Ilimi yana samar wa yara mata hanyoyin da suke bukata wajen yanke shawara mai kyau da zata amfani rayuwarsu / Photo: Reuters

Daga Shamsiyya Hamza

Al'adar yi wa ƴaƴa mata auren wuri ba sabon abu ba ne a yankuna da dama a fadin duniya, musamman yankin Afirka, lamarin da a lokuta da dama kan hana mata samun ilimi da kuma damar kai wa wani matsayin ci gaba a rayuwa.

Duk da wannan kalubalen, Ramatu Haruna ‘yar shekara 16, wacce ta fito daga kauyen Ganjarma da ke jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Nijeriyya ta nuna ƙwazo da jajircewarta wajen neman ilimi da ya sa ta fita daban daga cikin sauran 'yan mata masu irin shakarunta da ake yi auren wuri musamman a yankinta.

A wata tattaunawa ta musamman da TRT Afirka Hausa ta yi da Ramatu, albarkacin Ranar Yara Mata ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 11 ga watan Oktoban kowace shekara, matashiyar ta bayyana cewa ita ce mace ta farko da ta kammala karatun sakandare daga ƙauyensu, kuma tana da burin ci gaba.

''Mu shida mahaifiyata ta haifa amma ƴaƴan babana 13 ne, ni kaɗai ce daga cikinsu na kammala karatun sakandare, ba ƙaramar gwagwarmaya mahaifiyata ta yi ba wajen ganin na kai wannan matakin, da kuɗin tallan da nake yi mata ta biya mun kudin littattafai da sauran abubuwan da nake bukata a makaranta'' in ji Ramatu.

Cika burina

A cewarta ''Yawancin yara mata da aka yi wa aure a ƙauyenmu ba su taɓa zuwa makaranta ba, wasu kuma ba su wuce makarantar firamare ba aka musu aure, kusan ni kaɗai ce na bijire wannan al'ada a garinmu, domin bayan na gama firamare babana ya ce za a yi min aure, don ya aurar da duk sauran ƴan'uwana mata ne bayan sun kammala karatunsu na firamare.''

Na nuna ba na so saboda irin matsalolin da na ga yawancin mata har da ƴan'uwa da aka yi musu aure suke fuskanta. Da taimakon Allah da kuma mahaifiyata wacce ta tura ni wajen ƴar'uwarta da ke cikin garin Damaturu na ci gaba da karatuna har na kai wannan matsayi,'' in ji ta.

Ramatu ba ta da burin da ya wuce na zama likita domin ta taimaki al'umma musamman a yankin inda ta fito, "don muna ƙarancin ma'aikatan lafiya."

Auren wuri na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar yankin arewacin Nijeriya, sakamakon irin tarnakin da hakan ke haifawa ga samun ilimin yara mata da kiwon lafiyarsu da kuma hanyoyin ci gabansu baki daya.

IIlar auren Wuri

A wani ƙiyasi da Asusun Kula da Ƙananan Yara na MDD, UNICEF ya fitar a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2020, kashi 16 cikin 100 na yaran da aka yi wa auren wuri a Nijeriya ƴan shekara 15 ne, yayin da kashi 43 cikin 100 aka yi musu aure kafin su cika shekara 18.

A 2022 an yi wa yara mata miliyan 12 wadanda ƴan shekara kasa da 18 aure a duniya a cewar UNICEF.

A wasu lokuta auren wuri na janyo datsewar karatun yara mata tare da hana su kai wa ga samun damarmakin da za su kai su ga samun duk wani ci gaba a rayuwarsu.

Kazalika akwai yiwuwar su fada cikin hadarin fuskantar matsalolin kiwon lafiya a yayin da suka ɗauki ciki sakamakon yanayin rashin girman wasu gaɓoɓin jikinsu.

Muhimmacin ilimi ga yara mata

Wata mai fafutukar kare hakkin yara mata a Nijeriyya, Ummulkhairi Abdulmumini iliyasu ta ce "Ilimi yana bai wa yara mata damar yanke shawarar da ta dace a kan rayuwarsu da kuma hanyar kula da lafiyarsu.

"Sannan za su samu abun da za su iya dogaro da shi don kawar da talaucin da ke damun al'ummarmu,'' a cewarta.

TRT Afrika