Daga Abdulwasiu Hassan
Ku yi tunani a ce babbar hanyar da ababen hawa ke bi farat daya ta rikice da faduwar tankokin dakon mai.
Motar da ke dauke da lita 45,000 na man fetur, ta fadi a kan kwalta, tartsatsin wuta ya tashi a yayin da karfe ya gogi kwalta.
Wasu da ke kusa da wajen sun je wajen da gudu, suna gaggawar diban man da ya zube kasa.
A cikin kankanin lokaci, fashewar ta yi karfi tare da girmama, bakin hayaki ya tirnike sama.
Dan Nijeriya, Magaji Saidu ya san gaskiya mene ne haka. Yana jin takaicin abinda ya faru har cikin cikinsa, a yayin da yake tuna wa da mummunan ibtila'in da idanuwansa suka shaida da karfe 11 na daren ranar 15 ga Oktoban shekarar 2024.
"Ganin mutanen da ka sani da makusantanka na konewa a cikin wuta suna ihu suna neman taimako a yayin da muke tsaye daga nesa - wannan abu ne mai matukar kona zuciya." Magaji ya fada wa TRT Afrika game da tankar da ta fashe a Majiya, Jihar Jigawa.
Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna dandazon jama'a a kusa da tankar, suna amfani da bokitai suna diban mai da ya zube a kasa.
Magaji ya bayyana yadda ya girgiza da ganin fashewar, tare da fitowa daga gida ya ga abokai da 'yan uwa na ci da wuta.
Wutar ta kashe sama da mutane 200 tare da jikkata wasu da dama, wadanda wasun su har yanzu suna asibiti.

Sama da watanni uku bayan hatsarin, Mahaji na jin zuciyarsa na bugawa sosai, yana kuma jin hayaniyar da ta afku a lokacin da gobarar ta kama a kan titin.
Ibtila'in da ke yawan afkuwa
Ana yawan bayar da rahotannin fashewar tankokin mai da hatsarin mota ke janyowa.
A watan Satumban bara, tankar dakon mai ta yi taho mu gama da motar akori kura dauke da fasinjoji da shanu a Jihar Niger inda mutane 59 suka mutu.
A ranar 18 ga Janairu, wani hatsarin ya sake afkuwa a Jihar Niger, inda aka samu asarar rayuka kusan 100 bayan fashewar tankar mai kuma jama'a suka je diban man da ya zube kasa a motar da ke dauke da lita 60,000.
Kimanin mako gida baya haka, Jihar Enugu da ke kudu maso-gabashin Nijeriya ta yi makokin mutane mutane 20 a hatsarin motar dakon mai da ta kauce daga kan hanya tare da kama wa da wuta.
A 'yan watannin da suka gabata an samu asarar rayuka sama 300 sakamakon fashewar tankokin dakon man fetur a Nijeriya.
Alkaluman kamfanin dillancin labarai na Anadolu sun bayyana mutuwar mutane 1,896 daga 2009 zuwa yau sakamakon hatsarin tankar mai 172 d ya afku - ban da na Enugu da mutane 20 suka mutu.
Tambayoyin da aka gaza amsawa
Yawan fashewar tankokin man fetur da mutuwar 2,000 a shekaru 16 da suka gabata ya janyo tambayar ko har yanzu ba a dauki matakan kariya ba.

"Wasu 'yan dalilai ne suka zama musabbabin yawaitar hatsarin manyan motoci da ke janyo zurarar mai," George Ene-Ita, daraktan harkokin jama'a a Hukumar Kula da Dokoki a Fannin Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ya fada wa TRT Afrika.
Hukumar da ke kula da dakon man fetur a Nijeriya, ta lissafo tukin ganganci da jahiltar dokokin hanya, rashin kyawun wasu hanyoyinmu, da mummunan yanayin da wasu tankokin ke ciki, a matsayin dalilan da ke janyo wadannan hadurra.
Bayan afkuwr kowanne hadari irin haka, mahukunta na fada wa jama'a su kula.
"A yayin da mai yake zurara daga tankar da ta tintsire, ya zama dole nan da nan jama'a su dauki alhakin kiran jami'an tsaro da masu kashe gobara, kamar jami'an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayyar, 'yan sanda ko mahukuntan yankin," in ji Ene-Ita.
"Za su tabbatar da sun kewaye wajen da hatsarin ya afku don hana mutane yunkurin cewa za su dibi mai."
Tsarin shimfida bututu
A yayin da kasar da take ta farko a Afirka da ke fitar da mai ke ci gaba a inganta karfin tace mai, kwararru na bayar da shawarar a mayar da hankali ga wasu hanyoyin na dakon mai a fadin kasar.

Nijeriya ana akalla bututun da ake dakon mai da shi mai nisan kilomita 5,000 a fadin kasar.
"Abin takaici, mafi yawan bututunmu na fuskantar barnatarwa daga wasu mutane bata-gari," in ji Ene-Ita.
A shekarar da ta gabata, Mele Kyari, shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC ya ce cikin shekaru uku za su maye grbin dukkan bututun man da ke kasar.
"Bututu ne abu mafi inganci da kyau wajen dakon albarkatun mai," in ji Kyari. "Wannan ne ya sanya NNPC suka hade dukkan kusan yankunan kasar, tare da tashoshi 27 kuma da bututu mai tsayin sama da kilomita 5,000."
Amma a lokacin da Nijeriya ke jiran a sake bututun man ta, kwararru sun yi amanna da cewa gwamnati na bukatar inganta suran hanyoyin sufuri domin magance hatsarin tankokin man.
Ene-Ita na fatan kokarin gwamnatin Nijeriya za ta zuba jari wajen sake gina hanyoyi, gyara su, cigaban layin dogo, da kuma hukumomin kiyaye hadurra su ci gaba da wayar da kan direbobin manyan motoci don kawar da hatsarin.

Hukumar NMDPRA za ta karfafa ayyukanta na wayar da kai ta yadda mutane za su gano hatsarin kwasar mai idan ya zube daga motar dako da ta fadi.
"Dole ne mu sake duba dokokinmu da tabbatar da kamfanonin sayar da man fetur sun zuba jari wajen harkokin dakon mai a fadin kasar," in ji Ene-Ita.
Irin su Magaji da suka shaida kai tsaye yadda fashewar tanka ta kashe da jikkata mutane, za su yi fatan kokarin da mahukunta ke yi zai tsaftace dakon mai ga kowa.