Shirin ''From Brink'' ya mayar da hankali ne kan hanyoyin fahimtar damuwa da kuma ƙarfafa mutane su nemi taimako damuwar da suka taba fuskanta a baya. / Hoto: EAI Nigeria  

Daga Mazhun Idris

A rayuwar rubuce-rubucensa, fitattacen marubuci a ƙarni na 19 daga Rasha Fyodor Dostoevsky ya yi zurfi cikin rubuce-rubuce kan abubuwan da suka shafi zautuwa wato "trauma" da Turanci.

''Jin ciwon wani abu a rai da kuma wahala, abubuwa ne da ba za taba gushewa daga cikin kwakwalwa da zuciya ba,'' in ji shi, yana mai nuni kan bala'o'in da ya jure a tsawon rayuwarsa.

A wani nazarin falsafa na Dostoyevsky, wanda ya mutu a shekarar 1881, ya yi ƙarin haske kan ''zautuwa'' a rubuce-rubuce da ƙasidunsa tun kafin ilimin sanin halayyar ɗan'adam ya fito a matsayin darasin kimiyya a Turai a wuraren shekarar 1879.

Bayan kusan ƙarni ɗaya da rabi, an yarda da batun zautuwa a duniya a matsayin yanayin da ke buƙatar waraka - ilimin sanin yanayin jiki da kuma na ilimin sanin halayyar ɗan'adam.

A wasu al'ummomin arewacin Nijeriya da ke fama da rikici, ana amfani da wani shirin fim da ke nuna illar zautuwa wajen taimaka wa al'ummomin su yaƙi ƙyamar da ake nuna wa mutanen da suka fito neman taimako saboda halin zautuwa da suka shiga a dalilin faruwar wani mummunan abu a rayuwarsu.

Fim ɗin mai suna ''From the Brink,'' ya mayar da hankali ne kan cire ƙyama ga batun zautuwa, wanda wata ƙungiya mai suna Equal Access ta ƙasa da ƙasa mai zaman kanta da ke aiki don taimaka wa al'ummomin duniya wajen ''samar da sauyi mai ɗorewa'' ta shirya shi.

Mata da tsoffi sun fito domin kallon shirin fin ɗin na tattare bayanai./ Hoto: EAI Nijeriya

"Muna amfani tsarin kallon fina-finai na gargajiya, muna ziyartar al'ummomi, da kuma shirya taron kallon shirin a bainar jama'a," kamar yadda wani babban jami'i a ƙungiyar ya shaida wa TRT Afrika.

"Mun gabatar da jerin tarukan tattaunawa da gomman al'ummomi a faɗin jihohin uku a Nijeriya- da suka haɗa da Filato da Kaduna, da kuma Kano."

Ba laifi ba ne a nemi taimako

An tsara labarin fim ɗin From the Brink da nufin koya wa mutane ɗabi'ar sauya halayya da zamantakewa ta fuskar labari.

Fim din yana ba da labarin wata mata mai suna Sarah, wadda ke fama da matsalar zautuwa tsawon lokaci a rayuwarta, sakamakon wani abu da ya faru da ita tun da ƙuruciya, kuma damuwar hakan ke bibiyar ta har yanzu.

Tamkar dai Dostoevsky, wanda bai samu sauƙin yanayin da ya shiga ba tun kaduwar da ya samu na jiran yanke masa hukuncin kisa a Saint Petersburg lokacin yana ɗan shekara 27, kafin daga baya aka yi masa afuwa, ita ma Sarah a zauce take tun abin da ya faru da ita a baya/

Abin da ya faru shi ne an kashe wa Sarah iyayenta a kan idonta a lokacin wani faɗan ƙabilanci a garinsu. Bayan da ta rasa iyayenta, sai ta koma wajen ƙanwar innarta, inda a can kuma mijin matar ya dinga cin zarafinta ta hanyar yin lalata da ita.

An tsara labarin fim ɗin From the Brink da nufin koya wa mutane ɗabi'ar sauya halayya da zamantakewa ta fuskar labari. / Hoto: EAI Nigeria

A cikin fim ɗin, an nuna Sarah a matsayin wacce ke fama da lalurar zautuwa inda bayan da ta girma ta yanke shawarar yin aure, sai tsoro da fargabarta suka munana. Ta dinga yawan mafarkin cewa mijinta da mijin innarta da ya lalata suna zuwa don kashe ta.

Mijinta, wanda abin ya dame shi sosai sai ya yanke shawarar neman taimako da nuna mata cewa ya kamata ta yarda ta ga ƙwararru don samun shawara. Ya ƙi yarda maganganun mutane su yi tasiri a kansa, wadanda za su iya ayyana Sarah a matsayin mai fama da taɓin hankali, don kawai ta je neman lafiyar ƙwaƙwalwa.

Sarah da mijinta sun samu mafita bayan samun shawarwarin ƙwararru, lamarin da ya yi wa masu kallo daɗi.

"An nuna Sarah a matsayin wadda ke fama da zautuwa da damuwa daban-daban, lamarin da ya sa ta ƙaurace wa kowa har masu son taimakonta — a wannan yanayi, sai mijinta da ya fahimce ta kawai," a cewar jami'ai.

Fama da zautuwa na da tsanani

Trauma ko zautuwa, wani yanayi ne na tarin damuwa da firgici na gajere ko dogon lokaci na abubuwan da ke samun mutane marasa daɗi.

Sinima ta kasance hanya mai tasiri wajen yaɗa saƙonni ga al'umma. / Hoto: EAI Nigeria

Zautuwa ka iya kasancewa daga cin zarafi a gida kamar na duka ko na lalata da mutum da ma sauran matsaloli masu yin tasiri ga lafiyar hankalin mutum. Idan har wannan yanayi ya fara shafar mu’amalar mutumin da abin ya faru da shi da sauran mutane, to mutumin ka iya zama mai tsananin zafin rai ko yin martani mai zafi.

Ƙwararru sun ce bai kamata a dinga kamanta zautuwa da “ciwon hauka ba”. Kuma bai dace a dinga aibata ko kunyata wanda ya je neman taimakon kan halin da yake ciki ba.

Kamar cutar tsananin damuwa, yawanci ana fara samun waraka ne idan mutum ya fara faɗar abin da ke damunsa, Akwai matakan lafiya da ke bayyana yadda za a shawo kan zautuwa don samun nutsuwa da cikakkiyar lafiya.

Saƙon da ake yaɗa wa a cibiyoyin From the Brink suna magana ne a kan fahimtar zautuwa da goyon bayan mutane don su nemi taimako kan halin zautuwa da suka shiga sakamakon wani mummunan abu da ya faru a baya.

"Mun nuna fim ɗin a ƙananan hukumomin Nasarawa da Ungogo da Gezawa na jihar Kano", in ji jami'in Equal Access International.

Kallon fim a sinima na aiki tamkar magani

Ilimintar da mutane ta hanyar nuna musu fim a sinima yana buɗe idonsu kan fahimtar wasu abubuwa na rayuwa.

"Bincike ya nuna cewa al'ummomin arewacin Nijeriya suna matuƙar son kallon fina-finai, kuma hanya mafi kyau ta watsa shirin fim ko dirama su ne rediyo da talabijin," a cewar ƙungiyar.

A saboda dalilai kamar na sauƙin samu da muhimmancinsu a tarihi, rediyo da sinima sun kasance hanyoyi masu tasiri wajen yaɗa saƙonni ga al'umma.

A shekarar 2024 aka shirya fim ɗin don isara da saƙo ga mutanen da ke nuna alamar zautuwa. / Hoto: EAI Nigeria

A duk zagayen da aka yi na nuna fim ɗin From the Brink, waɗanda suka shirya taron suna ƙoƙarin jin ta bakin masu kallo kan darussan da suka koya daga fim ɗin.

"Cikin wadanda suka samu damar kallon fim ɗin har da matasa da mata da sarakunan gargajiya. A gari Barikin Ladi na jihar Filato, 'yan acaɓa kan tsaya su kalli shirin. A garin Jama'a na jihar Kaduna kuwa, a ƙofar gidan mai gari aka kalli fim din. A can Kafanchan ma, mai gari na daga cikin waɗanda suka kalli fim ɗin," in ji jami'in.

Mayar da hankali kan mutanen da suka fi rauni

A shekarar 2024 aka shirya fim ɗin don isara da saƙo ga mutanen da ke nuna alamar zautuwa wanda ya samo asali saboda rikici, ko tashin hankali, musamman ga wadanda ke zaune a yankunan da ake tashe-tashen hankula da sansanonin gudun hijira, da ma marasa lafiyar da aka gamo suna fama da zautuwa da firgici a dalilin wani abu mai muni da ya taɓa faruwa da su.

Waɗanda suka shirya fim ɗin sun yi nuni da jihohin Nijeriya da ke fama da matsalolin zamantakewa da tsaro da cin zarafi da rikicin addini da na manoma da makiyaya da na ƙabilanci.

"Wasu daga cikin waɗannan mutane sun rasa danginsu da kadarorinsu. Suna buƙatar tallafi don taimaka wa daidaituwar tunaninsu da waraka ba tare da fargabar nuna ƙyama ba," ya bayyana.

Tun bayan sakin fim ɗin ga jama'a, an yi ta martani kan, From the Brink. A cewar masu shirya shi, an ɗauki fim ɗin ne a wurare biyu da kuma 'yan wasa daban-daban don a nuna mabambantan al'adun arewacin Nijeriya.

TRT Afrika