Tsawon lokaci 'yan wasannin Afirka da ke da sunayen gargajiya na fuskantar kunar zuci saboda yadda ake furta sunayensu da kuskure kuma ta hanyar cin fuska. / Hoto: Reuters

Daga Dayo Yusuf

Lakabi a al'adun Yammacin duniya irin su "Bob, Ben da Billy" manyan alamu ne da suka shahara wajen furta sunaye ba daidai ba.

Tsawon lokaci 'yan wasannin Afirka da ke da sunayen gargajiya na fuskantar kunar zuci saboda yadda ake furta sunayensu da kuskure kuma ta hanyar cin fuska.

Ku yi tunani a ce kai ma'abocin wasa ne da kake wakiltar kasarka a babbar gasa, kuma ka ji mai gabatarwa na furta sunanka da ba ka san da shi ba.

Ferdinand Omanyala, dan Afirka da ya fi kow agudu, ya san abinda ake ji. A wajen gasar Olympics da aka kammala kwanan nan a Paris, wani mai sharhi ya ci fuskar sunan dan tseren kasar Kenya d aya kafa tarihi inda ya fadi sunan da ma bai yi kama da nasa ba.

A wannan karon, lamarin ya janyo korafi. Kafafan sadarwa na sada zumunta a Kenya sun fusata tun bayan wannan abu, suna bayyana bacin ransu kan abinda suka kira rashin girmamawa, girman kaida hassada.

Watakila Omanyala na iya zama mai sarkakiya a harshe ga wadanda ba su saba fadar sunan ba, amma wannan ba shi ne dan Afirka na farko da ake furta sunansa ba daidai ba a bainar jama'a.

Babban abin da ke akwai shi ne matukar mutum ba shi da sunan Yammacin duniya, sai a mayar da shi kamar sunan wani daban a bakin Turawan Ingilishi. / Hoto : X- Shola Shoretire

"Akwai wani dan kwallon kafa dan asalin Nijeriya mai suna Shola Shoretire, wanda a baya yake taka leda a kungiyar Manchester United. Amma sai suke kiran sa da Show-taya, kuma babu wanda ya yi yunkurin ya gyara hakan." in ji mai sharhin harkokin wasanni Mohammed Mowiz a tattaunawarsa da TRT Afirka.

'Wannan ya sha faruwa tsawon lokaci kuma zai ci gaba matukar ba a dauki wani mataki a kan sa ba."

Babban abin da ke akwai shi ne matukar mutum ba shi da sunan Yammacin duniya, sai a mayar da shi kamar sunan wani daban a bakin Turawan Ingilishi.

Dakatar da masu aikata kuskuren

Ba kowa ne ya shirya amincewa d ayafe yadda ake cin fuskar furta sunansa ba, musamman idan kwararru a wani fannin sana'a suka aikata hakan. Wasu na kallon furta suna ba daidai ba a matsayin abu na gangan ko da wata manufa ta muzantawa ko rashin girmamawa.

"A tare da 'yan yammacin duniya. Ina tunanin batu ne na jin su sun fi kowa, ko kuma kawai babu ruwan su," in ji Mowiz.

A yadda irin wannan kuskure ya zama ruwan dare, abin ya fi bata rai idan ka ji wanda dan asalin kasar da sunan ya fito ne ya yi shi. Ana dora wa masu sharhin wasannin motsa jiki laifin kin koyon yadda ake furta ko kuma ma'anar sunayen 'yan wasa.

A cikin al'ummu, ana yin zurfin tunani wajen baiwa yara suna. Son rai na taka rawa sosai, kuma sunan da ake zaba na iya samun ma'ana boyayyiya da ba kowa ne zai iya gano ta ba.

Ana saka wa wasu yaran sunayen mashahuran mutane ko kuma wasu da suka yi tasiri a cikin danginsu.

Wasu kuma na samun sunan makusantansu, da suka mutu ko wadanda suke raye, da ma mashahuran mutane. An san iyaye da baiwa yaransu sunan wani tare da fatan ya yi halin mai wannan sunan.

'Babban abin kunya'

A dukkan sunayen da ake furta wa ba daidai ba a duniya, na 'yan Afirka ne suka fi munana.

Mowiz ya ce "Idan mutum kwararren ne a harkokin wasanni, misali, ya kamata su nemi hanyoyin koyon yadda ake furta sunayen daidai."

Masu gabatarwa da sharhi a wasu lokutan na tambayar yadda ake furta sunayen 'yan wasa. / Hoto: Reuters

"Dan Afirka mai saukin kai bai damu da yadda za ka furta sunansa ba, ko ma yaya ne ba ya nuna damuwa."

Akwai togajiya amma. A gasar Zakarun Ingila ta Premier League, ana kiran 'yan wasa da su fadi sunayensu da karfi ta yadda kowa zai ji, hakan zai sa a dinga furta su yadda suke.

Masu gabatarwa da sharhi a wasu lokutan na tambayar yadda ake furta sunayen 'yan wasa.

"Ina jin rashin daji da kunya a lokacin da na kasa fadin sunan wani dan wasa daidai. Ina tambaya, don tabbatar da na koyi yadda ake furta sunan wannan mutumin a yaren kasarsa," in ji Mowiz.

"Aiki a matsayin mai gabatarwa ko sharhin wasanni, wani abu da za ka yi ta haduwa da shi, shi ne sabbin sunayen da ba ka taba ji ba. Idan ba ka shirya ba, za ka iya haduwar ba zata da suna a yayin gabatar da shiri kai tsaye. Wannan ne lokaci mafi muni. Sai a kacalcala sunan."

Sunaye irin su Santi Carzola, dan asalin kasar Spaniya da ya taba taka leda a kungiyar Arsenal ta gasar Premier, tsohon dan wasa gaba na Togo Emmanuel Adebayor, ko tsohon dan wasan Nijeriya Nwanko Kanu, duk an dinga furta sunayensu ba daidai ba a lokuta daban-daban.

A harkokin wasanni, 'yan kenya da suka lashe kambi, suna a duniya da sauran kyaututtuka na musamman, irin su mai gudun banfalaki Patrick Cherotich, da Omanyala sun zama wadanda da yawan masu shurhi da gabatarwa na Yammacin duniya suke shan wahalar firta sunayensu.

"Ina tunanin mafi yawan 'yan wasan ba su damu ba. Suna mayar da hankali kan wasanninsu kawai kuma da wahala su saurari sharhin da aka yi, to ba su damu da me ake yi ba. Amma hakan ba ya nufin an amince da furta sunayen ba daidai ba," in ji Mowiz.

TRT Afrika