Me ya sa ziyarar da Sarki da Sarauniyar Holland za su kai Kenya ke tayar da ƙura?

Me ya sa ziyarar da Sarki da Sarauniyar Holland za su kai Kenya ke tayar da ƙura?

Masu suka a shafukan sada zumunta na matsa lamba ga basaraken na Holland da ya soke tafiyar.
Sarki Willem-Alexander (Dama) ya karbi bakuncin Shugaban Kasar Kenya William Ruto a Fadar Noordeinde a ke Hague a watan Mayun 2023 Hoto: Reuters

Daga Emmanuel Onyango

Jami'an Kenya sun bayyana cewa "kutse ta yanar gizo" da masu fada a ji a shafukan sada zumunta suka yi ne musabbabin kiraye-kirayen a dakatar da ziyarar da shugabannin masarautar Holland Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima suka shirya kai wa Kenya.

A shafukan sada zumunta a Kenya an dinga rubuta "#CancelTheVisit" (#SokeZIyarar) inda ake neman iyalan masarautar ta Hoilland da su soke ziyarar ta aiki. An kuma aika da sakon e-mail na adawa da ziyarar zuwa ga ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Holland, inda aka dinga yada hoton sakon a shafukan sada zumunta.

Gwamnatin Holland ta tabbatar da samun daruruwan sakonnin e-mail a kwanaki ukun da suka gabata, daga mutanen da adawa da ziyarar da sarki da sarauniya suka shirya kai wa Kenya, kamar yadda tashar talabijin ta kasar Nederlandse Omroep Stichting ta bayyana.

Masarautar ta Holland na fatan ziyarar za ta zama "mai karfafa kyakkyawar dangantaka da hadin kai" tsakanin kasashen biyu.

Zanga-Zanga a tituna

A Kenya, tun wtaan Yunin 2024 ake matsa lamba ga gwamnati, a lokacin da zanga-zanga ta barke a kan tituna inda matasa ke neman mahukunta da su rage yawan harajin da 'yan kasa ke biya tare da kyautata shugabanci.

Sannan an samu batan mutanen da ke sukar gwamnati, inda kungiyar masu ra'ayin rikau ke cewa a watan da ya gabata an samu batan mutane 82.

Ministan Ayyukan Jama'a na Kenya Justin Muturi, wanda dansa na cikin wadanda aka yi garkuwa da su a watan Yuni, ya ce shirun da gwmanati ta yi gae da batan mutane a baya-bayan nan ya sanya cire rai daga amincewa da jami'an tsaron kasar.

Masu zanga a Kenya lokacin zanga-zangar adawa da karin haraji a birnin Nairobi a ranar 20 ga Yunin 2020.

"Garkuwa da mutane da batan jama'a a Kenya ya zama babbar damuwar tsaro a baya-bayan nan, kuma wadanda lamarin ke shafa ba maza ne kawai ba, har da mata da yara kanana, da ma 'yan kasashen waje," in ji shugaba Ruto a Jawabin Kasa da ya yi a watan Nuwamban bara.

Kokonton jama'a

Sai dai kuma, kokarin gwamnati na kawar da bacin ran jama'a, cik har da alkawarin bincikar batan jama'a ta karfi da ya ji, ya fuskanci rashin gasgatawa. Masu suka a shafukan sada zumunta na sukar yadda gwamnati ke kulla alaka da kasashen Yammacin Duniya.

A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen Kenya ta ce ta damu da yadda 'ake yada bayanai da labaran da ke zubar da mutuncin gwamnati" a idanun kasashen duniya.

Ta ce "wasu 'yan tsirarun masu fada a ji shafukan sada zumunta" na neman "haramta ganin kokarin gwamnati da hana afkuwar ziyara mai muhimanci" tare da aika wa da abinda ta kira sakonnin barazana ga manyan biranen kasashen waje.

"Wadannan ayyuka na yanar gizo, mafi yawan su an samar da su ne da Kirkirarriyar Basira, labaran karya, gangamin yada bayanan da ba haka suke ba da aika sakon e-mail, ana tura su ga manyan biranen kasashen waje," in ji ma'aikatar a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Kenya ta tabbatar da "dukkan cibiyoyin diflomasiyya, hukumomin MDD da kungiyoyin kasa da kasa vewa a shrye take da ta tattauna duk wata damuwa ko karin bayani, kuma a shirye suke don gance wannan matsala."

Sarakunan Turai

Sarkin Ingila Charles ke karbar tarba daga Shugaban kasar Kenya William Ruto a Fadar Gwamnati da ke Nairobi a watan Oktoban 2023.

Ziyarar ta iyalan masarautar Holland da aka shirya yi a tsakanin 18 da 20 ga Maris, za ta zama ta biyu da shugaba Ruto yake karbar bakuncin bazarake daga Turai.

Sarkin Ingila Sharles da matarsa Camilla sun ziyarci kasar ta Gabashin Afirka a watan Oktoban 2023. 'Yan Kenya sun soki wannan ziyara ma saboda zaluncin da Ingila ta yi a lokacin mulkin mallaka a Kenya.

Tabon zaluncin tikicin Mau Mau da dakarun Ingila suka yi a 1950 kafin samun 'yancin kai har yanzu na nan sabo.

Wasu mambobin kungiyar tirjiya sun je Kotun Tarayyar Turai ta Kare Hakkokin Dan Adam don neman a dawo musu da dala biliyan 2.2 daga Ingila saboda ta'annatin da aka yi.

An shata layi tsakanin dambarwar shirin ziyarar iyalan masarautar Holland da ta Sarki Charles.

Sarki Charles ya furta "Munanan abubuwa na rashin kan gado da aka aikata wa 'yan Kenya" a lokacin da suke gwagwarmayar kwatar 'yancin kai, amma ya gaza neman afuwa a hukumance kamar yadda masu sukar suka nema.

Laifukan 'yan mulkin mallaka

Duk da Holland ba ta da tarihi na kai tsaye na mulkin mallaka a Kenya, masu sarautar na Holland na iya amfani da ziyarar, idan har aka yi ta, a matsayin dama ta tattaunawa game da batutuwa masu wahala da suka shafi laifukan kasashen Yamma a Afirka.

"Masu sarautar na iya amsa gayyatar, amma daga cikin batutuwan da suke sha'awar tattaunawa, za a iya samun halin shugabanci a Kenya," in ji Javas Bigambo, wani malamin Jami'a a Kenya kuma kwararre a harkokin kasa da kasa yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Sarauniyar Holland Maxima (Hagu) da Sarkin Holland Willem-Alexander (Dama) a lokacin ziyara zuwa Afirka ta Kudu a watan Oktoban 2023.

"Ba na tunanin hakan zai yi tasiri kan ko ya zo ko kar ya zo. Duk ya ta'allaka kan dalilin da zai sa ya zo din. Idan dalilin na da muhimmanci, to zai yi biris da su," Mcharia Munene, wani farfesa kan harkokin kasa da kasa a Kenya ya shaida wa TRT Afrika.

Duk da wasu masu nazari na da ra'ayi daban kan ra'ayin jama'a da son zuciyarsu a shafukan sada zumunta don dakatar da masarautan na Holland kai ziyarar, suna cewa wannan rashin amincewa na aike wa da babban sako.

TRT Afrika