa TRT Afrika cewa, "Da yawan mata ƙwararru kan tsaro suna da aniyar haɓaka fannin tsaro, saboda fitacciyar basirarsu da masaniyarsu. Amma ba sa samun damar yin hakan saboda ba a ba su sarari a fannin ba".
Bayanai da Cibiyar International Security Training Academy (ISTA) ta tattara sun nuna cewa mata sun kai kashi 11% na ma'aikatan tsaro a faɗin duniya.
Kamfanin Lady Askari yana da manufar samar da damar samun horo kan ga ƙwararru kan tsaro, musamman mata, don inganta matakin ƙwarewarsu da haɓaka cigaban sana'arsu.
Kariya mai ƙarfi
Kalmar Askari, tana nufin "askarawa" a harshen Swahili, kuma ana amfani da sunan yawanci da nufin jami'in tsaro wanda ke gadin mashigar unugwanni, ko ginin ofis, ko shaguna a Kenya.
Yawancin asakarawa a ƙasar ma'aikata ne da ke matakin aiki na farko, waɗanda ba su da horo kan tsaro, wanda hakan ke taimaka wa wajen ƙarancin mata a harkar.
"Idan kashi 89% na ma'aikata a fannin tsaro maza ne, to kayayyakin da ake samarwa suna samuwa ne da irin mahanga ta maza," in ji Sienna, wadda ma'aikatanta ya ƙunshi ƙwararru kan tsaro 97, da mata 58.
"Fannin tsaro da mai jogo kan mata ba shi da manufat haɗa jayayya da maza da mata. Yana da manufar nemo hanyoyin da basirar mata, da ƙarfinsu wajen dacewa da tsarin rayuwa daban-daban, zai iya tasiri ga fannin tsaro."
Nazarin da ISTA ta yi ya bayyana cewa mata da dama sun ɗauka cewa jami'an tsaro dole su zama masu ƙwanji, kuma cewa aikin yana da "matuƙar haɗari" ga mata.
Sienna ta ce wannan rashin fahimta yana masa amfani yayin tattara bayanan tsaro don buƙatun daban-daban.
"Ɗaya daga cikin jami'an tsaro mata masu ba da kariya ga mutum tsayinta bai wuce ƙafa 5ft ba," cewar Sienna.
Aikin tsaron lafiyar fitattun mutane shi ne ba mutane wadanda suke fuskanta barazana kariya saboda yanayin daukakarsu ko arzikinsu ko dangantakarsu.
Don haka, ta yaya za a yi amfani da mace wajen wannan aiki? Winni Bolo, mai aikin ba da kariya mai tsayin kafa biyar ka karanta sanin halayyar dan Adam ne a jamia, sannan ta kasance tana wannan aikin tun a shekarar 2020.
Tsarin mace bai kula da lafiyar mutane na ba mutane da dama mamaki. Mutane da dama sukan dauka ni sakatariya ce ko mai taimakawa ta musamman a duk lokacin da nake gudanar da aikina, wanda hakan ke taimaka min wajen samun saukin aikin.
Cikin sauki nake sajewa cikin mutane, in rika samun bayanan sirri ba tare da sun gane ni ba, inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika.
Haka kuma ai ba dukkan aikin samar da tsaro ba ne yake bukatar karfin tuwo. Misali, ai aikin kare aukuwar barazana kwakwalwa yake bukata, in ji ta.
Amfani da kwakwalwa
Haka kuma a kamfanin Lady Askari suna amfani da kwararrun masana harkokin tsaro da suka kware a bangaren binciken kwakwaf, tattara bayanan sirri da sauransu.
Haka kuma a kamfanin Lady Askari suna amfani da kwararrun masana harkokin tsaro da suka kware a bangaren binciken kwakwaf, tattara bayanan sirri da sauransu.
Ta bayyana wani lokacin baya da mijinta James ya taba jagorantar masu gadin ambasada mace zuwa wani aiki a Iraq, wanda abin da ya faru ya sat a kara gane muhimmancin mata a wannan aikin.
Ambasadar ta tambaya James yaya za a yi idan za ta shiga bandaki, sai ya fada mata cewa sun riga sun tsara inda za ta shiga domin biyan bukatarta.
Sai ambasadar ta bukaci James ya tattara abokan aikinsa maza su je su gyara mata bandakin, sannan ya sanya mai gadi daya a kofar bandakin, wani kuma a bakin tagar duk lokacin da take ciki.
Da a ce akwai mata, da aikin ya fi musu sauki a irin wannan yanayi, in ji Sienna.
Don haka idan har ana so a magance dukkan matsalolin tsaron mutane, dole a rika amfani da kwakwalwar mutum wajen daukar masu gadin ba karfin jiki kadai ba. Samun kwararrun mata yana da matukar muhimmanci, wanda hakan ya sa muka sanya wa kamfaninmu sunan mace.
Tattara bayanan sirra da hadin gwiwa
Bangaren tattara bayanan sirrin kamfanin Lady Askari mata ne suka fi yawa-abin da Sienna ta bayyana da cewa ya taimaka musu wajen samun nasara.
Wannan fahimtar ta cewa mata sun cika gulma tana taimakawa, musamman wajen bincike da tattara bayanai, inji ta, sannan ta kara da cewa, a bangaren tsaro, gulma na da muhimmanci wajen tattara bayanan sirri.
Kwarewar da Sienna ke da ita a bangaren harkokin ci gaban alumma ya taimaka mata wajen samun hadakar aiki da kungiyoyin cikin gida da na kasashen duniya domin tabbatar da tsaron alumma.
Muna aiki da kungiyoyi kamar I Am My Bodyguard, wadda ke horar da mutane yadda za su kare kansu, musamman yara kanana, in ji ta.
Haka kuma muna aiki da She Hacks da Gidauniyar Protect Us Kids da sauransu, musamman bibiyar shafukan sada zumunta da suke jawo hankalin kananan yaranmu.
Haka kuma kamfanin Lady Askari ya gina wuraren wasanni a gidajen yari a kasar Kenya domin yara da mata su samu wajen shakatawa.
Yanzu Sienna tana yunkurin daukar direba mace ce, wadda kuma ta iya kanikanci.
Muna koyar da maaikatanmu tuki domin yana da alaka da kare kai, inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika.
Matsalar da muke fuskanta ita ce tukin ba da kariya na bukatar wasu lasisi na musamman da wasu horo na musamman, amma muna kokarin samun hadaka da wasu makarantun koyon tuki domin cimma wannan.