Daga Firmain Eric Mbadinga
Farida Tiemtoré, matashiyar lauya mai kishin ci gaban mata a Burkina Faso, ta ƙuduri aniyar samar da ci gaba wa al'ummarta.
''Sha'awata ba kawai ta tsaya ba ne a iya aikin da na ƙware a kai, har da kowane fanni na rayuwa,'' kamar yadda Farida ta shaida wa TRT Afrika.
Farida ta kasance tana wayar da kan mata matasa a karkashin tutar kungiyarta ta Heroines of Faso wato Jaruman Faso kan yadda za su inganta rayuwarsu.
Ta soma sha'awar gwagwarmayar ne a lokacin karatunta na sakandare, amma shekarar 2019 ne ta yi fice a lokacin da ta kafa shafin dandalinta na yanar gizo, wanda bayan shekaru biyu aka canza shi zuwa wata ƙungiya da nufin samar da murya ga al'amuran da suka shafi mata.
‘’A matsayina na shugabar kungiyar ‘yan mata, na samu gogewa sosai a fannin bayar da shawarwari da wayar da kan al’umma da kuma hanyoyin gudanar da ayyuka.
"Ƙwarewata da mai da hankalin da na yi na da alaka da manufa guda daya: don taimakawa wajen samar da kasar Burkina Faso mai adalci kuma wacce ta hada kan kowa da kowa, inda kuma za a inganta 'yancin mata," in ji ta.
Ƴan kungiyar Heroines of Faso suna yawan gudanar da taron horaswa don ilmantar da mata da kuma karfafa musu gwiwa.
"Muna aiki don tabbatar da cewa mata da 'yan mata sun sami damar samun ingantaccen kulawa da kuma bayanan da suka dace," in ji Tiemtoré.
"Muna yaki da ayyukan cin zarafi masu nasaba da jinsi ta hanyar ba da tallafi ga wadanda abin ya shafa da kuma bayar da shawarwari don kare hakkin mata da 'yan mata," in ji Tiemtoré.
Burkina Faso dai ta shafe samar da tsawon shekaru goma tana fama da tashe tashen hankula, wanda ya bar kusan kashi uku na al'ummomin kasar karkashin ikon mayakan.
Wani rahoton baya-bayan nan da hukumar ba da agaji ta Oxfam ta fitar, ya yi kiyasin cewa sama da mata da ‘yan mata miliyan daya a Burkina faso na fuskantar karuwar ayyukan cin zarafi da suka shafi mata da yunwa da kuma karancin ruwa a sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi.
A watan Oktoban 2023 ne kungiyar 'Heroines of Faso' ta kaddamar da wani shiri mai taken "School of Heroes" don ba da tallafin ilimi ga yaran da iyayensu suka shiga cikin ayyukan sa-kai na 'Defence of the Fatherland' (VDP) - wata kungiyar sa kai da ke yaki tare da sojoji don yakar mayaka masu dauke da makamai.
"Muna son kowane yaro da ya fito daga (iyalin) VDP su farka da safe tare da murmushin bege a fuskokinsu, da sanin cewa ana ƙaunar su, ana tallafa musu kuma suna da makoma mai kyau a gabansu," Tiemtoré ta shaida wa manema labarai a yayin da take mika kyaututtukan kayan makaranta ga yara mabukata.
Kungiyar za ta biya kudin makaranta na yara 15 har na tsawon shekarar kalandar karatun makaranta ta 2024/2025.
A ranar mata ta duniya, kungiyar ta shirya wani taron horaswa ga mata, tare da koyar da su hada sabulu a wani bangare na shirye-shiryen kungiyar don ''tsafta da horar da ayyukan samar da kudaden shiga'' in ji ta.
“Shirin taron shugabannin matasa na ƙungiyar yana samarwa matasa dandali da zai taimaka musu wajen fito da baiwarsu da ra'ayoyi zuwa rayuwa, inda ƙalubalen ƙasarmu za iya samun mafita, kuma inda ake ƙarfafa haɗin kai tsakanin kowane jinsi,” in ji mai fafutukar.
A shekarar 2019, shafin Heroines of Faso ya samu lambar yabo ta 'Coup de cœur des internautes' wato mafi kyawun shafin al'umma a yanar gizo a Kyautar Blog na Burkina Golden.
Don samar da kuɗadden gudanar da ayyukanta, kungiyar ta dogara ne kan karamcin masu aikin sa kai, da masu ba da tallafi da kuma goyon bayan waɗanda ke jin daɗin manufarta.
Kazalika Kungiyar ta na matukar jinjinawa goyon bayan da hukumomin yankin ke ba ta wajen gudanar da ayyuka da shirye-shiryenta a wannan fanni.