Hindou ta ce ta "zo wannan duniyar da kaunar muhalli.'' Hoto: TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

Game da batutuwa da dama na rayuwa, watakila abu mafi muhimmanci shi ne sanin manufar mutum. Mutane da dama na karar da rayuwarsu wajen gwagwarmaya.

Tana yawan fadin "na zo wannan duniyar da kaunar muhalli kuma ban taba daina yaki don kare shi ba."

Matashiyar da aka haifa a Chadi, rayuwar Hindou daga yankinta zuwa matakin kasa da kasa da zama sananniyar mai kare muhalli, tare da kasancewarta masaniyar ilimin taswira, sun samu ne saboda jajircewa da juriyarta wanda ta amince su ne jigon manufarta a rayuwa.

Ta yi rayuwarta a shekarun farko a N'Djamena babban birnin Chadi, inda take zuwa hutu wajen al'ummar Mbororo, asalinsu na yin noma da kiwon shanu.

Wannan alaka ta kai tsaye da salon rayuwar Mbororo, gami da kalubalen da take fuskanta na mace 'yar asalin yankin, ya sanya ta samun karfin gwiwar kare muhallii da ma al'ummarta.

Hindou ta yi tafiye-tafiye sosai a duniya - tun daga taron COP 15 mai tarihi a Paris, ind ata sanya hannu kan Yarjejeniyar Paris a madadin jama'ar yankinta, zuwa ga taron sauyin Yanayi na 2019 da aka yi a New York da ma COP 28 na watan Disamban bara.

Kwarjini da iya maganarta na isar da sako mai muhimmanci cikin sauki a wajen wadannan taruka. "Dole ne mu kare muhalli da muke rayuwa a ciki. Rayuwakanmu, da hanyar da muke rayuwa, sun dogara ken muhallinmu," in ji ta.

"Gwagwarmaya da wayar da kan jama'a don kare wannan muhallin abu ne da yake a jinina." An kuma san matashiyar mai shekaru sama da talatin da so da kaunar tufafin Afirka, wanda take saka wa a duk inda take.

Karfin gwiwar gangami

Duk da cewa ta halarci makaranta, amma Hindou ta koyi yadda za ta tsara ayyukanta ne daga abin da ta kira - wata hanya da ta saka ta a turbar aiki da dukkan jama'arta.

"A lokacin da na ke firamare, na so na yi magana da neman hakkina a matsayin yarinya, a matsayin yarinya karama, ta haka ne na samu damar fahimtar cewa ba za ka taba magana kan kare hakkokin dan adam ba, ba tare da ka kare muhalli ba.

A wannan lokacin ne na kirkiri wata kungiya ta Mata 'Yan Asalin Chadi (AFPAT)," in ji matar da ta lashe Kambin Pritzker na Kare Muhalli.

Hindou ta fito daga jama'ar Mbororo makiyaya. Hoto: TRT Afrika

A shekarar 1999 ne, a loakcin Hindou na da shekara 15. Tasirin ayyukanta ya yadu har zuwa yankunan da suke wajen kudu maso-yammacin Chadi da nan ne take son gudanar da shirin wayar da kan mutane.

Baya ga kambin Pritzker, ta kuma samu Kambin Holbrooke da kungiyr Kula da Masu Neman Mafaka ta Kasa da Kasa ta bayar, d akuma Kambin Danielle Mitterrand. Daya daga cikin manyan nasarorin Hindou a matsayinta na masaniyar ilimin taswira saboda gudunmowar da ta bayar na zanen 2D da 3D a yankin Sahel.

Aikin da ake gabatarwa da hadin gwiwar UNESCO, na da manufar kara yawan yankunan da jama'a ke zaune, duba ga halin da suke ciki wanda ya kebanta da su kawai. Wata manufa ta wannan shiri kuma ita ce kalubalantar rikici tsakanin manoma d amakiyaya a yankin.

Aikin ya kuma mayar da hankali wajen wayar da 'yan asalin yankin kan muhalli, a matsayin kokarin yaki da gurbacewar muhalli.

Hadin kan Hindou da UNESCO ya sanya an amince da hakkokin mata, inda aka samar da ayyukan da zau dinga kawo kudaden shiga, duba da yanayin noma a wasu yankunan. Kokarinta ba kakkautawa ya kuma sanya ta kafa sunan jama'arta a wajen taron COP15 a Paris, ciki har da bukatar kare hakki da ilmantarwa.

Kalubalen kudade

Ta fada wa TRT Afirka cewa kafi ta isa ga inda take a yau, Hindou ta fara a hankali, muamman kan batun samun kudaden. Ta ce "A lokacin aikina na farko a fagen daga, ban nemi tallafin kudi daga wata kungiyar kasa da kasa ba."

Hindou ta damu kan yadda sauyin yanayi ya shafi jama'ar yankinta. Hoto: TRT Afrika

"Na halarci tarukan kasa da kasa, wanda saboda su na samu 'yan kudade. Don na ajje kudi, sai na dinga cin abinci mafi arha, sannan na ke zama a otel mafi karancin kudi."

Kudaden da Hindou ke ajje wa, sun dinga tafiya ga ayyukan farko da ta fara yi. "Na fara kirga kudaden da na ke da su don kare abin da na ke takama da shi," Hindou ta fada wa TRT Afirka.

An ci gaba da kokarin cimma wannan manufa, amma Hindou ta yi nisa sosai. Alkaluma sun bayyana girman irin ayyukan da take yi.

Gwagwarmaya mara misaltuwa

Hukumar Kare Muhalli ta Faransa ta ce, sare bishiyu a Cjadi na janyo bacewar hekta 200,000 na dazuka a shekara. Hakan na janyo kwarorowar hamada a yankin Sahel da ke Chadi.

Ana hasashen sahara za ta ci gaba da karuwa da tsayin kilomita uku a kowacce shekara. irin wadannan abubuwa ne suke sanya Hindou zage damtse wajen taimaka wa a samu daidaito a zamantakewa tun kafi lokaci ya kure.

Ta ce "Domin kare muhalli, dole ne mu fara aminta da dukkan nau'ikan halittun da ke cikin muhalli, ba wai dan adam kawai ba, har da tsirrai da dabbobi.

"Muna bukatar kare tsuntsaye, kwari, tsirrai, bishiyu da ciyayi, duk suna da daraja da 'yanci. Dukkan masu zama a muhalli na da alaka da juna; wanzuwa a muhalli ta dogara kan juna; idan muka yi watsi da daya, hakan na nufin muna damun daidaiton dayan kenan."

A wajen taron kasa da kasa na COP28, Hindou ta yi jawabi game da cigaban da ayyukanta ke samu a wasu takardu da aka fassara zuwa wasu yarukan.

Hindou - mai fafutukar kare muhalli

Wani abu a ya faru a wajen taron ya bayyana me ya sa ta aminta da da aiki da masu ruwa da tsaki a karon farko, wanda shi ne mafi muhimmanci.

ya suka fada min "Mun son me kike yi. Muna goya miki baya da ba ki dukkan kuzarin da kike bukata".

Wannan ya faranta min da karfafa gwiwata. Karfafa gwiwa na da muhimmanci irin na kwarewa da samun kudade," in ji ta.

Ta ce "Ina son yaki da kasuwar hayakin gurbata muhalli (gawayi, mai da gas), wadanda ke janyo gurbatacciyar iska da ke janyo dumamar yanayi."

TRT Afrika