A wani lungu mai nisa a arewacin Kenya, fafutuka ake don don gudun ƙurewar lokaci wajen ceton nau'in dabbobin da ke fuskantar haɗarin ƙarewa.
A can cikin yankin gandun daji na Ol Pejeta Conservancy, akwai wasu manyan halittu biyu da suka rage a nau'insu, waɗanda su ma suke fuskantar barazanar ƙarewa.
Fararen karkanda, suna daya daga cikin manya-manyan dabbobi masu shayarwa a doron kasa. Duk da sunansu, waɗannan halittu masu ban sha'awa ba farare ba ne a zahiri. Suna da launin fata mai launin toka da ruwan ƙasa-ƙasa.
Yanayin girmansu da ƙarfinsu da tsarin ƙahonsu ya sa sun zama wata alama ta gandun dajin Afirka da kuma kyawun gani.
Fararen karkanda sun kasu naui biyu: farar karkanda ta arewaci da farar karkanda ta kudanci.
Farar karkanda ta kudu ita ce ta fi yawa, inda ake da kusan 18,000 da aka fi samu a Afirka ta Kudu da Namibiya da Zimbabwe da Kenya.
Ita kuwa farar karkanda ta arewa, abin baƙin ciki, tana gab da ƙarewa, inda biyu kacal suka rage a doron ƙasa kuma a Kenya kadai ake iya samun su.
A shekarar 2018 naui'n namiji tilo na farar karkanda da ke Sudan ya mutu, yanzu sai fararen karkanda mata biyu na arewa ne suka rage a duniya: Najin da Fatu.
Barazana
Gomman shekaru da suka wuce, wannan nau'in farar karkandar ta arewa ana samun ta sosai a yankin tsakiyar, kamar yadda Samuel Mutisya, shugaban kula da tsare tsare na Ol Pejeta na Kenya ya shaida wa TRT Afrika.
''Wato a yankin da ke tsakanin Kongo da Kudancin Sudan da wani sashe na Uganda da kuma Chadi . Don haka yanki ne da aka keɓe. Mun ce a da suna da yawa a sassan tsakiyar Afirka,'' in ji shi.
''Abin takaicin shi ne, yankin ya fuskanci tashe-tashen hankula da dama na tsawon wani lokaci, wanda wataƙila hakan na da nasaba da ƙarewar dabbobin. Ta wani wajen kuma saboda lalata mazaunansu, saboda wannan tashin hankali da rashin ingantaccen tsaro, mun rasa wannan nau'in dabbaobin," in ji mai kula da kiyaye muhallin.
Masana irin su Mutisya sun yi imanin cewa matsalar farar karkanda a Afirka ta kara ta'azzara saboda dalilai daban-daban tare da farautar kahonsu da ya zama babbar barazana.
Ana amfani da sassan jikin karkanda irin su ƙaho a cikin magungunan gargajiya da kuma kayan ado a wasu sassan duniya da ke kai ga haramtaccen fatauci.
Rikici tsakanin mutane da dabbobi masu shayarwa a halin yanzu ya kasance mafi girma a cikin manyan barazanar da ke haifar da kare namun daji a sassan Afirka, in ji masana.
Hali mai rikitarwa
Al'ummomin da ke zaune a yankunan da namun daji suke na ƙorafin yadda namun daji ke shiga gonakinsu da matsugunansu yayin da masana ke ganin farautar dabbobi da lalata wuraren zaman su ne babban dalilin rikicin.
''Rayuwar ɗan'adam ta dogara sosai ga tsarin muhalli da na yanayin rayuwa. Don haka a ra’ayina, namun daji da rayuwar dan’adam suna bukatar juna don su dace da wanzuwa. Don haka ba za ku fifita ɗaya a kan ɗayan ba. Ba na tsammanin yana da sauƙi kamar irin wannan,'' in ji Mutisya.
''Akwai wurin da 'yan'adam suka mamaye a cikin tsarin. Kuma akwai wurin namun daji. Don haka, ya kamata su biyun su nemi wanzuwa fiye da gasa." in ji shi
Masana sun yi imanin cuɗanya ko mu'amala tsakanin halittu daban-daban a cikin yanayin zama yana tabbatar da daidaiton da ake buƙata don rayuwa mai ɗorewa amma sun yarda cewa kiyaye muhalli yana da tsada.
"Idan alal misali Kenya ta yi watsi da yarjejeniyoyin da aka ƙulla kan bambancin halittu da rage iskar Carbon da sauran iskar gas, to, mun koma baya a matsayinmu na al'ummar duniya baki daya. Muna bukatar mu yi aiki tare. Muna buƙatar samun wadatattun albarkatu, '' Mutisya ya bayyana.
Masana kimiyya suna da kyakkyawan fata
Daya daga cikin matsalolin da ke sa wa yawan fararen karkanda ba ya ƙaruwa shi ne cewa ba sa haihuwa akai-akai.
Sai dai a bayan fage, ana wani ƙoƙari don tabbatar da wanzuwar farar kankandar. Masana kimiyya da masu kare muhalli sun ba da lokacinsu sosai wajen tsara matakan ceto dabbobin da ke barazanar ƙarewa.
Sun kasance suna amfani da dabarun haihuwa na wucin gadi, a wani yunƙuri na haɓaka yawan adadin nau'ikan dabbobin.
"Bayan binciken dalilin da ya sa dabbobin ba sa samun juna biyu, mun gano cewa karamar macen tana da cututtuka ko yanayin cuta a cikin mahaifa wanda ba zai iya ba da damar daukar ciki ba, '' in ji Mutisya.
"Mun fahimci cewa har ma mun yi sa'a ɗaya macen ba ta samu ciki ba saboda a lokacin ba za ta dauki ciki har ya kai haihuwa ba saboda kalubale na tsarin dabba. Ƙafafunta na baya sun yi rauni, ba za su iya daukar nauyin cikin har zuwa lokacin haihuwa ba,'' ya bayyana.
Hanyoyi
A watan Oktoban 2015, masana a birnin Berlin sun fara tattara ƙwai daga farar karkanda na kudancin ƙasar tare da tura su Italiya.
Daga baya masana kimiyya sun samar da wata fasaha ta ƙirƙirar ɗan tayi. Masana kimiyya sun kwashi ƙwan haihuwar Naji da Fatu da sauran fararen karkanda na arewa a watan Agustan 2019 don ƙyanƙyashe su da maniyyin namijin farin karkanda na kudu.
Wannan abu ya bai wa masana kimiyya ƙwarin gwiwar cewa wata farar karkanda ta arewa za ta iya ɗaukar cikin farar karkanda ta kudu saboda duka nau'ukan biyu tsawon goyon cikinsu ɗaya.
Cike gurbi
Ceton fararen karkanda ba taimakawa haɓaka rayuwar namun dawa kawai zai yi ba, zai inganta harkar yawon buɗe ido.
Wannan zai samar da kudaden shiga ga gwamnatoci da al'ummomin yankin tare da wayar da kan jama'a game da muhimmancin kiyaye wadannan kyawawan halittu da wuraren zama.
"Akwai babbar dama da za mu iya cike giɓin sake farfado da wannan farar karkanda ba wai kawai ta hanyar kiyayewa da nau'in halitta ba, har ma don ba da gudunmawa ga tsarin halittu," in ji Don Jooste Rhino Rewilding Project Manager Kungiyar kare muhalli ta African Parks.
Tabbatar da wanzuwar farar karkanda ta arewa ba batu ne na kare dabbar ba kawai, har ma da batun kiyaye al'adunmu, da yanayinmu, da ma'auni mai kyau na yanayi, in ji masu kare muhalli.