Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu (daga hagu) da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa lokacin ganawar su a Cape Town. / Hoto: Reuters

Daga Emmanuel Onyango

Ana ta mhawara da cece-ku-ce kan sanarwar da Afirka ta Kudu ta fitar na saukaka sharuddan Visa ga 'yan Nijeriya da ke shirin ziyartar kasar don yawon bude ido da kasuwanci.

Shugaba Cyril Ramaphosa ne ya fitar da sanarwar hakan a lokacin da ya karbi bakuncn talwaransa na Nijeriya, Bola Tinubu, a makon da ya gabata don tattauna wa kan habaka alakarsu.

Rikici tsakanin 'yan kasashen biyu a baya ya janyo hare-haren nuna tsana ga 'yan kasashen waje a kasashen biyu - inda aka kai hari kan wuraren kasuwanci tare da sace dukiyoyi.

Nijeriya ce babbar cibiyar kasuwanci da zuba jarin 'yan Afirka ta Kudu a Yammacin Afirka. A gefe guda kuma, Afirka ta Kudu na sayen mai da gas daga Nijeriya.

Tattalin arzikin Afirka ta Kudu ba ya habaka yadda ya kamata, ta yadda zai tallafi yawan jama'ar kasar da ke daduwa, kuma kasar na fama da rashin ayyukan yi, inda ya kai kashi 30, kamar yadda alkaluman Bankin Duniya da Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa suka bayyana a watan Yunin 2024.

Nijeriya ma na fama da kalubalen tattalin arziki inda 'yan kasar da dama ke tafiya kasashen ketare saboda rashin ayyukan yi.

Hakan ya sa babu mamaki cewa Ramaphosa, tare da niyyar janyo hankalin kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, ya fada wa Tinubu sauyi a sharuddan bayar da Visa, ciki har da kara wa'adin Visar kasuwanci ga 'yan kasuwar Nijeriya da kuma saukaka sharuddan.

Kamfanin sadarwa na MTN mallakin Afirka ta Kudu na daga manyan kamfanonin da ke kasuwanci a Nijeriya. Hoto / Reuters

"Muna sauraron ganin kamfanonin Nijeriya sun zuba jari a Afirka ta Kudu. Tabbas, muna son ganin kayan Nijeriya a kantocin shagunan Afirka ta Kudu...

'Yan kasuwar Nijeriya da suka cancanta na iya karbar Visa ta shekaru biya da za su dinga shuga kasar a duk lokaci da suka gaba dama." in ji shi.

“Kazalika, 'yan yawon bude ido daga Njeriyaa yanzu za su iya neman visa ba tare da mika fasfo din su ba," Ramaphosa ya bayyana.

Takwaransa na Nijeriya Bola Tinubu ya kira Afirka ta Kudu da sunan "Babbar 'yar uwa gare mu" da kuma yabon wannan yunkuri a matsayin "dalilin 'yan uwantaka".

Afirka ta Kudu na karbar bakuncin 'yan gudun hijira miliyan 2.3, kusan kashi uku na al'ummar kasar.

Wasu 'yan Afirka ta Kudu na cewa 'yan kasashen waje, da suka hada da 'yan Nijeriya, na kwace ayyukan 'yan kasa.

Mahukunta na ci gaba da bayar da tabbaci ga 'yan kasa na za a samar da karin damarnakin tattalin arziki, suna kuma bayyana musu alfanun samun masu zuba jari na kasashen waje da 'yan yawan bude ga jama'ar yankunan.

Sanarwar Ramaphosa ta sassauta sharuddan bayar da visar Afirka ta Kudu ga 'yan Nijeriya ya bakanta wa wasu 'yan Afirka ta Kudun.

Ana kallon hakan ya saba wa alkawarin da gwamnatin ta yi na magance gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Da yawa sun bayyana rashin jin dadinsu a shafukan sada zumunta kan yadda 'yan yawon bude ido daga Nijeriya ba sa bukatar bayar da fasfo din su don karbar Visa din zuwa Afirka ta Kudu.

Ofishin shugaban kasar ya yi wuf wajen fayyace wannan rashin fahimta ta saukaka sharuddan visa ga 'yan Nijeriya.

Bankin Acccess na Nijeriya na daya daga manyan masu taka rawar gani a Afirka ta Kudu. Hoto / Reuters

Sanarwar ta ce maziyarta daga Nijeriya za su bayar da fasfon su a matakan karshe na karbar Visa din.

"Zamantar da tsarin neman biza ba ya raunata tsari da kimar visar." in ji sanarwar.

"Da zarar an amince a neman biza, sannan ne za a bukaci su mika fasfo din su don kammala ba su visa din, wadda za a lika a jikin fasfon."

Wasu masu nazari sun ce matakin na Afirka ta kudu na da kyau a yayin da nahiyar ke ci gaba da kokarin saukaka kai komo tsakanin kasashenta da inganta yarjeniyoyin kasuwanci.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka na kasa da kashi 16 kuma a wani rahoton Tarayyar Afirka na baya-bayan nan an soki yadda kan halayyar kasashen Afirka na baiwa 'yan nahiyar damar shiga kasashensu.

Dan kasuwar Nijeriya Aliko Dangote da ya fi kowa a nahiyar, a baya ya bayyana yadda ake shan wahalar tafiya da fasfon Nijeriya a cikin nahiyar.

"A matsayin mai zuba jari, a matsayin wanda ke son habaka Afirka ta zama mai karfi, a yanzu ya zamar min wajibi na nemi visa 35 a kan fasfo di na.

Ba ni da lokacin zuwa ofisoshin jakadancin wadannan kasashe don karbar biza," ya fada wa wani taron kasuwanci na Afirka da aka yi a watan Satumba.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a watan Janairun 2024 ya kaddamar da daukar kaya a jirgin ruwa a karon farko karkashin yarjejeniyar (AfCFTA). Hoto /AFP

Tarayyar Afirka na matsa lamba ga mambobinta da su samar da tsarin saukaka zirga-zirga a tsakaninsu don saukaka kasuwanci a fadin nahiyar.

A watan Janairusn 2021 a kaddamar da Yarjejeniyar Kasuwanci Mara shinge ta Nahiyar Afirka (AfCTA) da manufar samar da yankin kasuwanci mafi girma a duniya da mutane biliyan 1.2.

Sai dai kuma, bayanin da aka samu a rahoton bayar da visa ya nuna cewa nahiyar na da aiki a gabanta. Benin, Rwanda, Gambia da Seychelles kadai ne suka bayar da damar shiga kasashen ga dukkan 'yan kasashen Afirka ba tare da Visa ba.

"Kasashe da dama sun yi shiru... Akwai aiki mai yawa a gaban Afirka, kuma akwai babban aiki kan batun visa," in ji Minata Samate Cessouma, Kwamishinar Tarayyar Afirka kan harkokin Jinkai.

TRT Afrika