Ranar Malamai ta Duniya: Yadda Nijeriya za ta cimma muradun saka yara a makaranta

Ranar Malamai ta Duniya: Yadda Nijeriya za ta cimma muradun saka yara a makaranta

Nijeriya tana cikin jerin kasashen da suka fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.
Nigeria tana fama da ganin miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta sun samu shiga aji. / Hoto/Reuters

Daga Abdulwasi'u Hassan

Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya yana tayar da hankali. Nijeriya tana kokarin ganin ta fadada shirin ilimantar da yara mafi karancin matakin karatu.

Wannan yunkuri ya zamo dole, ganin yadda illolin hakan yake bayyana.

Nijeriya tana bukatar akalla makarantu 20,000 kafin ta iya samun daukar yaran da a yau ba sa cikin tsarin karatun zamani.

A cewar shugaban Hukumar Ilimin Matakin Farko, Dr Hamid Bobboyi, hakan na nufin samar da azuzuwa 907,769 don tabbatar da wadannan yaran ba su ƙare da jahilci ba.

Kididdigar da Dr Bobboyi ya ayyana ba ta haɗo da babban batun ba: wato adadin yara a Nijeriya da ba sa zuwa makaranta. Wani rahoto da UNESCO ta saki a 2022 ya bayyana adadin ya kai yara miliyan 20.

Ana kallon adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a matsayi wani abin ban-tsoro, inda masana da jami'an a Nijeriya suke ganin dalilin tsoron shi ne kasar tana da al'umma miliyan 200, wato mafi yawa a Afirka.

Ranar Malaman Makaranta ta Duniya, ita ce ranar da ake tunawa da amincewa da "Shawarar Matsayin Malaman Makaranta ta Kungiyar Kwadago ta Duniya/UNESCO ta 1966".

Matsala mai munana

Kididdiga a hukumance ta baya-bayan nan, ta ƙiyasta adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya ya kai kusan miliyan 10, shekaru goma da suka wuce kenan.

Ra'ayi mafi rinjaye shi ne abin ya munana a shekarun baya-bayan nan, sakamakon karuwan al'umma da matsalolin tsaro a ƙasar.

Nijeriya ta kafa tsare-tsare dan samar da ilimi ga kowa. / Hoto: Getty Images

Masana sun ce mafita guda daya ita ce inganta samar da wuraren karatu, daidai da ƙaruwar da ake samu na adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ilimi ga kowa

A 2004, gwamnatin Nijeriya ta ƙirƙiri Dokar Ilimin Bai-daya, wadda za ta tabbatar da ilimi kyauta kuma wajibi ga dukan yara a matakin shekarun da ya dace, na firamare da ƙaramar sakandire.

Wasu yaran da ba sa zuwa makaranta suna yawon talla don samar da kudi ga iyayensu. / Hoto: Getty Images

Shirin na gwamnati yana da burin cimma ilimin bai-ɗaya har zuwa matakin ƙaramar sakandire.

Dokar har ta ayyana hukuncin da ya ƙunshi tara ko zaman gidan yari, idan iyaye suka saba wa tanade-tanaden wannan dokar.

An ƙarfafa dokar ta hanyar kafa Hukumar Ilimin Bai-daya, wadda take samun kashi 2% daga Ausun Kudin-shiga na Nijeriya, mai suna Consolidated Revenue Fund.

Hukumar tana amfani da kudin don daukar nauyin ayyukan ilimin bai-daya a jihohi 36 na kasar, karkashin sharadin kowace jiha za ta samar da wani bangare na kudin daukar nauyin ilimi a jihar.

Ya zuwa shekarar 2022, kudaden jihohi da dama sun makale a hukumar, yayin da wasunsu ba su bayar da nasu tallafin ba. Tsarin da ake kai yana hana wasu jihohin damar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

A cewar wasu masana, ko da wadannan jihohi sun iya samun kudaden kuma har suka kashe su gaba daya kan ilimin firamare, kalubalen samar da ilimin bai-daya ba zai kau ba.

Dr Danlami Bala Gwammaja, daraktan tsara karatu a makarantar Aminu Kano College for Legal and Islamic Studies da ke Kano a Nijeriya, ya fada wa TRT Afrika cewa, "Matsalar ta ci gaba da hauhawa tsawon lokaci kuma yanzu ta girmama. Ko da gwamnati ta mayar da hankali don kawar da ita, za ka ga sauyin da za a samu kadan ne."

Dabbaka dokar

Wata matsala dangane da Dokar Ilimin Bai-Daya wadda masana suka nunar ita ce bukatar cikakkaen bayanin yadda za a hukunta wadanda suka saba wa dokar.

Masu sharhi suna ganin gwamnati da daidaikun mutane suna da rawar takawa don ganin duka yara sun shiga makaranta. / Hoto: Getty Images

"Daga shekarar 2004 zuwa yau, ban taba jin an kai wasu iyaye kotu ba ko an hukunta su saboda kin kai yaransu makaranta," a cewar Dr Dalhatu Jumare na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Ya kuma ce dokar ba ta ce komai ba kan wasu tarin batutuwa da ke da alaka da yadda za a kaddamar da hukuncin wadanda suka karya dokar.

Dr Jumare ya kara da cewa, "Shin iyayen ne za su kai kansu bayan ƙin kai ƴaƴansu makaranta ba, ko kuwa al'umma ce za ta kai ƙarar iyayen? Ko kuma alhakin malaman makaranta ne yin hakan, ko 'ya'yan ne za su kai karar iyayen da suka ki tura su makaranta?"

Wata matsalar da masana suke nunawa ita ce gane alhakin sassan gwamnati dangane da aiwatar da shirin.

Dr Jumare ya gaya wa TRT Afrika cewa, "Akwai giɓin aikin dabbaka dokar, abin da aka saba gani a Afirka, musamman a Nijeriya. Duk sanda aka batun dabbaka doka, akan ga rashin damuwa wajen aiwatar da shirin wanda yake hana cigaba".

Tunanin iyaye

A cewar ƙwararru, iyaye da ba su yi nisa a karatu ba, ko wadanda ba su riga sun cimma alfanun ilimin matakin farko ba, sun fi karancin mutunta batun saka yaransu a makaranta.

Dr Gwammaja ya ce, "Yawancin mutane a karkara talakawa ne, kuma suna dogara ne kan 'ya'yansu don samun kudade saboda suna tura su talla, musamman yara mata."

Jami'an gwamnati sun ce Nijeriya tana bukatar karin makarantu 20,000. / Hoto: Getty Images

Wani shiri na bai wa iyaye kudi don ganin sun tura yara mata makaranta, wanda aka kaddamar wa wasu jihohi kamar Kano a arewacin Nijeriya tun shekara 10 da suka wuce, sai dai ba a ga babban tasiri ba.

Ganin yadda rayuwa take ƙara tsada, da karuwar talauci, masu sharhi suna ganin lamarin zai kara kamari ga iyaye wajen biyan kudin makaranta.

Mafita

Wata mahangar masana ita ce gwamnatin tarayya tana bukatar ta dauki gabarar wannan aiki don tabbatar da aiwatar da shirin ilimin bai-daya.

Masana suna ganin daukar karin malamai da ba su horo, tare da inganta yanayin aikinsu da wuraren aikin, suna da babban tasiri wajn magance matsalar karatu.

Dr Jumare ya ce, "Idan gwamnati tana iya daukar nauyin biyan diyya don rushe gine-gine don a yi tituna, to kuwa ba ta da wani dalilin kin yin haka idan ana batun makarantu, ko lokacin da makarantu ke bukatar a fadada su".

Haka nana, masana sun yi imanin cewa iyaye da sauran 'yan kasa dole su tallafa wa yunkurin gwamnati wajen samar da bayanai da rohotannin kan ilimi kyauta, da yadda ake saba wa dokar shirin.

TRT Afrika