Daga Gaure Mdee da Charles Mgbolu
Wasan damben zamani da ake kira Mixed Martial Arts wato MMA a takaice da Turancin Ingilishi, wasa ne da ya kunshi doke-doke sosai da ke kara samun karbuwa a Nahiyar Afrika. Kasashe 19 na Afrika sun amince da wasan a cikin wasanninsu na kasa a hukumance.
Wannan wasan yana bukatar juriya sosai-saboda ya kunshi kwambe da dambe da kokuwa a hade.
Idan har kana da sha'awar kallon wasan, dole ka shirya gane wa idonka fada mai zafi da juriyar gaske.
Kasashen Kamaru da Zambia da Aljeriya da Tunisia da Ghana da Maroko da Masar suna cikin kasashen Afirka da aka amince da wasan a hukumance.
Ana tsammanin kara samun wasu zakarun gasar daga nahiyar, kamar yadda dan Najeriya, Usman Kamaru, wanda shi ne dan asalin nahiyar na farko da ya lashe Gasar ta duniya wato UFC a tarihi a watan Maris na shekarar 2019.
A shekarar kuma, wani dan Najeriyan mai suna Israel Adesanya ya sake lashe gasar ta 'yan ajin matsakaitin nauyi, duk da cewa a matsayin dan kasar New Zealand ya shiga gasar.
Tsohon dan boksin, dan asalin kasar Kamaru mazaunin Faransa mai suna Francis Ngannou, yana cikin masu taimakawa wajen kara bunkasa wasan a Afirka. Ya lashe gasar ajin mafi nauyi a shekarar 2021.
Amma daga martabar damben na zamani a gida Afirka domin ya yi gogayya da na duniya aiki ne babba da ke bukatar sadaukarwar jini, hawaye da zufa.
Wani dan damben dan kasar Tanzania mai suna Chris Tibenda ya ce rashin inganta wasan a kasashen Afrika da dama na jawo cikas ga ci gaban wasan a nahiyar.
"Muna da yan dambe, muna da 'yan kwambe da masu kokawa kwararru matuka, amma ba su samun damar inganta kwarewarsu domin nuna kwanjinsu a duniya," in ji Tibenda a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Haka kuma akwai rashin gasanni, wanda shi ma yana taimakawa wajen hana wasan ci gaba.
“A duk yan damben da muke da su a Afrika, misali a Najeriya babu wanda ya taba fafata fada ya kai sau bakwai," in ji Henry George, wanda shi ne Shugaban MMA din a Najeriya a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Amma 'yan damben na cikin gida suna ta hankoron daga darajar gasar zuwa idon duniya.
"Mutane da dama ba su da masaniyar cewa akwai kungiyoyin wasan MMA a nan, amma kasancewar mun fara nuna kanmu, yanzu mutane suna ta kara shigowa," in ji Tibenda.
Misali, a Ghana akwai kungiyar Wushu Martial Arts Association of Ghana.
Gabashin Afrika akwai gasar kamar ta 1 Zone, inda yan dambe masu tasowa irin su Chris Tibenda na Tanzaniya da Rebecca Amongi suke nuna bajintarsu.
Wata gasar ta 'yan ajin mafi nauyi ita ce ta Impact Championship da ake yi a DRC, wanda ta fara zama matattar yan damben Gabashin Afrika.
"Muna cikin kasashen Afrika na farko-farko tare da Afirka ta Kudu da suka fara wasan a hukumance. Yanzu matasa da dama a nan kasar ta DRC na shiga gasar sama da wasu kasashen yankin," in ji Adam Mozer.
"Akwai kungiyoyi 25 na damben a duniya, inda akwai jimillar matasa 1000 a kungiyoyi daban-daban, sannan gwamnati ta amince da wasan," in ji shi.
A shekarar 2022, sama da yan dambe 20 daga kasashen Afrika da dama ne suka hadu a birnin Windhoek domin fafata gasar damben na zamani na farko a kasar Namibia.
A Afirka ta Kudu, ana samun yan damben daga kasashen duniya irin su Scotland da Faransa da Jamus da suke shigowa.
Harin mamayar zubar da jini
Chris Tibenda, wanda yana daya daga cikin na gaba-gaban yan damben a Tanzania ya fara wasan ne bayan harin da aka kawo masa.
"Dalilin da na fara wasan nan shi wani harin mamaya da aka kawo min. Watarana ina tafiya tare da yar uwata, kawai ban yi aune ba, sai na ji duka, inda na samu raunuka. Tun daga ranar ce na fara shirya kare kaina, kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika.
Wani masanin wasan na MMA, ya ce kada nahiyar ta fi mayar da hankali a kan shiga gasannin duniya kadai, yana da kyau ta kara kaimi wajen bunkasa nata na gida.
"Burina shi ne mu bunkasa wasan. Idan ana maganar bunkasa wasan, akwai bukatar samun masu horo na gasar. Ni a tunanina kusan kashi 80 zuwa 90 na masu horar da 'yan damben na zamani ba asalin 'yan damben na zamani ba ne, yawanci asalinsu 'yan wasu wasannin ne irin kwambe da sauransu. Ka ga ai ba su kwarewa sosai a wasan na MMA," in ji Ambasada Henry George.
"Burina in samu nasarori da dama domin jan hankalin matasa su shigo gasar saboda ko a yanzu, a sanadiyar wasan na kara sanin mutane da dama, na samu masoya sannan na kara fahimtar rayuwa. Ko ba komai na san yadda zan kare kaina da na kusa da ni," in ji Tibenda.