Gwamnatin Nijeriya na fatan amfani da CNG zai rage wahalhalun da cire tallafi fetur ya jawo. Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Shekara guda kenan tun bayan ɗaukar matakin cire tallafin man fetur a Nijeriya wanda ya jawo cece-ku-ce da ɓacin rai daga al'ummar

Tun cikin shekarun 1970 gwamnatin Nijeriya ke biyan tallafin man fetur, lamarin da ya rage wa 'yan ƙasar raɗaɗin tsadar fetur da wasu ƙasashen ke fama da shi tsawon shekaru a duniya.

Kwatsam, sai ga shi a watan Mayun 2023 gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar da cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙrshen biyan rarar man fetur da yake tsotse lalitar gwamnati tsawon lokaci.

Amma duk da cewa an daɗe da cire tallafin, 'yan ƙasar da dama na ci gaba da jin raɗaɗin tasirin hakan. Litar mai da a baya ake sayar da ita a kan Naira 190 (kwatankwacin dala 0.12) a yanzu kudinta ya kai Naira 700 zuwa Naira 1,000 ((kwatankwacin dala 0.46 zuwa 0.65).

Wannan lamari ya yi matuƙar sawa farashin sufuri ya ƙaru sosai, sannan tsadar rayuwa ta sake ta'azzara.

To me gwamnati ke yi ne don magance wannan matsala wacce ƙwararru suka yi amannar dole ana buƙatar ɗaukar tsattsauran mataki a wata gaɓar?

Canjin da aka tsara samarwa na komawa amfani da iskar gas, ko CNG, a bayyane yake cewa ita ce sabuwar hanyar yaƙi da matsalolin makamashi na ƙasar.

Don "rage raɗaɗin tsadar fetur da ke gallabar talakawa", gwamnatin ta ware Naira biliyan 50 (kwatankwacin dala miliyan 34) don sayen motocin bas da keke mai ƙafa uku masu amfani da iskar gas har 5,500, da ababen hawa masu amfani da lantarki guda 100 da kuma kayayyakin da ake amfani da su wajen sauya ababen hawa daga fetur zuwa gas.

Gwamnati ta ce samar da motocin bas masu amfani da CNG zai rage wahalhalun sufuri. Hoto/Reuters

Manufar ita ce a yi amfani da albarkatun iskar gas da ake da su a kasar don fara rage tasirin da cire tallafin ke yi a kan tsadar rayuwa da kuma ƙara ƙaimi a hankali wajen bunƙasa tattalin arziki.

Tuni dai gwamnatin Shugaba Tinubu ta tsara manufar ƙarfafa amfani da CNG a matsayin madadin man fetur da dizal a fannin sufuri.

Ƙarancin amfani da ma'adanai

Ana kallon yawan iskar iskar gas ɗin da Nijeriya ke da shi da ƙarancin amfani da shi a matsayin man sufuri a wani saɓani na tattalin arzikin a ƙasar.

Nijeriya wadda ke da iskar gas har kubik mita tiriliyan 206, tana daga cikin manyan ƙasashe 10 da aka albarkace su da wannan ma'adanin. Akasin haka, bisa ga bayanai daga worldometer.info, Nijeriya tana matsayi na 38 a cikin ƙasashen da suka tara iskar gas ɗinsu.

Abin farin cikin shi ne cewa a shekarun bayan nan gwamnatin Nijeriya na ta ƙoƙarin jawo hankalin masu zuba jari a fannin albarkatun gas ɗinta.

Kwanan nan Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da kamfanoni uku a wani ɓangare na wannan shiri, a jihohin Delta da Imo. A wuraren tarukan ƙaddamarwar, ya tabbatar wa masu zuba jari cewa za a inganta yanayin kasuwancin a ƙasar tare da fatan nasararsu za ta yi kyakkyawan tasiri a kan 'yan ƙasar.

Ƙalubalen rarrabawa

Rashin isassun wuraren sayar da gas ɗin da ake amfani da shi a ababen hawa na CNG a Nijeriya na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da za a fuskanta wajen musayarsa da fetur a wajen amfani.

Duba da wannan matsala ne ya sa masu sayar da ababen hawa a ƙasar suke yi wa motocinsu dabara ta hanyar bai wa masu saye damar amfani da ko dai fetur ko gas a jikinta.

"Muna sayar da bas-bas da kuma ƙananan motoci da suke amfani da CNG da kuma fetur," kamar yadda Okorie Ifeanyi mai kamfanin sayar da motoci na Kojo Motors Ltd ya shaida wa TRT Afrika.

'Yan Nijeriya na ta jiran motocin bas masu amfani da CNG da Shugaban Ƙasa ya yi alkawari. Hoto/ Reuters

"Idan CNG ya ƙare wa abin hawan kuma babu wajen sayar da shi mafi kusa, to mutum na iya mayar da motar yanayin da za a saka mata fetur," in ji Ifeanyi.

Gwamnati tana shirin ƙara lokacin ɗage karɓar haraji da cire tallafi don ƙara wa mutane ƙwarin gwiwar mayar da tsofaffin motocinsu yanayin da za a iya dinga saka musu CNG.

"Muna samar da wuraren mayar da ababen hawa kan wannan tsari a fadin ƙasar. Muna fatan ci gaba da samar da wannan tsari a farashi mai rangwame da kuma tsarin biya wanda zai bai wa mutane damar dinga biya da kaɗa-kaɗan," a cewar Michael Oluwagbemi, daraktan Shirin Samar da CNG na Fadar Shugaban Ƙasa (Pi-CNG).

Gwamnatin na burin samar da wuraren mayar da ababen hawa kan tsarin CNG guda 100 da kuma wajen sayensa guda 60 a jihohi 18 zuwa nan da shekarar 2024. Za a mayar da hankali ne kan sufurin jama'a.

Ribar ƙarancin fitar da iska

Wani burin shirin shi ne rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli a ƙasar.

Ana fatan wannan sabuwar manufar zata amfani tattalin arzikin Nijeriya: Hoto/Reuters

"Motocin da ke amfani da iskar gas sun kai kashi 40 cikin 100 na hayakin da ake fitarwa idan aka kwatanta da masu amfani da man fetur ko dizal. Yunkurin da Nijeriya ta yi na bin wannan turbar zai ba ta damar cika alkawuran da kasar ta dauka a karkashin yarjejeniyar yanayi ta Paris, wadda muka sanya hannu a kai," in ji Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan sadarwa da dabaru.

An riga an tsara ƙa'idar aminci tare da ƙa'idoji 80 waɗanda dole ne duk masu ruwa da tsaki su bi su.

Kamar yadda aka bayyana a shafin intanet na Pi-CNG, makasudin samar da wannan tsari ba wai don riba ba ne, sai don sauƙaƙa wa mutane wahalhalun da cire tallafin man fetur ya jawo.

TRT Afrika