Akalla an fuskanci barazanar kutsen yanar gizo sama da biliyan 1 a rubu'in karshe na shekarar 2023 a Kenya. Hoto: Getty Images.      

Daga Dayo Yusuf

Masu kutsen yanar gizo domin aikata laifuffuka kullum kara fito da sababbin dabaru suke yi, da kuma nemo hanyoyin da za su tsallake duk wani yunkurin da ake yi na dakile su.

Sai dai fa idan sun gamu da ingantaccen tsaro na intranet da kamfani ko hukumar gwamnati ko daidaikun mutane suka shirya domin dakile su. Amma duk da haka, hanzu kallon-kallo ake yi. Suna neman hanyar cuta, masu kaya na ta kara neman hanyoyin tsaro.

Yusuf Kileo, masanin dakile kutsen yanar gizo ne, sannan kuma mai sharhi a kan kutsen a Tanzania, ya bayyana cewa, "ba samun karuwar kutsen yanar gizon kadai ake yi ba, yanzu kara fito da wasu sababbin dabarun suke yi," inji shi a tattaunawar shi da TRT Afrika.

"Kuma har yanzu babu cikakken adadin wadanda aka cutar ta yanar gizon saboda mutane da dama ba sa kai rahoton."

A kasar Kenya, kullum lamarin kutsen na yanar gizo kara ta'azzara yake yi. A rubu'in karshe na bara kawai, an fuskanci akalla barazanar kutse sama da biliyan 1, kari a kan miliyan 123 da aka samu a watannin farkon shekarar.

Wannan barazanar tana kawo kalubale mai girma ga yunkurin dakile masu kutse a kasar.

Domin fuskantar wannan barazanar, Ma'aikatar Watsa Labarai da Sadarwa da Fasahar ta sanar da yunkurin yaki da kutsen yanar gizo a kasar baki daya.

"Gwamnati za ta inganta fasahar gano kutsen yanar gizonta sannan za ta ba ma'aikatanta kayan aiki na zamani domin yaki da barazanar," in ji Edward Kisiang'ani, babban sakataren watsa Labarai ta hotuna masu motsi.

"Mun shirya tsaf domin hada gwiwa da kasashen da muke makwabtaka da su domin yaki da matsalar a tare."

Kutsen yanar gizo da dama ba a kai rahotonsu. Hoto: Getty Images 

Babu wanda ya tsira

Don haka, yaya daidaikun mutane da ma'aikatu suke samar da daidaito wajen amfani da yanar gizon da kuma fama da barazanar kutse?

"Kutsen yanar gizo zai iya fadawa kan kowa, amma a zahiri yake wani zai fi wani jin zafi," inji Kileo a zantawarsa da TRT Afrika.

"Ana kara kai farmakin kutsen a kan bankuna, da masu karbar fansho, inda wasunsu suke asarar fanshonsu da suka tara. Asibitoci ma ba su tsira ba, inda masu kutsen suke kwashe bayanan marasa lafiya a wasu kasashen Afirka. "

Watakila barazanar da ta fi tayar da hankali ita ce wadda take fuskantar yara kananan, wadanda bayan sun rasa kudi, a kan ja hankalinsu kan harkokin badala ko kuma a yi fataucinsu.

"Tsofaffi da kananan yara sun fi fuskantar barazana domin ba su fahimci kutsen yanar gizon sosai ba," inji Kileo.

Misali a Tanzania, an tsara dokoki da suke yaki da kutsen yanar gizo da suke barazana ga kananan yara.

Dokar mai suna Child Online Protection Act, wadda aka yi a bana, an tsara ta ne domin kare yara daga fadawa komar masu kutsen. Za a gwada amfani da dokar ce na shekara daya, daga nan sai a duba tasirinta da kuma yiwuwar yi mata garambawul domin a fitar da ta dindindin.

Daga cikin tsarin akwai wayar da kan yara a kan hanyoyin magance kutsen, da duba dokar lokaci bayan lokaci da kuma amfani da na'urorin kariya tunda yaran sun saba amfani da yanar gizon.

Alkaluma sun nuna cewa har da kwararrun masu amfani da intanet ba su tsira daga kutsen ba.

"Mun sha ganin matasa masu hada-hadar kudaden kirifto suna korafin an sace musu kudi, ko kuma an yaudare su, an kwashe musu kudi," inji Kileo a lokacin da yake amsa tambayoyin TRT Afrika.

Alkaluma sun nuna cewa har da kwararrun masu amfani da intanet ba su tsira daga kutsen ba.

Daƙile ayyukan masu kutse

Kasashe da dama suna da dokokin yaki da masu kutsen yanar gizo, amma masana suna cewa ba dokar ba ce matsalar, dabbaka ta.

Haka kuma kutsen yanar gizo ba shi da wani yanki za a ce ya fi yawa, kuma ba ya bambanta wadanda ake hara, da wadanda suka taba fadawa komarsu.

Wannan ya sa masana suka ba da shawarar a samu hadin kai a tsakanin ma'aikatun da suke cikin kasa daya da ma na wasu kasashen masu makwabtaka, musamman wajen raba bayanan sirri a tsakaninsu.

Don haka, me mutum zai yi domin dakile masu kutsen?

Na farko dai, wanda kuma shi ne mafi muhimmanci shi ne mutum ya fahimci cewa kai za ka fara kare kanka, kuma nauyin kare kanka da harkokinka ya rataya ne a kanka, kamar yadda masana suka nuna.

TRT Afrika