Aikin ungozoma na taimakon mata wajen haihuwa, aiki ne da ya samo asali tun shekaru aru-aru. Rubuce-rubucen tarihi sun nuna yadda aka rika amfani da hikimomi wajen karbar haihuwa a dalolin Masar da Byzantium da Mesopotamia da daular Mediterranean ta kasar Girka da Daular Rumawa.
Masu aikin a lokacin suna amfani da wasu ganyayyaki da sauyoyi a matsayin magani wajen karbar haihuwar.
Ana matukar girmamawa irin wadannan matan tun a wancan lokacin saboda hikimarsu da tausayinsu. Aikinsu na agaji ne domin taimakon al'umma. Kamar yadda wani likitan Faransa Robert Debre ya bayyana, "yaranmu su ne rayuwarmu."
A kasar Benin da ke yankin Afirka maso Yamma, Annick Nonohou, wata ungozoma wadda asali ta fara karatun lauya, ta kuduri aniyar yaki da matsalolin haihuwa wadanda sakaci da wulakancin masu aikin ungozoma suke jawowa da wata gidauniyar da ta assasa.
Matsalolin kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana, su ne matsalolin da masu aikin ungozoma suka jawo wa mata wajen haihuwa ko mata masu juna biyu."
Annick ta assasa Gidauniyar RSAP a Jamhuriyar Benin domin yaki da irin wadannan matsalolin ta hanyar wayar da kan mata masu juna biyu da masu aikin karbar haihuwa a kan hanyoyin samun haihuwa cikin sauki.
"Muna so mu fayyace hakkin mai haihuwa da kokarin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta wajen haihuwa domin inganta hanyoyin haihuwa domin kiyaye yawan mace-macen mata masu juna biyu da yaransu a kasarmu," inji Annick a tattaunawarta da TRT Afrika.
Samun horo daga Maroko
Gidauniyar Réseau des soignants amis des patients, ko kuma RSAP a takaice ta samo asali ne daga wani kwas da Annick ta je a shekarar 2012 a kasar Maroko.
Sai ta hada hannu wata kawarta ungozoma Émilienne Badou Adjobo, domin dabbaka abin da suka koyo daga kasar ta Maroko na taimakon mata da kare su daga shiga matsaloli a lokacin haihuwa.
"A kwas din ne muka koyo yadda ungozoma suke aiki a Maroko wajen kare mata shiga matsaloli a lokacin haihuwa, da kuma yadda suka samu nasarar rage yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da jariransu da kaso 50 a cikin shekara goma (2001-2011).
Sun samu wannan nasarar ce ta hanyar wayar da kan mata," inji Annick mai shekara 40. Abin da ya kara jan hankalinta shi ne hadin kan da suke da shi a can Marokon, wanda ya taimaka musu wajen saukin samun nasara.
A gida Benin kuwa, Anita da abokan aikinta, ciki har da Émilienne suna ta kokarin samun nasara, wanda hakan ya sa suka bude ofishin gidauniyar a gundumar Tankpè da ke Abomey-Calavi.
Ofishin ne ya zama hedkwatar RSAP Benin. Suna wayar da kan mata a ofishinsu, sannan wasu lokutan sukan bi mata gidajensu domin wayar musu da kai. "Idan mun fita zagaye, muna ilimantar da mata ne a kan abubuwan da suke kawo matsala da kuma sanin hakkokinsu.
Su kuma masu aikin karbar haihuwa da sauran al'umma da iyalai muna ilimantar da su irin cigaban da aka samu a bangaren haihuwa," inji Annick.
Masu aikin kiwon lafiya ma suna karuwa daga horo da gidauniyar ke ba su a kan dokokin da harkokin da suke tattare da matsalolin masu aikin karbar haihuwa sukan jefa mata a ciki, domin su rika saka tausayi da lura da harkokin masu haihuwar a lokacin aikinsu.
Tashin hankalin mai juna biyu
Bangaren shari'a da Annick ta fara karanta ya taimaka mata wajen sanin dokoki da kwarewa wajen wayar da kan mat
A lokacin da take tasowa, ta ga yadda mahaifiyarta ta sha fama da matsaloli wajen haihuwa.
Tun a lokacin ne Annick ta kuduri aniyar kawo sauyi a bangaren domin ganin sakaci da wulakancin masu karbar haihuwa bai zama matsala ba sama da haihuwar.
"Ni kaina na fuskanci irin wannan matsalar lokacin da zan haifa dana na farko. Na san irin wulakancin da mata suke fuskanta a asibitoci, wadanda a wasu lokutan suke sanadiyar mutuwarsu," inji ta.
Aikin agaji da take daukar nauyi
Bayan dawowarta daga Maroko, sai ta yi amfani da 'yan kudadenta wajen assasa gidauniyar, wadda yanzu ta fara kawo sauyi a kasar.
A cikin shekara goma da suka gabata, Annick tana ajiye wani kaso na albashinta a duk wata domin ganin gidauniyar ta samu nasara.
Sannan sukan samu wasu 'yan kudade kalilan daga wadanda suka samun horo, wanda kudaden ma na taimakawa wajen dawainiyar tafiyar da gidauniyar.
"Muna ilimantar da mata masu juna biyu hakkinsu na neman a girmama su da ba su kula da walwala. Muna ilimantar da su muhimmancin fitowa fili su bayyana damuwarsu domin kare shiga matsala a sanadiyar sakaci ko wulakancin masu ungozoma," kamar yadda Annick ta bayyana wa TRT Afrika.
Ana amfani da kwatancen yadda ake daukar ciki da laulayin da ke biyo baya domin koyar da mata da kuma ungozoma yadda lamarin yake a aikace.
"Muna da rigunan da aka tsara da suke nuna yanayin yadda halittar ciki take domin maza su ga yadda lamarin yake domin ilimantar da su muhimmancin taimakon matansu da aikace-aikacen gida a lokacin da suke cikin laulayi.
"Wannan yana kuma tamkawa wajen mazantaka na kwarai," inji Annick. Gidauniyar RSAP tana kuma kokarin jawo hankalin 'yan majalisar kasar domin samar da dokar da za ta kare hakkin mata masu juna biyu a lokacin haihuwa.
Wani bincike da Asusun Kidaya na Majalisar Dinkin Duniya ya yi a shekarar 2015 ya gano cewa kusan kashi 45 na mutuwar yara 'yan kasa da shekara biyar a kasashen Afirka maso tasowa yana faruwa ne a tsakanin jarirai.
Mafi yawan wadannan mace-macen suna faruwa ne a makon farko na haihuwa. Daga ciki kuma kashi 25 zuwa 45 suna aukuwa ne a kasa da awa 24.
Binciken na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa yawancin mace-macen nan suna faruwa ne a kasashe maso tasowa, inda ake fama da matsalolin rashin ingantaccen kiwon lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana rashin kwarewa wajen taimakon mata masu juna biyu da rashin kayan aiki a matsayin manyan abubuwan da suke jawo matsalar.
Annick, wadda ta ga akalla matsalolin haihuwa da sakaci da rashin kula na masu aikin ungozoma suka jawo guda 5,000 zuwa yanzu, ta kuduri aniyar yaki da matsalar duk runtsi duk wahala.