Dalibai na jiran fara zana jarrabawar kasa a Nairobi/ Hoto : Shafin X na Ruto

Daga Dayo Yussuf

Wata kararrawa da aka buga ce ta kawo karshen mararin dalibai 300 da ke zumudin karatu a dakin zana jarabawa na makarantar firamare ta St John da ke rukunin gidaje na Kariobangi a babban birnin Nairobi.

Daliban sun kammala makarantar firamare. Sun shiga sabon shafi. Za su fara karamar sakandire.

Amma wannan ba wai kawai batun kammala karatu ba ne, lokaci ne na kawo karshen yadda dalibai ke karatu daga makarantun raino har zuwa jami'a.

Makarantu a kasar da ke gabashin Afirka na sauya wa daga tsarin Sakamakon Makarantun Firamare na Kenya (KCPE) da aka di sani da tsarin 8-4-4, zuwa sabon tsarin koyo da koyarwa bisa nagarta (CBC.

Tsarin 8-4-4 ya samu ne daga bukatar yin shekaru takwas a firamare, hudu a sakandire da hudu a jami'a.

Morgan Oduor na daya daga cikin dalibai miliyan 1.4 da suka rubuta jarrabawar kammala firamare a fadin kasar karkashin manhajin KCPE a watan Nuwamba.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ba na tunanin KCPE ya y tsauri ko yana da wahala. Na kasnace ina tsoron jarrabawar karshe, amma kuma ta zama abun da na ke iya yi."

Kamar sauran dalibai da suka kammala karatu tare, Morgan ya zama marar mayar da hankali - a kalla a yanzu - ga muhimmancin wannan tsari, wanda a yanzu ya rubuta jarrabawa ta karshe a karkashin tsohuwar manhajar.

Tun shekarar 1985 ake da tsarin manhaji na 8-4-4. Hoto : Ma'aikatar Ilimi ta Kenya

"Manufar kasar ita ce a samar da nagartaccen tsarin koyo da koyarwa mai dokoki da kishin kasa," in ji Milly Bulungu, wani tsohon malamin makaranta a Kenya.

Tushen wannan kokari ya faro ne tun 2010 a lokacin da aka yi shirin samar da sabon kundin tsarin mulkin Kenya.

Wannan ya biyo bayan korafe-korafen da ake ta yi game da nauyin da tsarin 8-4-4 yake kawowa dalibai.

Babban korafin jama'a da iyayen yara shi ne kowanne mataki na manhajar ya yi yawa kuma tsarin duba jarabawa da bayar da maki ya yi tsauri.

An fara amfani da tsarin tun 1985 bayan da Kenya ta ajiye tsarin manhajin 'yan mulkin mallaka.

"A lokacin da muka koma aiki da tsarin 8-4-4, an umarce mu da mu koyawa yara darussa 11 a matakin firamare," Bulungu ya shaida wa TRT Afrika.

"Wannan ya yi tsauri ga dalibai 'yan shekara 13 ko 14. Nauyin ya karu sosai ba ga daliban kadai ba, har da ma malamansu."

Milly ta yi amanna da cewa abu mafi kyau game da wannan tsarin shi ne rage makin neman shiga jami'a.

"Wannan na nufin mutane da yawa a yanzu sun samu damar shiga manyan makarantu," in ji ta.

Bijirewa sauyi

A 1985, jama'a da dama na Kenya suka nuna kin amincewa da wannan tsarin da ake watsi da shi a yanzu bisa hujjar cewar zai hana dalibai da dama samun damar zuwa jami'a.

Ana karfafar gwiwar dalibai a karkashin sabon manhajin CBC na koyo da koyarwa da su zama masu fasaha da basira. Hoto : X- Sanata Khalwale Kenya

Manhajin ya bayar shawarwarin bayar da horo da koyar da sana'o'i ga wadanda ba su samu damar shiga jami'a ba.

Matsalolin da ake fuskanta a tsarin sun yi tasiri kan tsarin 8-4-4. Amma hakan ma ya zo da kalubale da yawa, kamar yadda Milly ta bayyana.

"Muna ta bayar da digiri ba tare da kallon ko akwai ayyukan yi ba," in ji ta. "Iyaye na farin cikin yaransu na zuwa jami'o'i, amma ingancin digirin bai haifar da da mai ido ba."

Amurka da Kanada sun fara gwada irin wannan tsari na 8-4-4 kafin su ji cewa suna bukatar wani tsarin na daban.

Bayan shekaru 35, 'yan kasar kenya ma sun farka inda sauka gano illar tsarin 8-4-4. Ko'ina cike da masu digiri amma babu ayyukan yi.

Nagartaccen tsari

Kamar yadda sunansa yake bayyanawa, an tsara manhajin CBC don kubutar da jama'ar yau da masu zuwa a nan gaba daga nauyin yin digiri da ba su da amfani.

Sabon kundin tsarin mulki ya tanadi cewa dole ne kowanne yaro ya samu jagoranci wajen gano ina yake da karfi meye zai iya yi tun yana yarinta, tare da taimakon sa wajen cimma wannan buri.

Amma kuma Steven mwangi, wani malamin makarantar firamare a Nairobi, na daya daga cikin wadanda suka yi amanna cewar kasar ba ta shirya aiwatar da wannan sabon tsari ba.

Ya shaidawa TRT Afirka cewa "Mun ji cewa ana ci gaba da tattaunawa. Muna goyon bayan sauyin.

Sai dai kuma, mafi yawan mu mu malaman makaranta ba mu samu isasshen horo ba. Tsarin sauyin ba ya tafiya daidai.

A watan Disamban 2017, gwamnatin ta fitar da sanarwar bayar da umarnin fara aiki da sabon manhajin.

An bukaci masu ruwa da tsaki wajen samar da manufofin cigaban al'umma da masu samar da manhaji da su fara shirin tabbatar da wannan tsari a aikace.

Steven ya bayyana cewa "Har kayan aikin ma ba a samar ba." "Tsarin CBC ya bayyana kar a wuce mutane 30 a azuzuwa don samun aiki yadda ya kamata. A yanzu haka malami na fama da dalibai 70 a aji daya. Wannan mummunan yanayi ne."

Ya zama dole iyaye ma su yi babban gyara, musamman ma na kudi. "Da fari na dimautu. Abubuwan da zan sayawa yarinyata sun yi yawa," in ji Fatma, wadda 'yarta ke aji na uku a firamare.

"Suna yi darussa da dama a aikace. Kayan kwabawa, duwatsu, alkaluma da na girki. Kullum akwai wani da za a kai gida."

Sabon tsarin na bukatar ayyuka da dama a azuzuwa. Hoto : TRT Afrika

A daya gefen kuma, ana baiwa yara damar su yi abubuwan da ke suke ba su sha'awa, su kuma jarraba basirarsu.

Ana daukar tsawon lokaci wajen jarraba kokarin dalibai, ba wai ta hanyar yi masa jarrabawa a lokaci guda ba.

Auna kwakwalwar yara a azuzuwa ya hada da sadarwa da bayar da hadin kai, tunani mai kyau da warware mtsaloli, kirkirar abubuwa da zuzzurfan tunani, sanin yadda za a sarrafa na'ura mai kwakwalwa da yanar gizo da kuma inganta kai.

Milly ta ce "Malamai ba sa bayyana dalibi ya samu A ko kaso 90. SUna amfani da kalmomi, kamar 'yaron ya wuce inda ake zato', ma'ana ya yi kokari sosai.

Wani kuma shi ne 'yana kokarin yin yadda aka tsammata', ma'ana daidai gwargwado yana da kokari'."

Babban kalubalen wannan sauyi ga kasar a yanzu shi ne yadda jama'ar da suka ginu kan tsare-tsaren ilimi mabambanta za su hadu waje guda su samar da yanayi da tsarin da zai taimaka tare da ghabaka Kenya.

TRT Afrika